Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin Ya Samu Tikitin Takarar APC a Kano

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin Ya Samu Tikitin Takarar APC a Kano

  • Sanata Barau Jibrin ya samu nasarar lashe tikitin APC na takarar sanatan Kano ta Arewa a babban zaben 2027
  • An tabbatar da takarar Sanata Barau Jibrin ne a taron da ya gudana a hedkwatar jam'iyyar APC da ke karamar hukumar Bichi
  • Mataimakin gwamnan Kano, Murtala Sule Garo da manyan jiga-jigai da magoya bayan APC sun halarci wannan taro yau Litinin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya zama dan takarar jam’iyyar APC na mazabar Sanatan Kano ta Arewa a zaben 2027.

An gudanar da taron tabbatar da shi a hedikwatar APC da ke karamar hukumar Bichi, inda dubban magoya bayan daga kananan hukumomi 13 na mazabar Kano ta Arewa suka halarta.

Barau.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin a taron tabbatar masa da takara a karamar hukumar Bichi Hoto: Barau I. Jibrin
Source: Facebook

Haka kuma jami’ai daga hedikwatar APC ta kasa da wakilan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) sun halarci taron, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisa da wasu wakilai 2 sun sha 'kasa a zaben tsiada gwanin APC a Nasarawa

Barau ya samu tikitin takarar APC

Da misalin karfe 2:20 na rana, shugaban kwamitin zaben fidda gwani na APC na Kano ta Arewa, Hon. Shehu Isa Direba, ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar su tabbatar da Sanata Barau a matsayin dan takarar APC na mazabar.

Da yake jawabi bayan taron, shugaban tawagar INEC mai sanya ido kan zaben, Abdulrahman Haruna, ya bayyana gamsuwarsa da yadda aka gudanar da taron cikin lumana da tsari.

Gwamna Abba ya hango nasarar APC

A nasa bangaren, gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya yaba da yadda aka gudanar da taron cikin kwanciyar hankali.

Mataimakin gwamnan, Murtala Sule Garo, wanda ya wakilce shi, ya nuna kwarin gwiwar cewa al’ummar Kano ta Arewa za su zabi Shugaba Bola Tinubu, Gwamna Abba, Sanata Barau da sauran ‘yan takarar APC a zaben 2027.

“Muna cike da farin ciki, Kano ta Arewa ta APC ce a kowane lokaci. Mu iyali daya ne a APC.

Kara karanta wannan

Maidoki: Sanatan APC a Kebbi ya fice daga jam'iyyar ana dab da zaben fitar da gwani

"Insha Allah, kafin tsakar rana a ranar zabe, Sanata Barau zai lashe kujerarsa, yayin da Shugaba Tinubu da sauran ‘yan takararmu za su yi nasara,” in ji shi.
Barau Jibrin.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin tare da dubbanagoya baya a Kano Hoto: Barau I. Jibrin
Source: Facebook

Sanata Barau Jibrin ya gode wa al'umma

Da yake mayar da martani a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sanata Barau ya gode wa ‘yan APC bisa goyon bayan da suka nuna masa tare da tabbatar musu da cewa zai ci gaba da wakilci nagari.

“Da farko ina gode wa Allah Madaukakin Sarki da Ya ba mu wannan nasara. Ina kuma gode wa Shugaban Kasa kuma Babban Kwamandan Rundunar Sojin Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, bisa jagorancinsa ga APC da kasa baki daya.
“Ina kuma gode wa gwamnanmu, Abba Kabir Yusuf, bisa aikin da yake yi wajen sake gina jihar Kano. Yana aiki tukuru domin cika alkawurran da ya dauka.
"Ina fatan tare da mataimakinsa, Murtala Sule Garo, za su kawo gagarumin ci gaba ga jiharmu ta Kano,” in ji shi.

Sanata Barau ya bukaci al’ummar jihar Kano su zabi dukkan ‘yan takarar APC a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Yusuf Buhari ya san matsayarsa bayan kammala zaben fitar da gwani na APC a Katsina

Sanata Garba Maidoki ya bar APC

An ji cewa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta rasa daya daga cikin sanatocin da take da su a Majalisar dattawa wadanda suka fito daga jihar Kebbi.

Sanata Garba Musa Maidoki, mai wakiltar mazaɓar Kebbi ta Kudu a majalisar dattawa, ya fice daga jam’iyyar APC.

Sanatan ya ɗora alhakin matakin da ya dauka a kan dambarwar cikin gida da ta daɗe tana faruwa a cikin jam’iyyar APC mai mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262