An Kori Manyan Ma'aikata daga Aiki da Gwamnatin Tinubu Ta Fara Sauye Sauye a NNPCL
- NNPCL ya kori wasu daga cikin manyan ma'aikatansa bayan sabon shugaban kamfanin, Injiniya Bayo Ojulari ya kama aiki
- Rahotanni sun nuna sabon shugaban ya fara sauye-sauye a ɓangarori daban-daban na NNPCL da nufin kawo gyara da zai amfani Najeriya
- Wannan dai na zuwa ne bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sallami Malam Mele Kyari tare da maye gurbinsa da Ojulari
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Manyan ma'aikata da dama sun rasa ayyyukansu a kamfanin mai na ƙasa watau NNPCL tun bayan korar Malam Mele Ƙyari daga matsayinsa na shugaba.
Rahotanni sun nuna cewa NNPCL ya kori wasu daga cikin mutanen Kyari da sabon shugaban kamfanin, Injiniya Bayo Ojulari, ya fara aiwatar da sauye-sauye.

Asali: UGC
An kori manyan ma'aikata a NNPCL
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa wadanda abin ya shafa sun hada da Bala Wunti, tsohon shugaban sashen zuba jari (NAPIMS) da Ibrahim Onoja, Manajan Daraktan Matatar Man Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban matatar Fatakwal da ta Warri na daga cikin waɗanda kamfanin NPCL ya kora daga aiki, kamar yadda The Nation ta kawo.
Haka nan kuma rahoton ya nuna cewa an kori jami’in kula da da’a kuma tsohon Manajan Daraktan sashen kasuwanci na kamfanin NNPCL, Lawal Sade.
Wannan sauye-sauye ya shafi sama da ma'aikata 200, inda aka nada Maryam Idrisu a matsayin sabuwar Manajan Darakta na NNPC Trading, bangaren da ke da alhakin dukkanin harkokin sayar da danyen mai.
Kamfanin NNPCL ya fara sauye-sauye
Bugu da ƙari an kuma naɗa Obioma Abangwu a matsayin jami’in kula da harkokin gudanarwa na kamfanin NNPCL.
A kwanakin baya, an samu labarin cewa NNPCL na shirin ci gaba da sauke wasu shugabanni a hedikwatarsa da ke Abuja da kuma rassan jihohi.
Kamfanin ya ɗauki wannan matakai ne yayin da Injiniya Ojulari ya kama aiki a matsayin sabon shugaban NNPCL na ƙasa.
Rahoton ya bayyana cewa sauye-sauyen za su fara ne daga babban ofishin NNPCL zuwa sauran sassa kamar ɓangaren haƙo mai, kasuwanci da ɓangarorin gas da makamashi.
An dai yi sauye-sauyen ne da nufin tabbatar da cewa an sa ma'aikata a wuraren da suka dace domin kawo ci gaba mai amfani a fannonin fetur da gas.

Asali: Twitter
Bangarorin da NNPCL ya yi sauye-sauye
Wasu daga cikin sassan da sauye-sauyen suka shafa sun hada da:
NNPC E&P Limited (NEPL)
NNPC Upstream Investment Management Services (NUIMS)
NNPC Energy Services Limited (EnServ)
NNPC Engineering and Technical Company (NETCO)
NNPC New Energy Limited (NNEL)
NNPC Gas Infrastructure Company (NGIC)
NNPC Gas Marketing Limited (NGML)
NNPC Gas & Power Investment Services (NGPIS)
NNPC Trading Limited (NTL)
NNPC Retail Limited (NRL)
NNPC Shipping Limited (NSL)
NNPC RefChem Limited (NRCL)
NNPC Downstream Investment Services (NDIS)
Nigerian Pipelines and Storage Company (NPSC)
National Energy Reserve Management Company (NERMC)
NNPC Non-Energy Investment Services (NNIS)
NNPC Foundation
NNPC Academy
NNPC Properties Limited (NPL).
An buƙaci Minista ya binciki Mele Kyari
A wani labarin, kun ji cewa an buƙaci gwamnatin tarayya ta binciki tsohon shugaban NNPCL da aka kora, Malam Mele Kyari.
Hakan ya fito ne daga wasu masu zanga-zanga da suka mamaye ofishin Antoni Janar kuma ministan shari'a Lateef Fagbemi (SAN), a ranar Talata a Abuja.
Har ila yau, masu zanga-zangar ƙarƙashin ƙungiyar CCA sun nemi gwamnati ta gurfanar da Mele Ƙyari a gaban ƙuliya.
Asali: Legit.ng