Kawu Sumaila: Sanatan Kano, Ya Fice daga NNPP Kwanaki bayan Gana wa da Ganduje

Kawu Sumaila: Sanatan Kano, Ya Fice daga NNPP Kwanaki bayan Gana wa da Ganduje

  • Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa, AbdulRahman Kawu Sumaila ya bayyana karshen siyasar a NNPP
  • A yammacin Laraba ne Sanatan ya tabbatar da cewa ya fice daga jam'iyyar, bayan an shafe lokaci ana jiran a ji matakin da zai dauka
  • Sanatan bai bayyana jam'iyyar da ya koma ba, amma ana hasashen ya bi jam'iyya mai mulki da ke hannun Abdullahi Ganduje

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Sanata mai wakiltar yankin Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa, Abdurrahman Kawu Sumaila, ya tabbatar da cewa ya fice daga jam'iyyarsa ta NNPP.

A cewar Sanatan, wannan mataki nasa ya samo asali ne daga jajircewarsa wajen inganta jin daɗin al’ummarsa da kuma cika alkawuran da ya dauka a matsayinsa na wakilinsu.

Sumaila
Kawu Sumaila ya bar NNPP Hoto: AbdulRahman Kawu Sumaila
Asali: Facebook

Sanata Kawu ya bayyana hakan ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya sanar da sabuwar matsayarsa a siyasa bayan shafe lokaci ana hasashen zai bar NNPP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Na fice daga jam'iyyar NNPP” – Kawu Sumaila

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Sanata Kawu Sumaila ya tabbatar mata da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP.

Ya ce:

“Eh gaskiya ne. Rahotannin da ke cewa na fice daga jam’iyya gaskiya ne. Tun farko abin da na fi bai wa muhimmanci shi ne jin daɗin al’ummata — har yanzu kuma hakan ne burina.”

Dalilin ficewar Sanata Sumaila daga NNPP

Sanatan ya ce manufarsa har kullum ita ce ci gaban jama’arsa da tabbatar da wanzuwar walwala da jin daɗi a rayuwarsu ta yau da kullum.

Sumaila
Sanatan Kano ta Kudu, AbdulRahman Kawu Sumaila Hoto: AbdulRahman Kawu Sumaila
Asali: Facebook

Kawu Sumaila ya ce:

“Na kuduri aniyar ci gaba da kokarin inganta rayuwar mutanen da nake wakilta, tare da tabbatar da cewa bukatunsu na yau da gobe sun samu kulawa da mafita.”

Kodayake har yanzu bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba, ficewarsa Kawu daga NNPP na nuna wani babban sauyi a harkokin siyasar jihar Kano.

NNPP: Kawu ya jima da rabuwa da Kwankwasiyya

Sanata Kawu ya bayyana rabuwa da tafiyar Kwankwasiyya da kuma jam’iyyar NNPP mai alamar littafi a kwanakin baya, wanda hakan ya nuna yana da sabani da jagororin tafiyar. A baya-bayan nan ne dai jagororin NNPP da ke mubaya'a ga Rabi'u Musa Kwankwaso suka dakatar da shi tare da wasu ‘yan majalisa biyu – Kabiru Alhassan Rurum da Ali Madakin Gini. Sai dai su ukun sun musanta dakatarwar, su na cewa ba sa daga cikin rukunin jam’iyyar da ya yanke wannan hukunci, saboda haka su halastattun 'yan NNPP ne.

Alakar Kwankwaso da Sumaila

Dangantaka tsakanin Sanata AbdulRahman Kawu Sumaila da Rabi’u Musa Kwankwaso ta samo asali ne daga siyasar Kano, musamman tun lokacin da duka biyun suka kasance a tafiyar Kwankwasiyya.

Kawu Sumaila, wanda ya taɓa kasancewa Kakakin Marasa Rinjaye a Majalisar Wakilai, ya kasance ɗaya daga cikin jiga-jigan da suka mara wa Kwankwaso baya a lokacin da ya kafa tafiyar Kwankwasiyya da kuma a lokacin da suka koma jam’iyyar NNPP tare da gina ta da tushe a jihar Kano.

Rahotanni sun nuna cewa akwai rashin jituwa tsakanin Sumaila da wasu manyan jiga-jigan Kwankwasiyya, ciki har da Kwankwaso kansa, musamman kan yadda aka gudanar da harkokin jam’iyya da rabon mukamai.

Kawu Sumaila ya nuna rashin jin daɗinsa da yadda tafiyar Kwankwasiyya ke tafiya, har ta kai ga dakatar da shi daga jam’iyyar NNPP tare da wasu ‘yan majalisa biyu.

Wannan mataki ya ƙara tabbatar da dambarwar siyasa tsakanin su da Kwankwaso, inda Sumaila ya musanta dakatarwar yana mai cewa ba a bi doka ba, kuma wadanda suka yi hakan ba su da hurumin yanke irin wannan hukunci.

Sabani tsakanin su ya ƙare da Kawu Sumaila ya fice daga NNPP, wanda hakan ke nuna ƙarshen dangantaka ta siyasa tsakaninsa da Kwankwaso, tare da alamar komawa ga APC – jam’iyyar da ke karkashin shugabancin babban abokin hamayyar Kwankwaso, Abdullahi Ganduje.

Wannan sauyi na iya ƙarfafa APC a Kano, yayin da yake rage karfin Kwankwasiyya a arewacin Najeriya.

Kawu Sumaila ya magantu kan barin NNPP

A wani labarin, kun ji cewa Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Abdulrahman Kawu Sumaila, ya bayyana cewa ya fara tuntuɓar jama’arsa a kan yiwuwar komawa APC.

Wannan na zuwa ne bayan da wasu manyan APC daga ƙananan hukumomi 16 na Kano ta Kudu suka nemi ya dawo cikin jam’iyyar tare da tattaunawa da Abdullahi Ganduje.

Shugaban APC na ƙaramar hukumar Albasu, Iliya Jibrin Hungu, ya ce dawowar Kawu Sumaila jam’iyyar zai haɓaka ƙarfinta a yankin tare da ba ta damar nasara a zaben gaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.