Wata Sabuwa: DSS Ta Kara Kama Malam El Rufai bayan Kotu Ta ba da Belinsa a Abuja

Wata Sabuwa: DSS Ta Kara Kama Malam El Rufai bayan Kotu Ta ba da Belinsa a Abuja

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya fada hannun jami'an hukumar DSS bayan kammala zaman babbar kotun tarayya a Abuja
  • Hakan dai na zuwa ne biyo bayan belin da aka ba tsohon gwamnan a zaman kotu na yau Litinin, 18 ga watan Mayu, 2026
  • Hajiya Aisha Nasir El-Rufai ta bayyana irin barazanar da suke fuskanta tun bayan kama mijinta, ta kuma roki DSS ta bi umarnin kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Dakarun Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) sun kama tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai jim kadan bayan babbar kotun tarayya ta ba da belinsa.

Iyalan tsohon gwamnan sun nuna damuwa jan yadda jami'an DSS suka cafke El-Rufai, suka tafi da shi ofishinsu bayan zaman kotu a Abuja yau Litinin.

Kara karanta wannan

Hukumar DSS ta sake gurfanar da El Rufai, yana fuskantar sababbin tuhume tuhume

El Rufai.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma babban jigo a ADC, Malam Nasir El-Rufai Hoto: @elrufai
Source: Facebook

A cewar iyalan, matakin ya saba umarnin kotu da ya tanadi cewa El-Rufai ya ci gaba da zama a hannun Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ICPC), kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Ana yi wa iyalan El-Rufai barazana

Matar El-Rufai, Aisha Nasiru El-Rufai, wadda ta yi magana da manema labarai a kusa da ofishin DSS, ta ce iyalansu suna rayuwa cikin tsoro saboda barazana da kuma bibiyar da ake yi musu.

“Yanzu muna rayuwa cikin fargaba kullum. Kowace rana muna samun barazana cewa DSS za ta kai farmaki gidanku, ICPC za ta zo gidanku ko kuma ‘yan sanda za su kai samame. Ana bibiyarmu kuma ana sauraron wayoyinmu,” in ji ta.

Ta bayyana cewa tun da fari a ranar Litinin, El-Rufai ya gurfana a gaban Mai shari’a Joyce AbdulMalik na Babbar Kotun Tarayya, inda aka ba shi beli sannan aka dage shari’ar zuwa karfe 1:00 na rana.

Yadda DSS ta sake kama El-Rufai

Kara karanta wannan

El Rufai: Kotu ta bada belin tsohon gwamnan Kaduna, ta kafa sharuda masu tsauri

A lokacin hutun zaman kotun ne, ta ce an yi yunkurin kai shi ofishin DSS, amma ya ki amincewa, yana mai cewa akwai umarnin kotuna biyu daga Kaduna da suka tanadi cewa a ci gaba da tsare shi a hannun ICPC.

“Haka ya fada musu cewa ba zai fito daga motar ba saboda akwai umarnin kotu biyu da suka ce ICPC ta tsare shi. Ya tambaye su dalilin da ya sa ake son kai shi DSS. Ya ce, ‘Ni ba kayan daki ba ne da za a rika motsawa daga wuri zuwa wuri,’” in ji Aisha.

Ta ce daga baya an mayar da shi ICPC, amma bayan zaman kotun da rana, inda masu gabatar da kara suka nemi dage shari’ar zuwa washegari, sai aka sake kai shi DSS maimakon mayar da shi hannun ICPC.

Hukumar DSS.
Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a kan aiki a Najeriya Hoto: @OfficialDSSNig
Source: Twitter

A rahoton The Nation, iyalan tsohon gwamnan sun bukaci a gaggauta mayar da shi hannun ICPC kamar yadda umarnin kotu ya tanada, a dawo masa da damar ganin likitocinsa.

Kotu ta ba da belin Nasir El-Rufai

An ji cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada belinntsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, kan kudi N100m tare da sharudda masu tsauri.

Kara karanta wannan

"Dama sharrin shaidan ne": Abba ya kawo ƙarshen rikicin Rurum da Kawu Sumaila a Kano

Kotun ta ce dole ne Malam Nasir El-Rufai ya gabatar da mutum daya da zai tsaya masa a matsayin wanda zai karbi belinsa.

Mai shari’a ta kara da cewa dole ne wanda zai tsaya wa El-Rufai ya kasance ma’aikacin gwamnatin tarayya wanda bai gaza mataki na 17 ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262