'Yan Sanda Sun Gayyaci Kakakin Abba kan Kitimurmurar Dakatar da Ganduje daga APC

'Yan Sanda Sun Gayyaci Kakakin Abba kan Kitimurmurar Dakatar da Ganduje daga APC

  • Sufeto Janar na yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya umarci a gurfanar da Kakakin Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa a gabanta
  • Ana zargin Sanusi da hada makarkashiyar da ta jawo wani sashe na APC a karamar hukumar Dawakin Tofa ta dakatar da Abdullahi Ganduje a 2024
  • A baya, Sanusi Bature ya samu kariya daga kotu wadda ta hana ‘yan sanda kama shi bayan tsagin Abdullahi Ganduje ya mika koke ga rundunar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Kayode Egbetokun, ya umarci jami'ansa da su gurfanar da Kakakin Gwamnan Jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, a gaban ofishin rundunar a Abuja.

Wannan na zuwa ne sakamakon zargin ɓatanci da ya shafi dakatarwar tsohon Gwamna, kuma shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje da Kakakin Abba, Sanusi Bature Dawakin Tofa
Yan sanda sun gayyaci Kakakin Abba Sanusi Bature Dawakin Tofa Hoto: Abubakar Baffah/Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa a shekarar 2024, shugabannin jam’iyyar APC na mazabar Ganduje suka dakatar da shi daga mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan mataki ya biyo bayan zargin gudanar da ayyukan da suka saba wa jam’iyya da kuma ayyukan yiwa jam'iyya zagon kasa.

Ganduje: Ana zargin kakakin Abba da makarkashiya

Daily Post ta ruwaito a cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 23 ga Mayu, 2025, da aka aika zuwa Ofishin Sakataren Gwamnatin Kano, Egbetokun, ya nemi Sanusi Bature da ya bayyana gaban SP Mojirode B. Obisiji

Wannan wasiƙar na ɗauke da sa hannun shugaban sashen sanya idanu na Sufeton 'yan sandan, DCP Akin Fakorede ya bukaci Sanusi Bature da ya bayyana a ranar Alhamis, 29 ga Mayu, 2025.

Sufeton yan snadan Najeriya, Kayode Egbetokun
Wannan ne karo na biyu da rundunar ta gayyaci Sanusi Bature Dawakin Tofa Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

A cikin wasiƙar, an bayyana cewa:

“Rundunar ‘yan sanda na bincike kan koken ɓatanci da gangan, cin mutunci da keta doka da zai iya tayar da rikici, wanda ya shafi mai magana da yawun bakin Gwamna na Jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa.”

An taba yunkurin kama kakakin Abba

A watan Disamba na shekarar 2024, Sufeton Janar Egbetokun, ya bayar da umarnin kama Sanusi Bature tare da kai shi hedkwatar leƙen asiri ta ‘yan sanda a Abuja.

Amma a lokacin, kakakin ya samu kariya daga kotu wadda ta hana rundunar ‘yan sanda kama shi ko ci gaba da bibiyarsa da makusantansa.

Rahotanni sun nuna cewa yanzu haka, rundunar ‘yan sanda na ƙara matsa lamba wajen kama Sanusi Bature bisa zargin sa da hannu wajen dakatar da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, a shekarar 2024.

Kwankwaso ya sasanta kakakin Abba da 'Dan Majalisa

A baya, mun wallafa cewa Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya shiga tsakanin rikicin siyasa da ya barke tsakanin wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar NNPP a Kano.

Cece-kuce ya balle a tsakanin 'dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Tofa/Dawakin Tofa/Rimin Gado, Hon. Tijjani AbdulKadir Jobe, da Kakakin Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa.

A cewar wata sanarwa da Sanusi Bature ya fitar, ya tabbatar da cewa Sanata Kwankwaso ya gayyace shi tare da Hon. Jobe domin zaman sulhu, kuma yanzu haka komai ya zama tarihi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.