Sarkin Musulmi Ya Aika da Sako ga Jami'an Tsaro kan Kisan Binuwai

Sarkin Musulmi Ya Aika da Sako ga Jami'an Tsaro kan Kisan Binuwai

  • Jama'atul Nasril Islam ta bayyana rashin jin dadin yadda jami'an tsaro basa iya kare afkuwar kashe-kashen jama'a a fadin kasar nan
  • Kungiyar a karkashin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ta ce ya kamata a sauya dabarar yaki da rashin tsaro
  • JNI ta kuma shawarci yan Najeriya su daina bari ana amfani da wasu batutuwa wajen rarraba kawunansu don ba zai haifar da da mai ido ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Benue – Jama’atu Nasril Islam (JNI), karkashin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na Sokoto ta bayyana takaicin yadda ake asarar rayuka a Binuwai.

Kungiyar ta bayyana cewa ci gaba da yin shiru kan kashe-kashen da ake ta yi a Jihar Binuwai ba zai haifar da alheri ba ga zaman lafiyar kasa baki daya.

Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar II
Sarkin Musulmi ya yi kakkausan suka a kan kashe-kashe a Binuwai Hoto: Sultan of Sokoto TV
Asali: Facebook

Nigerian Tribune ta wallafa cewa wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakatare Janar na JNI, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu, ya fitar kuma aka rabawa manema labarai a Kaduna ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sultan ya yi takaicin kisan mazauna Binuwai

Rahoton ya ci gaba da cewa Mai Alfarma Sarkin Musulmi yana cikin damuwa matuka da alhinin rikicin da ke sanadin zubar da jini da kuma hallaka rayuka da dama a sassan Jihar Binuwai.

Ya kuma bayyana cewa abin takaici ne yadda ake ta kashe fararen hula da ba su aikata laifin komai ba.

Ya ce:

“Har yaushe za a ci gaba da wannan kisan wulakanci a Najeriya? Me ya sa jami’an tsaro suka kasa gano hare-haren kafin su afku domin dakile su?”
Ana kara kashe jama'a a Binuwai
Sarkin Musulmi ya nemi a kawo karshen kisan Binuwai Hoto: @HyacinthAlia
Asali: Twitter

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya kara da cewa Allah Subhanahu Wa Ta'ala ya haramta kashe ran dan Adam ba tare da hakki ba, kuma akwai tsattsauran hukunci kan masu ta'asar.

Ya ce:

“Don haka bai kamata ace a cikin wani tsarin dimokuradiyya da wayewa ana ci gaba kuma babu hukunci ga wadanda ke aikata laifukan ba.”

Binuwai: JNI ta caccaki sakacin jami’an tsaro

JNI ta ce duk da godiya da ta ke yi wa jami’an tsaro kan kokarinsu, tana da bakin ciki da yadda suke daukar mataki ne bayan an gama aika ta'asa.

Kungiyar ta ce hakan ya zama kamar jiki, domin rikice-rikice da kashe-kashe suna faruwa ne sau da dama kafin a dauki matakin da ya dace domin kare afkuwar harin.

A cewar JNI:

"Yayin da muke jimamin abin da ya faru da mutanen Binuwai, lokaci ne da ya kamata a yi nazari."

Ta bukaci 'yan Najeriya da su guji duk wani tunani ko fahimta da ke raba kan jama’a, su tashi tsaye a matsayin al’umma daya domin kare rayukan jama'a.

Gwamnan Binuwai ya fusata

A baya, kun ji gwamnan Jihar Benue, Reverend Hyacinth Iormem Alia, ya bayyana fushinsa kan harin ta’addanci da wasu makiyaya masu aikata laifuffuka suka kai kan jama'a kan wasu kauyuka.

Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindiga sun mamaye ƙauyen Yelwata a karamar hukumar Guma ta jihar Benue, inda suka kashe sama da mutum 200 tare da kona gidaje da dama.

An gano cewa an kashe akalla mutum 200 tare da ƙona gidaje, lamarin da gwamnan ya kara da cewa zai tabbatar da an farauto tare da hukunta dukkanin wadanda aka tabbatar sun aikata laifin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.