APC Ta Yi Magana kan Zargin Ganduje na Harin Kujerar Kashim Shettima
- Jam’iyyar APC ta zargi wasu 'yan adawa, musamman mabiya tafiyar Kwankwasiyya da yayata hatsaniyar da ta faru da Gombe fiye da kima
- Sakataren yada labaran APC, Ahmed S Aruwa ya shaidawa Legit cewa abin da ya faru ba sabon batu ba ne a siyasa, kuma baya nufin akwai baraka a
- Aruwa ya karyata rade-radin da ke cewa Dr. Abdullahi Ganduje na shirin neman kujerar mataimakin shugaban kasa a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – APC ta zargi wasu 'yan adawa, musamman tafiyar Kwankwasiyya, da kokarin dagula siyasar jam'iyyar kan batun hayaniya da aka samu yayin babban taron Arewa maso Gabas na jam'iyyar.
Ahmed S. Aruwa, Sakataren Yada Labaran APC, ne ya bayyana haka a ranar Litinin, kan yadda aka samu hatsaniya yayin taron da ya gudana a jihar Gombe.

Asali: Facebook
Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya halarci taron, wanda daga baya ya kusan rikidewa zuwa rikici.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan rashin ambaton mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, a cikin tafiyar Bola Tinubu a zaben 2027.
APC ta musanta rikici a jam’iyyarta
A zantawarsa da Legit, Ahmed S. Aruwa ya ce 'yan adawa na neman hanyoyin da za su nuna akwai matsala a cikin APC, bayan da Bola Tinubu ya bayyana cewa rikicin ya dabaibaye su.
Ya ƙara da cewa hargitsin da aka gani ya biyo bayan bayanin da wani (ba shugaban APC ba) ya yi – kalaman da ba su yi wa wasu daɗi ba.
Ahmed S. Aruwa ya ce:
“Yanzu, akwai inda kika gani cewa an yi wa shugaban jam’iyya wani abu na rashin jin daɗi ko rashin mutunci? Da suka ga cewa sun tayar da hayaniya, sai kawai aka raka shugaban jam'iyya da mukarrabansa zuwa mota, tunda dama an kammala taron – tafiya kawai za a yi.”
Ya yi nuni da cewa ba sabon abu ba ne a samu wadanda ba su gamsu da yadda ake gudanar da mulki ba, ko da kuwa 'yan jam’iyya ɗaya ne.
APC ta yi bayani kan takarar mataimakin Tinubu
Da yake amsa tambaya kan zargin cewa Abdullahi Umar Ganduje na neman kujerar mataimakin shugaban ƙasa da Kashim Shettima ke kai a yanzu, Ahmed S. Aruwa ya ce babu wani abu makamancin haka.

Asali: Facebook
Ya ƙara da cewa:
"Babu magana ma mai kama da wannan, ba a taba yin ta ba, ba a taba kawo ta ba. Shi kansa shugaban jam'iyya bai taba hasashen wannan ba, bai taba kawo ta ba, fitina ce kawai ake son a yi amfani da ita, tunda ba a samu gaba a rigimar APC ba, to amma yanzu ya za a yi amfani da wata gaba yadda al'amarin zai lalace baki daya."
Kan batun rashin hoton Kashim Shettima a cikin hotunan jiga-jigan da aka lika a wajen taron, Aruwa ya kare shugaban APC, inda ya ce 'yan APC na yankin ne suka shirya komai.
Taron APC ya rikice a Gombe
A baya, mun wallafa cewa an samu rikici a wani babban taron jiga-jigan jam’iyyar APC na yankin Arewa maso Gabas, wanda aka gudanar a jihar Gombe a ranar Lahadi, 15 ga Yuni, 2025.
Lamarin ya faru ne bayan da Kwamred Mustapha Salihu, mataimakin shugaban jam’iyya na ƙasa daga yankin, ya bayyana goyon bayansa ga shugaban Bola Tinubu amma bai kira sunan Shettima ba.
Da zarar Salihu ya gama jawabin nasa, wakilan da ke wurin taron sun fara bayyana fushinsu – wasu har suna barazanar kai masa hari, lamarin da yasa aka gaggauta fita da Abdullahi Ganduje.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng