Rigima Ta Barke a Wurin Taro, Matasa Sun Yi kan Dan Majalisar Tarayya, Hon. Yusuf Tafida
- 'Dan Majalisar wakilai daga jihar Taraba, Hon. Sadiq Tafida ya sha da kyar a hannun matasa lokacin da ya koma mazabarsa don neman goyon baya
- Matasa sun tari dan Majalisar gaba da gaba, inda suka zarge shi da yin watsi da mazabar da yake wakilta tun da ya ci zabe
- Lamarin dai ya jawo hayaniya amma daga bisani shugaban karamar hukumar Jalingo, Hon. Nura Dantsoho, ya shiga tsakani don warware matsalar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Taraba, Nigeria - Rahotanni sun nuna cewa an yi wata 'yar rigima tsakanin matasa da 'dan Majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jalingo, Yorro da Zing, Hon. Sadiq Abbas Tafida a jihar Taraba.
Lamarin ya faru ne a makarantar Raddai Metropolitan School da kebrinin Jalingo a yammacin ranar Asabar lokacin da dan Majalisar ya dawo neman goyon bayan jama'a domin ya yi tazarce a zaben fitar da gwanin APC.

Kara karanta wannan
Shugaban majalisa da wasu wakilai 2 sun sha 'kasa a zaben tsiada gwanin APC a Nasarawa

Source: Facebook
Matasa sun tari dan Majalisa a Taraba
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa matasa sun tari Hon Sadiq gaba da gaba, inda suka tuhume shi da watsi da mazabarsa tun bayan nasarar da ya samu a zaben da ya wuce.
Rahotanni sun ce fustattun matasan sun zargi 'dan majalisar da rashin kula da al’ummar mazabar bayan ya lashe zaben shekarar 2024.
A cewar matasan da suka kalubalanci Hon. Sadiq, tun da ya ci zabe bai sake bayyana a yankin ba sai yanzu da ya dawo neman goyon bayansu domin neman tazarce a zaben 2027.
Yadda aka kwantar da hankulan matasa
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa lamarin ya rikide zuwa hayaniya bayan matasan da suka fusata suka tunkari dan majalisar yayin taron.
Sai dai wasu majiyoyi sun ce an samu kwantar da tarzomar ne bayan shugaban karamar hukumar Jalingo, Hon. Nura Dantsoho, ya shiga tsakani.
An ruwaito shugaban karamar hukumar ne ya ceci dan Majalisar tare da rokon matasan su kwantar da hankalinsu, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Kara karanta wannan
"Dama sharrin shaidan ne": Abba ya kawo ƙarshen rikicin Rurum da Kawu Sumaila a Kano
Matakin da Hon. Sadiq ya dauka
Bayanan da aka samu daga Taraba suj nuna cewa daga baya Sadiq Tafida ya tabbatar da tsaron kansa bayan ya bayar da wasu kudade domin kwantar da tarzomar matasan.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga dan majalisar ko mataimakansa dangane da lamarin.

Source: Original
Haka zalika yayin da aka tuntubi jami'in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, ASP Victor Mshelizah, domin jin cikakken bayani, bai amsa kiran waya ba.
Mutanen da APC ta hana su yi takara
A wani rahoton, kun ji cewa Jam’iyyar APC ta fitar da jerin sunayen masu neman takarar kujerar Majalisar Wakilai da ta sanya wa alamar “ba a amince da su ba” a jihohi da dama a Najeriya.
Daga cikin jihohin da masu neman takara suka gaza tsallake matakin tantance wa a APC akwai Ondo, Bauchi , Ebonyi, Kogi da Rivers.
Jam'iyyar APC ta bayyana cewa sunayen na daga cikin wadanda ba su tsallake tsarin tantancewar da jam’iyyar ta gudanar domin tabbatar da cancantar su ba a mazabu daban-daban.
Asali: Legit.ng