Wajibi ne: Gwamnatin Tinubu Ta Fito da Sabon Tsarin Haraji
- Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da sabon tsarin haraji a Najerya, wanda zai tilasta wa kowane dan kasar nan karbar shaidar biyan haraji
- Hukumar tattara haraji ta kasar nan, NRS ta ce sabon tsarin zai haɗa bayanan masu biyan haraji waje guda domin rage maimaici
- Sabuwar lambar harajin da duk wadanda suka isa biyan kudin zai maye gurbin tsohuwar manhajar tantance TIN da hukumomi ke amfani da ita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ƙaddamar da sabon tsarin lambar tantance masu biyan haraji (Tax ID) ga duk mutanen da doka ta tanada su biya haraji a ƙasar nan.
Wannan al'amari na zuwa ne jim kadan bayan yan Najeriya sun yi kuka da sababbin dokokin haraji da shugaba Bola Tinubu ya bijiro da su.

Source: Facebook
Amma hukumar tattara kuɗin shiga ta Najeriya, wato NRS tare da haɗin gwiwar JRB ne suka sanar da sabon tsarin harajin a wata sanarwa da aka wallafa a shafin X ranar Litinin.
An samar da sabon tsarin haraji a Najeriya
A cewar hukumar, an samar da sabon tsarin ne domin a tafi da zamani da inganta harkokin gudanar da haraji tare da ƙarfafa bin dokokin biyan haraji a faɗin ƙasar nan.
NRS ta bayyana cewa sashe na 6, 7 da 8 na dokar kula da haraji ta Najeriya ta shekarar 2025 ne suka bai wa tsarin kariya ta doka, inda aka wajabta wa duk mai biyan haraji samun shaidar haraji da ake kira 'Tax ID'.
Hukumar ta ce sabon tsarin zai zama wata kafa guda ɗaya da za ta haɗa dukkannin bayanan masu biyan haraji domin sauƙaƙa hulɗa tsakanin masu biyan haraji da hukumomin gwamnati a matakin tarayya da jihohi.
A cikin sanarwar, hukumar ta ce:
“Shaidar biyan harajin zai zama wata lamba guda ɗaya da za ta haɗa duk masu biyan haraji, tare da ba su damar gudanar da hulɗa cikin sauƙi da hukumomin haraji na tarayya da na jihohi.”
Ta ƙara da cewa sabon tsarin zai taimaka wajen tattara bayanan masu biyan haraji waje guda tare da kawar da maimaita bayanai da kuma inganta kula da bayanan haraji.
Yadda sabon tsarin haraji zai yi aiki
Hukumar NRS ta ce sabon tsarin zai sauƙaƙa yin rajista, cike takardun haraji da kuma biyan haraji ga ‘yan Najeriya da kamfanoni.

Source: Facebook
A cewar hukumar:
“Sabon tsarin zai sauƙaƙa hanyoyin bin dokokin haraji, daga ciki har da rajista, cike bayanan haraji da kuma biyan haraji.”
Haka kuma, hukumar ta ce tsarin zai ƙara bayyana bayanan masu biyan haraji domin rage almundahana da kuma inganta gaskiya da riƙon amana wajen tattara kuɗin shiga.
A wani ɓangare na sauye-sauyen, NRS ta sanar da cewa sabon tsarin zai maye gurbin tsohuwar manhajar tantance lambar TIN da ma’aikatu, hukumomi, bankuna da sauran cibiyoyi ke amfani da ita a yanzu.

Kara karanta wannan
"Babu hujja," Sojojin Najeriya sun yi magana kan zargin kashe fiye da mutane 100 a Zamfara
An gano wadanda za su biya haraji
A baya, mun wallafa cewa gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa kamfanoni 149 da ke cin gajiyar hutun haraji za su ci gaba da amfana da shi na akalla karin shekaru biyu bayan sabuwar dokar da aka yi.
Matakin na zuwa ne yayin da Najeriya ta fara aiwatar da sabon tsarin haraji daga Janairu, 2026, ba tare da karya yarjejeniyar da aka riga aka kulla da wadannan kamfanoni a baya ba.
Rahotanni sun nuna cewa hukumar NIPC ta ce tsarin zai kare masu zuba jari tare da sauya tsarin hutun zuwa sabon salo na karfafa tattalin arziki yayin da ake nema wa kasa karin kudin shiga.
Asali: Legit.ng

