"Shirun da Muka Yi ba Tsoro ba ne," Gwamna Abba Ya Tura Zazzafan Sako ga Kwankwaso

"Shirun da Muka Yi ba Tsoro ba ne," Gwamna Abba Ya Tura Zazzafan Sako ga Kwankwaso

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya gargadi tsohon ubangidansa na siyasa, Rabiu Kwankwaso da ya ja girmansa
  • Abba Gida-Gida ya bayyana cewa idan Kwankwaso ya ci gaba jifarsa da kalamai mara dadi, to zai fara maida martani
  • Gwamnan ya ce kada a dauki shirun da ya yi a matsayin tsoro, yana mai gargadin cewa zai fara magana idan aka kai shi bango

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya fara gajiya da kalamai mara dadi da tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Kwankwaso ke jefo masa.

Gwamna Abba ya gargadi tsohon ubangidan nasa da cewa ya kamata ya rike girmansa, yana mai cewa shirun da yake yi ba tsoro ba ne.

Gwamna Abba da Kwankwaso.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf tare da tsohon ubangidansa na siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Gwamna Abba ya aika sako ga Kwankwaso

Kara karanta wannan

"Dama sharrin shaidan ne": Abba ya kawo ƙarshen rikicin Rurum da Kawu Sumaila a Kano

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Abba Gida ya yi wannan furuci ne a wurin taron tabbatat da Sanata Kawu Sumaila a matsayin dan takarar sanatan Kano ta Kusu na APC a zaben 2027.

Gwamnan ya ce zaman lafiya a Kano shi ne abin da gwamnatin sa ta fi bai wa muhimmanci, amma idan aka ci gaba da matsa masa, zai fara maida martani.

Wannan ne karo na farko da aka ji Gwamna Abba ya yi raddi ga madugun Kwankwasiyya tun bayan rabuwar da suka yi a farkon wannan shekara ta 2026 da muke ciki.

Yadda Kwankwaso ke sukar Abba Kabir

Kwankwaso ya sha fitowa yana sukar gwamnan Kano, tare da kalaman da ke nuna gori kan taimakon da ya masa har ya samu nasara a zaben 2023.

Ko a baya-bayan nan, madugun Kwankwasiyya ya fito a wata hira da aka yi da shi, ya ce Abba Kabir ya yi babban kuskure da ya fice daga tafiyar Kwankwasiyya, in ji rahoton Aminiya.

Da yake martani a taron tabbatar da takarar Kawu Sumaila yau Litinin, Gwamna Abba ya yi gargadin cewa zai fara bude bakinsa yana maida martani ga Kwankwaso idan aka kai shi bango.

Kara karanta wannan

2027: Martanin Kwankwaso ga zargin yana yi wa Tinubu aiki a NDC

Sakon da Abba ya aika wa Kwankwaso

Abba ya ce:

“Mu dai zaman lafiya a Kano shi ne abin da ya fi muhimmanci a gare mu. Amma idan aka kai mu bango, za mu bude baki mu yi magana. Yin shiru ba alamar tsoro ba ce.
“Ko yin shiru ma ibada ce, ba don muna tsoro ba, ba kuma don mu yara ba ne. Ta yaya mutum mai shekara 69 zai kira mai shekara 63 yaro? Girmamawa da ladabi ne kawai saboda ka fi ni shekaru kadan.
“Amma idan dattijo bai mutunta kansa ba kuma bai yi shiru ba, to matashi zai samu abin fada. Don haka muna hada su da Allah da Manzonsa su rufe bakunansu. In ba haka ba, za ku ji abubuwa masu yawa da za mu tona,” in ji shi.
Abba.
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf yana jawabi yayin ganawa da kwamishinoni Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Abba ya sasanta Rurum da Kawu Sumaila

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sasanta rikicin da ya shiga tsakanin Kabiru Alhassan Rurum da Sanata Kawu Sumaila.

Kara karanta wannan

Magana ta fito, an ji abin da Tinubu ya shirya yi a shekaru 2 na farko bayan ya ci zaben 2027

Rikici ya nemi ya yi kamari a tsakanin manyan wakilan Kano ta Kudu a majalisun tarayyar kasar nan, har an ji Rurum na cewa ya shata layi tsakaninsa da Kawu Sumaila.

Bangarorin biyu sun sanar da cewa sun yafe wa juna tare da warware duk wani sabani da ya shiga tsakaninsu bayan Gwamna Abba ya kashe wutar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262