"Na Kira Shugaban APC," Murray Bruce Ya Yi Fatali da Rahoton Hana Shi Takarar Sanata
- Tsohon sanatan Bayelsa ta Gabas, Ben Murray-Bruce ya yi fatali da rahoton cewa APC ta sanya shi a jerin wadanda ba su cancanci takara ba
- Hakan na zuwa ne bayan APC ta fitar sunayen mutane 47 da ba ta amince su nemi takarar sanata a mazabu daban-daban a Najeriya
- Murray-Bruce ya ce ya kira shugaban APC na kasa, Farfesa Netawe Yilwatda domin neman karin bayani kan lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bayelsa, Nigeria - Sunayen masu neman takarar sanata da jam'iyyar APC ta yi fatali da su a matakin tantancewa ya fara tayar da kura.
A yau Litinin, 18 ga watan Mayu, 2026 ne APC ta fitar da sunayen masu neman takara 47 da ta ayyana a matsayin 'ba su cancanci," su shiga zabukan fitar gwani a jihon Najeriya ba.

Source: Facebook
APC ta hana mutane 47 shiga takarar sanata
Jam'iyyar APC ta wallafa sunayen mutanen tare da mazabu da jihohin da suka fito a shafinta na manhajar X.
Daga cikin waɗanda ba a amince su nemi takara ba akwai Ben Murray-Bruce, tsohon sanata wanda ya wakilci Bayelsa ta Gabas tare da Benson Agadaga, wanda shi ma ya tsaya takara a wannan mazaba.
Sai dai bayan jaridar Punch ta wallafa wannan rahoto, tsohon sanatan Bayelsa ta Gabas ya musanta cewa APC ta ki amincewa da takararsa.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a matsayin martani, Ben Murray-Bruce ya tabbatar da cewa yana cikin masu neman takara kuma APC ba ta dakile shi a wurin tantancewa ba.
Murray-Bruce ya karyata hana shi takara
A cikin sakon da ya wallafa, Murray-Bruce ya ce ya yi mamakin ganin rahoton hana shi takara, lamarin da ya sa ya tuntubi shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, domin neman karin bayani.
"Wannan rahoto ƙarya ne (babu gaskiya a cikinsa). Na yi mamakin ganin sa a shafinku (Punch). Hakan ya sa na kira shugaban jam'iyyarmu ta APC, Farfesa Nentawe Yilwatda, domin gano dalilin da ya sa kuka wallafa rahoton.
Ni ban janye daga takara ba, kuma ba a dakatar da ni ba (ba a ce ban cancanta ba). Wannan lokaci ne da abubuwa ke sauyawa cikin sauri.
"Saboda haka zai fi dacewa domin nuna ƙwarewa a aikin jarida ku riƙa yin taka-tsantsan da kuma binciken gaskiyar lamari, maimakon gaggawa wajen bayar da rahotanninku. Allah ya albarkaci Tarayyar Najeriya."

Source: Twitter
APC ta amince da mutane 17 a Kogi
A wani rahoton, kun ji cewa Yahaya Bello da Sanata Sunday Karimi na cikin ’yan takarar da kwamitin tantance APC ya amince su fafata a zaɓen fidda gwani na sanatoci a Kogi.
Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, zai kara da Momoh Yusuf Obaro da Ibrahim Yakubu Adoke domin neman tikitin APC na Kogi ta Tsakiya.
Kwamitin tantance ’yan takarar APC ya amince da ’yan takarar sanatoci 17 daga yankunan sanatoci uku na jihar domin zaɓen fitar da gwani ranar Litinin.
Asali: Legit.ng

