Abin da Trump Ya ce game da Shirin Kai wa Iran Sabon Hari

Abin da Trump Ya ce game da Shirin Kai wa Iran Sabon Hari

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya ce ya dakatar da wani sabon harin soja kan Iran da aka shirya kai wa a ranar Talata, 19 ga watan Mayu, 2026
  • Trump ya bayyana cewa shugabannin ƙasashen Qatar, Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa ne suka roƙe shi ya ba da damar ci gaba da tattaunawa
  • Ya kuma yi gargadin cewa Amurka za ta iya kai wani mummunan hari kan Iran nan take idan ba a cimma yarjejeniyar da za ta gamsar da ita ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Kasar USA – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ya dakatar da wani hari da ƙasarsa ta shirya kai wa Iran bayan roƙon da shugabannin ƙasashen yankin Gulf suka yi masa.

Kara karanta wannan

Trump ya nanata barazanar kawar da Iran daga doron kasa, ya fadi dalili

Trump ya ce shugabannin Qatar, Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa sun nemi Amurka ta dakata domin bai wa tattaunawar sulhu damar gudana.

Amurka ya yi shirin kai wa Iran hari a ranar Talata
Shugaban Amurka Donald Trump, jagoran addini na Iran Mojtaba Khamnei Hoto: Donald J Trump/Imam Sayyid Mojtaba Khamnei
Source: Getty Images

A ruwayar BBC News, an sanar da shi cewa ana daf da kulla wata yarjejeniya da za ta kasance mai matuƙar gamsarwa ga Amurka.

Trump ya dakatar da kai hari Iran

A rahoton da kafar Aljazeera ta wallafa, Shugaba Donald Trump ya jaddada cewa ba za a amince Iran ta mallaki makaman nukiliya ba.

Trump ya rubuta cewa:

“Ana ci gaba da tattaunawa mai muhimmanci, kuma an tabbatar min cewa za a samu yarjejeniya da za ta yi wa Amurka dadi.”

Sai dai shugaban na Amurka ya yi gargaɗin cewa idan har ba a cimma yarjejeniya mai karɓuwa ba, to Amurka za ta iya koma wa kai cikakken hari kan Iran cikin ƙanƙanin lokaci.

Martanin Iran ga kalaman Trump

A martanin da ta mayar, wani babban kwamandan sojin Iran ya gargadi Amurka da kada ta sake yin abin da ya kira kuskuren dabarun soja da rashin kyakkyawan lissafi.

Kara karanta wannan

Rundunar tsaron Najeriya ta karyata bayanan Amurka kan kisan Abu Bilal Al Minuki

Wannan sabon yanayi ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan yiwuwar faɗaɗar rikici a Gabas ta Tsakiya, lamarin da ya sa kasuwannin duniya ke fargaba musamman kan farashin mai.

Amurka ta dakatar da kai harin da ta shirya kai wa Iran
Shugaban Amurka Donald Trump a ofishinsa da ke White House Hoto: @Radiotv10rwanda
Source: Twitter

Rahotanni sun nuna cewa farashin mai ya sauka bayan furucin Trump na cewa ya dakatar da harin da aka shirya kai wa Iran.

Haka kuma, sabon matakin na Trump na zuwa ne yayin da kuri’un jin ra’ayin jama’a ke nuna raguwar farin jininsa a gida.

Wani binciken jin ra’ayin jama’a da jaridar New York Times tare da Siena suka gudanar ya nuna cewa 64% na masu jefa ƙuri’a a Amurka na ganin shiga yaƙi da Iran kuskure ne.

Masana harkokin tsaro na ganin dakatar da harin na iya bai wa ɓangarorin damar cimma matsaya ta diflomasiyya, duk da cewa barazanar rikici tsakanin Amurka da Iran na ci gaba da ƙara ɗaukar hankali a duniya baki ɗaya.

Trump ya nanata barazanar shafe Iran

A baya, mun kawo labarin cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya sake gargadin Iran kan amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya a Gabas ta Tsakiyta a cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

'Saboda wasu ƙasashe ne': Trump ya fadi dalilin tsagaita wuta a yaƙi da Iran

Rahotanni sun ce shugaba Trump da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu sun tattauna kan rikicin Iran da yiwuwar sababbin hare-hare, yayin da ake kokarin kawo karshen tashe-tashen hankula.

Iran ta zargi Amurka da rashin sassauci a tattaunawar tsagaita wuta da kawo ƙarshen rikicin yayin da aka shafe watanni ana buga wa, sannan ta jaddada matsayarta na cewa babu mai yi mata barazana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng