Mabiya Obi Sun Fadi Tsarin da Kwankwaso zai Mulki Najeriya a 2031
- Ibrahim Abdulkarim ya bayyana kudirin Peter Obi na yin wa’adi guda ɗaya na shugabanci a matsayin wani ɓangare na dogon shirin sauyin siyasa
- Magoya bayansa na tattauna shirin mika mulki ga Rabiu Musa Kwankwaso domin tabbatar da ci gaba bayan wa’adin Obi na farko ya kare
- Da yake magana kan hakan, Abdulkarim ya jaddada mayar da hankali kan gyaran tsarin mulki da gina ƙwararan hukumomi fiye da nasarar zaɓe kawai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Wani na hannun daman Peter Obi, Ibrahim Abdulkarim, ya ƙara haske kan rahoton alkawarin wa’adi guda ɗaya da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya yi da kuma dogon shirinsa na siyasa gabanin zaɓen 2027.
Ibrahim Abdulkarim a yi magana ne yayin da wasu 'yan siyasa ke nuna shakku kan alkawarin da Obi ya yi na cewa wa'adi daya kacal ya ishe shi.

Kara karanta wannan
An dora Hayatu Deen a gaban Atiku, Obi da Amaechi a takarar zama shugaban kasa a 2027

Source: Facebook
Da yake magana a wata hira da Trust TV ta wallafa a X, Abdulkarim ya ce har yanzu Obi yana nan daram kan kudirinsa na yin wa’adi guda ɗaya idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa.
Martani kan shakka game da Obi
A cewar Ibrahim Abdulkarim, masu shakkar alkawarin Obi ba su fahimci hangen nesa na dogon lokaci da sansanin siyasar shi ke tunani ba.
“Ya ce ko da an daura masa bindiga a kai, wa’adi guda ɗaya zai yi,”
In ji Abdulkarim a yayin hirar.
Ya ƙara da cewa Obi ya yi imanin cewa har yanzu ana iya aiwatar da manyan sauye-sauye cikin shekaru huɗu.
“Wasu mutane sun rusa ƙasa gaba ɗaya cikin shekaru biyu kacal. Wani kuma zai iya zuwa ya sauya alkiblar ƙasa cikin shekaru huɗu sannan ya dawo da hukumominmu su fara aiki yadda ya kamata,”
In ji shi.
Shirin mikawa Obi Kwankwaso mulki
Abdulkarim ya kuma bayyana cewa magoya bayan Obi sun riga sun fara tattauna batun siyasar 201 wanda zai iya kai ga mika mulki ga Rabiu Musa Kwankwaso bayan wa'adin Obi na farko.
A cewarsa, manufar ita ce tabbatar da ci gaba da sauye-sauye bayan gwamnatin Obi:
“Yana da wani da yake aiki tare da shi wanda suka fahimci inda suke son zuwa,”
“To, mika wa Kwankwaso mulki bayan 2031, abin da suke tunani kenan, tunaninmu kenan, shirinmu kenan, abin da muke son yi kenan.”
Ya ci gaba da cewa:
“Muna son daga wajensa a koma wajen Kwankwaso. Wannan shi ne tunaninmu. Haka muke kallon lamarin saboda mun san ci gaba ne.”

Source: Twitter
Ga bidoyon da Abdulkarim ya yi bayani:
Oshiomhole ya caccaki Obi da Atiku
A wani labarin, mun kawo muku cewa Sanata Adams Oshiomhole ya caccaki Atiku Abubakar da Peter Obi yayin da ake maganar 2027.
Adams Oshiomhole ya ce 'yan adawa suna sukar juna a Najeriya, lamarin da ke kara tabbatar da cewa suna taya APC yakin neman zabe.
Sanatan ya kara da cewa duk yadda 'yan adawa za su yi kokari ba za su iya doke shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba a zaben 2027.
Asali: Legit.ng
