Atiku Ya Haƙura da Neman Mulkin Najeriya, Ya Faɗi Lokacin Ƙarshe na Yin Takara
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana shirinsa na yin ritaya daga neman kujerar shugaban kasar Najeriya
- A cewar Atiku Abubakar, zaɓen 2027 shi ne karo na ƙarshe da zai fito neman mulkin Najeriya, don haka zai yi duk mai yiwu wa a 2027
- Ya kuma amsa tambaya game da dalilin da zai sa ƴan Najeriya su amince da shi a 2027 bayan yunƙurin neman wannan mukami sau da dama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja – Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana lokacin karshe da zai nemi mulkin Najeriya, yain da siyasar 2027 ke gabatowa.
A wani sako da zai girgiza siyasar kasar, Atiku ya bayyana cewa zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 shi ne zai zama fafatawarsa ta ƙarshe a fagen neman mulki.

Source: Twitter
Shekarar karshe da Atiku zai tsaya takara
Atiku ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 15 ga Afrilu, 2026, yayin wata hira ta musamman da gidan talabijin na Arise TV a shirin "Prime Time".
Tsohon jagoran PDP, ya jaddada cewa ba zai fasa takara a zaɓe mai zuwa ba, amma kuma wannan ita ce dama ta ƙarshe da zai ba kansa da kuma magoya bayansa.
Atiku, wanda ya fara neman takarar shugaban ƙasa tun a shekarar 1992, ya bayyana cewa:
"Zaɓen 2027 shi ne zai zama karo na ƙarshe da zan tsaya takarar shugaban ƙasa,"
Wannan furuci nasa ya zo ne a daidai lokacin da ake ta mahawara kan makomar tsofaffin jiga-jigan siyasar ƙasar da kuma buƙatar ba matasa damar yin mulki.
Dalilin Atiku na dade wa yana neman mulki
Atiku ya kuma amsa tambaya game da dalilin da zai sa ƴan Najeriya su sake amincewa da shi bayan yunƙurin neman wannan mukami sau da dama, musamman idan aka yi la'akari da shekarunsa.
A amsar da ya bayar, tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa matsalar Najeriya ba ta shekaru ba ce, face ta iya shugabanci.
Ya ce shi kansa yana wakiltar tarihin Najeriya na baya da kuma kyakkyawar makomar da ƙasar ke buƙata.
Atiku ya ƙara da cewa ilimi da gogewar da ya samu a tsawon shekarunsa na siyasa sune makaman da yake son amfani da su wajen gyara ƙasar a karo na ƙarshe.

Source: Getty Images
Bukatar ba matasa horo kan shugabanci
Wani muhimmin sashe na hirar tasa shi ne inda ya nuna damuwa kan yadda matasa ke bukatar shiri na musamman kafin su karɓi ragamar mulki.
Atiku ya ba da shawarar cewa ya kamata a samar da tsari na bai ɗaya na horar da matasa kan dabarun shugabanci.
"Najeriya na buƙatar shugabanni waɗanda aka shirya su da ilimi da kishin ƙasa, kuma hakan ba zai yuwu ba idan ba a samar da ingantaccen horo ga matasa masu tasowa ba."
- Atiku Abubakar.
Wannan kalami nasa na zuwa ne a lokacin da matasa da dama ke kiran a ba su dama su fafata a zaɓen 2027 ba tare da tsangwama ba.

Kara karanta wannan
Tsohon shugaban APC ya hango faduwar Tinubu, ya fadi wadanda za su iya lashe zaben 2027
Kalli bidiyon hirar a nan kasa:
"Ka hakura" - Baba Ahmed ga Atiku
Tun a baya, mun ruwaito cewa, Hakeem Baba-Ahmed ya shawarci Atiku Abubakar da ya hakura da neman shugabancin Najeriya, ya zama uban al'umma don ci gaban ƙasa.
Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana cewa ya kamata a ce zuwa yanzu Atiku ya yi ritaya daga siyasa, ya zama gwarzon dimokuraɗiyya a matsayinsa na tsohon mataimakin shugaban ƙasa.
Ya kuma buƙaci Atiku da ya mai da hankali kan samar da sababbin shugabanni, masu jini a jika, wadanda za su karbi mulki daga hannun APC, su kawo ci gaba ga kasar.
Asali: Legit.ng

