Zaben 2027: "Kwankwaso Ya Amince Ya Zama Abokin Takarar Peter Obi"

Zaben 2027: "Kwankwaso Ya Amince Ya Zama Abokin Takarar Peter Obi"

  • Wani na kusa da Peter Obi ya bayyana cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya amince ya zama abokin takarar tsohon gwamnan Anambran a zaɓen 2027
  • Ibrahim Abdulkarim ya tabbatar da cewa an riga an tsara taron haɗin gwiwa tsakanin magoya bayan Kwankwasiyya da kuma Obidients
  • Kwankwaso ya taba cewa zai karɓi muƙamin mataimakin shugaban ƙasa na Peter Obi, muddin aka samar da amana, duk da ya girmi Obi a siyasance

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja – Wani babban na kusa da tsohon gwamnan jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Ibrahim Abdulkarim, ya tabo batun siyasar 2027.

Ibrahim Abdulkarim ya yi ikirarin cewa jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya amince ya zama abokin takarar Peter Obi a zaben mai zuwa.

Kara karanta wannan

Atiku ko Obi: An yi hasashen wanda zai samu tikitin ADC a zaben 2027

An rahoto cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya amince ya zama abokin takarar Peter Obi a zaben 2027
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da Peter Obi. Hoto: @PeterObi
Source: Twitter

"Kwankwaso zai zama abokin takarar Obi"

Makusancin tsohon d'an takarar shugaban kasar na jam'iyyar LP ya bayyana cewa Kwankwaso ya amince ya zama mataimakin shugaban kasar ne a yayin da yake tattauna wa da Trust TV a Abuja.

Wannan sanarwa na zuwa ne a daidai lokacin da jiga jigan jam'iyyar adawa ta ADC ke ke ƙoƙarin dinke duk wata baraka domin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Ibrahim Abdulkarim ya nuna cewa wannan yarjejeniya ta biyo bayan jerin taruka da aka rinka gudanarwa tsakanin ɓangaren Kwankwaso da na Peter Obi a watannin baya-bayan nan.

Legit Hausa ta rahoto cewa Kwankwaso ya shiga jam’iyyar ADC ne makonni kaɗan da suka gabata, bayan da aka yi zargin cewa burinsa na samun tikitin mataimakin shugaban kasa a APC ya faskara.

Za a yi taron Kwankwasiyya da Obidients

Ibrahim Abdulkarim, wanda hadimi ne ga Peter Obi, ya bayyana cewa tattaunawar ta su ta wuce matakin 'wai wai', domin yanzu an shiga mataki na haɗakar gadan gadan.

Kara karanta wannan

Atiku: "Yadda ADC za ta fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa a 2027"

Ya bayyana wa gidan talabijin din cewa shugabannin biyu sun haɗu fiye da sau biyu domin cimma wannan matsaya.

A cewar Ibrahim:

“Eh, zan iya tabbatar muku da cewa ya amince. Sun haɗu ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba. Har ma mun riga mun tsara babban taron haɗin gwiwa tsakanin Kwankwasiyya da Obidients wanda zai gudana nan ba da daɗewa ba.”

Wannan mataki na kallon matsayin sake fasalin siyasar adawa a Najeriya, musamman yadda kowane ɓangare ke da dimbin magoya baya.

Kalli bidiyon a nan kasa:

Sharuɗan Kwankwaso kan takara da Obi

A wani bidiyo da ke yawo a kafofin sada zumunta, Sanata Kwankwaso ya tabbatar da shirye-shiryensa na zama mataimakin Peter Obi, muddin aka cika wasu sharuɗa kuma aka samar da amana tsakanin ɓangarorin.

An ce Kwankwaso ya ce zai zama abokin takarar Obi a 2027 idan aka samar da amana.
Peter Obi (tsakiya) ya na daga hannu ga 'yan Kwankwasiyya a Kano yayin shigar Rabiu Kwankwaso ADC. Hoto: @PeterObi
Source: Twitter

Sai dai ya jaddada cewa ta fuskar siyasa da ilimi, ya fi Peter Obi girma, duba da matsayinsa na mai digirin digirgir (PhD) da kuma yadda ya gudanar da mulki a jihar Kano, in ji rahoton Business Day.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ko Obi: Atiku ya fadi dan takarar da zai iya goya wa baya a ADC

Gabanin zaben 2023, Kwankwaso ya bayyana cewa:

“Ni na girmi Peter Obi a siyasa, ni babban wansa ne, kuma na yi rawar gani fiye da shi lokacin da nake gwamnan jiha ta. Ba ni da matsala da zama mataimakinsa, muddin aka samar da amana.”

Idan za a iya tunawa, a zaɓen da ya gabata, Obi ya samu ƙuri’u sama da miliyan shida a jihohi 11 da Abuja, yayin da Kwankwaso ya mamaye jihar Kano da ƙuri’u kusan miliyan ɗaya da rabi.

Tikitin Obi/Kwankwaso ya fara jan hankali

Tun da fari, mun ruwaito cewa, yiwuwar hadakar Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso na kara haifar da farin ciki a tsakanin wasu ‘yan Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan shirin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na komawa ADC a ranar Litinin 30 ga watan Maris, 2026.

Wasu na ganin hadakar za ta kawo sauyi a zaben 2027, la'akari da cewa Peter Obi ne ya zo na uku a zaben 2027, yayin da shi ma Kwankwaso ke da miliyoyin mabiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com