Bauchi: Bala Wunti Ya Gana da Matashi da Ya Sayar da Ransa kan Takararsa Ta Gwamna
- Wani matashi, Adamu Salisu ya hau kan karfen sadarwa a Bauchi, yana neman Dr. Bala Maijama’a Wunti ya fito takarar gwamna
- Wakilan dan siyasar sun kai ziyara ofishin ‘yan sanda domin karɓar matashin a jihar Bauchi
- Daya daga cikin yaransa, Haske No Shaking ya ce Bala Wunti ba ya goyon bayan matakin da zai jefa rayuwar masoyansa cikin haɗari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - A ranar Lahadi aka wayi gari da wani abun al'ajabi bayan matashi ya hau karfen sabis saboda wani dan siyasa.
Matashin mai suna Adamu Salisu ya ce ba zai sauko ba har sai Bala Maijama'a Wunti ya fito takarar gwamna a Bauchi.

Asali: Facebook
Wunti: Matashi ya sayar da ransa a Bauchi
Daraktan wayar da kan jama'a na Bala Wunti a kafofin sadarwa, Haske No Shaking ya fadawa wakilin Legit Hausa cewa wakilan dan siyasar sun ziyarci matashin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haske ya ce wakilan sun ziyarci ofisoshin yan sanda ne bayan jami'an rundunar ta dauke matashin zuwa ofishinta.
Ya ce tawagar ta yi ziyarci Kwamishinan yan sanda a jihar game da lamarin matashin.
Mutane da dama sun yi mamakin irin soyayyar da matashin ke yiwa ɗan siyasar a Bauchi.
Matashin bayan ya dare kan karfen sabis, ya tabbatar da cewa ba zai sauko ba har sai Bala Wunti ya hallara a wurin.
Hakan bai samu ba, amma jami'an yan sanda sun hallara inda suka yi ta kokarin shawo kan matashin ya sauko.

Asali: Facebook
Shawarar Bala Wunti ga masoyansa a Bauchi
Bayan rarrashi da ba shi tabbacin tsaron lafiyarsa, matashin ya sauko inda yan sanda suka tafi da shi ofishinsu domin kare lafiyarsa da kuma ba shi kulawa.
A cikin bayaninsa, Haske ya ce:
A ranar Lahadi, wakilan Dr. Bala Maijama’a Wunti sun kai ziyara ofishin kwamishinan yan sanda na jihar Bauchi domin karɓar matashi Adamu Salisu
"Matashin shi ne wanda ya hau kan ƙarfen sabis yana ɗaga takarda cewa sai Dr. Bala Maijama’a Wunti ya amsa kiran al’ummar bauchi domin takarar gwamna a 2027.
"Wannan mataki da ya ɗauka ya samo asali ne daga irin ƙauna da goyon bayan da yake da shi ga Dr. Bala, tare da buƙatar ganin ya fito ya wakilci jihar.
"Wakilan sun nuna godiyarsu matuƙa ga jami’an tsaro bisa kulawa da amincewar da suka nuna wajen karɓar matashin cikin lumana.
"Sun yi jinjina ga Adamu Salisu bisa ƙaunar da ya nuna, amma sun ja kunnensa cewa soyayya da goyon baya ga jagora abin alfahari ne, amma bai kamata ta wuce gona da iri har ta jefa mutum cikin haɗari ko saba wa dokoki."
Daga karshe, Haske ya yi addu'ar Allah ya saka da alheri, ya tsare Dr. Bala Maijama’a Wunti da masoyansa, ya kuma tabbatar da alheri da nasara a duk inda aka nufa da niyya ta gaskiya.
NNPCL ta kori wasu manyan makarantanta
Kun ji cewa kamfanin NNPCL ya kori wasu daga cikin manyan ma'aikatansa bayan sabon shugaban kamfanin, Injiniya Bayo Ojulari ya kama aiki.
Rahotanni sun ce wadanda abin ya shafa sun hada da Bala Wunti, tsohon shugaban sashen zuba jari (NAPIMS) da Ibrahim Onoja, Manajan Daraktan Matatar Man Kaduna.
Majiyoyi sun nuna sabon shugaban ya fara sauye-sauye a ɓangarori daban-daban na NNPCL da nufin kawo gyara da zai amfani Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng