Yadda matashi a Gombe ya dale karfen sabis ya ce ba zai sauko ba sai an masa aure

Yadda matashi a Gombe ya dale karfen sabis ya ce ba zai sauko ba sai an masa aure

  • Wani matashi ya hau karfen tirken sadarwar MTN a jihar Gombe, inda ya ce sam ba zai sauko ba sai an saurare shi
  • Lamarin ya faru ne a jihar Gombe a yau Lahadi, inda mutane da dama suka taru don jin me yake bukata
  • A cewar matashin, yana son a yi masa aure ko kuma a hada masa kudade har Naira miliyan biyu

Gombe - Jama'ar unguwar Checheniya dake karamar hukumar Gombe a jihar ta Gombe sun shiga alhini da firgici yayin da wani matashi ya dale karfen tirrken sadarwar MTN, inda ya ce sam ba zai sauko ba sai an biya masa daya daga cikin wasu bukatunsa da ya ambato.

Lamarin da da ya faru a ranar Lahadi 5 ga watan Satumba ya tara dubban jama'a, inda aka samu jami'an tsaro da jami'an taimakon gaggawa da dandazon jama'a yayin da matashin ya ke barazanar hallaka kansa ta hanyar fado wa daga saman karfen.

Kara karanta wannan

Bagudu: Muguntar 'yan bindiga ta fi shafar Fulani, ba mu sauraron labaransu ne kawai

Yadda matashi a Gombe ya dale karfen sabis ya ce ba zai sauko ba sai an biya bukatunsa
Matashin da ya hau karfen tirken sadarwa a Gombe | Hoto: Saif Photography
Asali: UGC

Shaidun gani da ido sun shaida wa wakilin Legit.ng Hausa a jihar ta Gombe cewa, yayin da jami'an agajin gaggawa suka hau karfen domin taimakawa wajen lallabarsa ya sauko, matashin ya kara haurawa sama.

A bangare guda, an samu wasu matasa da abin ya tunzura su, wadanda tuni suka nemo makarar daukar gawa tare da shaida cewa, suna nan suna jiran faduwarsa, kuma daga nan za su wuce dashi makabarta.

Menene bukatarsa?

Matashin da aka ambata sunansa da Umar, ya bayyana bukatar cewa, yana son a yi masa aure ko kuma a bashi kudi Naira miliyan biyu.

Yayin da wakilin Legit.ng Hausa ya tuntubi wani mai daukar hoto, wanda ya samu nasarar dauko hotunan matashin daga sama da na'urar daukar hoto mai saukar ungulu ya ce:

Kara karanta wannan

Shekaru 35 yana aikin koyarwa a Borno, dan Najeriyan da Turawa suka horar ya koma talla

"Gashi nan dai yana saman karfen, ya ce ba zai sauko ba sai an bashi Naira miliyan biyu ko kuma a yi masa aure."

Za a biya masa bukatarsa

Majiyoyi daga kafafen sada zumunta na makusantar shugaban hukumar GOGIS ta Jihar Gombe Dakta Kabiru Usman ta ce, shugaban ya yi alkawarin yiwa matashin aure.

A cewar majiyar, Dakta Kabiru ya bukaci a tuntubi iyayen matashin domin jin ta bakinsu da kuma amincewarsu.

Kalli bidiyon lokacin da yake sama:

Tashin hankali yayin da sojojin Guinea suka kame shugaban kasa, suka kwace mulki

A wani labarin, rahoton BBC ya nuna cewa ba a san makomar shugaban kasar Guinea, Alpha Condé ba bayan wani faifan bidiyo da ba a tantance ba ya nuna shugaban a hannun sojoji, wadanda suka ce sun yi juyin mulki a kasar.

Legit.ng ta tattaro cewa, ministan tsaron kasar, duk da haka, an ambato shi yana cewa yunkurin juyin mulkin ya ci tura.

Kara karanta wannan

An sassauta doka: Mazauna Jos sun garzaya kasuwanni domin sayen kayan abinci

A cewar rahoton, wannan ya biyo bayan harb -harben da aka shafe sa'o'i ana yi a kusa da fadar shugaban kasa a Conakry babban birnin kasar yayin da sojoji ke sintiri kan titunan da ba kowa a kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.