Gwamna Uba Sani Ya Nada Sabon Sarki Mai Martaba a Jihar Kaduna
- Gwamna Uba Sani ya amince da nadin Suleiman Sa’ad Abubakar a matsayin wanda zai gaji kujerar Sarkin Kagarko da ke karamar hukumar Kagarko
- Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kaduna, Sadiq Mamman, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 18 ga Mayu, 2026
- Gwamna Uba Sani ya taya sabon sarkin murnar hawa karagar mulki tare da bukatar ya yi aiki tukuru wajen karfafa zaman lafiya da hadin kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna, Nigeria - Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya nada sabon Sarki a masarautar Kagarko.
Gwamnan ya amince da nadin Suleiman Sa’ad Abubakar a matsayin sabon Sarkin Kagarko da ke karamar hukumar Kagarko a kudancin jihar Kaduna.

Source: Facebook
Gwamna Uba Sani ya nada Sarkin Kagarko
Jaridar Leadership ta rahoto cewa an sanar da nadin ne a ranar Litinin cikin wata sanarwa da kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kaduna, Sadiq Mamman, ya fitar.

Kara karanta wannan
"Dama sharrin shaidan ne": Abba ya kawo ƙarshen rikicin Rurum da Kawu Sumaila a Kano
Sanarwar ta bayyana cewa nadin Sarkin zai fara aiki ne nan take, ma"ana daga yau Litinin, 18 ga watan Mayu, 2026.
Sabon sarkin, wanda kafin yanzu yake rike da sarautar San Turakin Kagarko, ya gaji marigayi Sa’ad Abubakar wanda ya rasu a watan Janairu da ya gabata.
Yadda aka zabi sabon Sarki a Kagarko
Rahotanni sun nuna cewa marigayi Sarki Sa'ad Abubakar ya rasu ne bayan shafe shekaru shida a karagar mulki.
Sabon Sarkin Kagarko, Suleiman Sa'ad ya kasance dan marigayin, wanda a yanzu ya samu nasarar zama magajin mahaifinsa bayan gudanar da zabe bisa tsari da doka.
Sanarwar ta bayyana cewa Suleiman Sa’ad Abubakar ya samu nasarar zama sabon sarkin ne bayan tsallake duka tsauraran matakai da tsarin zabe da masu nada sarki na masarautar Kagarko suka gudanar.
Gwamna Uba Sani ya tura sakon taya murna
Gwamna Uba Sani ya taya sabon sarkin murnar hawa karagar mulki tare da bukatar ya yi aiki tukuru wajen karfafa zaman lafiya, hadin kai da zaman tare cikin lumana a fadin masarautar.
A cewar mai girma gwamnan, zaman lafiya shi je ginshikin ci gaban kowame al'umma, yana mai kira ga Sarkin ya hada kan al'ummarsa.

Source: Twitter
“Mai girma gwamna, Sanata Uba Aani ya kuma bukaci sabon sarkin da ya ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da jituwa tsakanin al’ummarsa,” in ji kwamishinan.
Gwamnatin jihar Kaduna ta kara da cewa daga baya za a sanar da ranar bikin nadin sarautar da kuma mika sandar mulki ga sabon sarkin.
Uba Sani ya nuna kwarin gwiwa kan Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Uba Sani ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa ’yan Najeriya, musamman 'yan Arewa, za su zaɓi shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Gwamnan na Kaduna ya ce Tinubu ya samu nasarar daidaita tattalin arziƙin Najeriya tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023.
Ya kalubalanci ’yan adawa, waɗanda ke yawan sukar Tinubu, kan sauyin da za su iya kawowa, yana mai cewa har yanzu ba su gabatar da wata mafita mai gamsarwa ba.
Asali: Legit.ng
