"Ba Kudin Ni Bane": Dirama Yayin Da Wani Ya Hau Karfen Sabis Bayan N500k Sunyi Ɓatar Dabo Daga Bankinsa A Kano

"Ba Kudin Ni Bane": Dirama Yayin Da Wani Ya Hau Karfen Sabis Bayan N500k Sunyi Ɓatar Dabo Daga Bankinsa A Kano

  • Wani mutum da ya hadu da sharrin yan damfara ya hau kololuwar karfen sabis bayan ya ziyarci banki
  • Mutumin ya yi ikirarin cewa fiye da N500,000 ya bata a asusunsa na banki yan mintuna bayan ya samu alat
  • Jami'in hukumar kashe gobara sun ceto shi bayan roko da lallaba cewa za su taya shi kwato kudin

Jihar Kano - Jami'an hukumar kashe gobara na jihar Kano sun ceto wani mutum dan shekara 27 bayan ya hau kololuwar karfen sabis.

BBC ta ambato cewa wani Saminu Yusuf na hukumar kashe gobarar yana cewa mutumin ya na shirin rabuwa da duniya ne bayan N500,000 ya yi batar dabo daga asusun bankinsa.

Hukumar kashe gobara
"Ba Kudin Ni Bane": Dirama A Yayin Da Wani Ya Hau Karfen Sabin Bayan N500,000 Suka Bata Daga Asusunsa Na Banki. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Aiki Ya Kwabe Maku, Ku Je Ku Koyi Dambe, Shehu Sani Ga Ma'aikatan Banki

A cewarsa, ya samu alat din shigar kudi na N500,000 a asusunsa, amma da ya isa bankin sai ya gano babu kudin a asusun.

Yusuf ya yi bayani cewa:

"Mun samu rahoto cewa wani ya hau karfen sabis na ARTV, nan take muka gaggauta zuwa wurin muka lallashe shi ya sako bayan mun dade muna roko.
"Mun yi sa'a, ya yarda ya sako ba tare da wani rauni ba kuma muka mika shi hannun yan sanda.
"Mutumin ya ce kudin da ya yi batar dabo daga asusun bankin ba nasa bane, kuma bai san abin da zai yi ba."

Yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu.

@SemiNigerian ya rubuta:

"Dukkan mu mun san bankin, lokaci ya yi da bankuna za su inganta tsaronsu, mutane na rasa rayukansu da kudin su.

"@chuksmadi shima ya ce:

"Wannan abin takaici ne, wata kila alat din bogi ya samu ko kuma a tuhumi bankin game da kudin."

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Goyi Bayan Buhari, Ya Fallasa Manufar Canja Kuɗi Ana Gab da Zaben 2023

Kungiyar yan kasuwar arewa ta yaba wa Matawalle kan bada umurnin kama duk wanda ya ki karbar tsohuwar takardar naira

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar hadakar yan kasuwar arewa ta yaba wa gwamnan Zamfara, Bello Matawalle kan ba wa jami'an tsaro umurnin kama duk wanda baya karbar tsaffin takardun naira yayin kasuwanci.

Yan kasuwan sun bayyana hakan ne a ranar Asabar 11 ga watan Fabrairun shekarar 2023 a jihar Sokoto, The Punch ta rahoto.

Alhaji Yusuf Nufawa, shugaban matasa na kungiyar yan kasuwar na arewa ya ce wannan matakin da Matawalle ya dauka zai taimaka wurin habbaka kasuwanci da suka yi kasa sakamakon karancin nairan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel