Shugaba Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya daga Arewa maso Yamma gabanin 2027

Shugaba Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya daga Arewa maso Yamma gabanin 2027

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya fara tattara goyon bayan ƴan Arewa gabanin babban zaɓen da ke tafe a 2027
  • Shugabanni da masu ruwa da tsakin APC a Arewa maso Yamma sun ayyana goyon bayansu ga tazarcen Bola Tinubu
  • Sun cimma matsayar ne a taron da suka yi a Kaduna wanda ya samu halartar gwamnoni, ƴan majalisa da jiga-jigan APC a yankin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Jam’iyyar APC reshen Arewa maso Yamma ta amince da marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin ya zarce zango na biyu a 2027.

Manyan kusoshin APC a shiyyar Arewa maso Yamma da suka haɗa da gwamnoni, sanatoci, tsofaffin gwamnoni da sauransu sun amince Tinubu ya yi tazarce.

Shugaban kasa Tinubu.
Masu ruwa da tsakin APC a Arewa maso Yamma ya amince Tinubu ya zarce wa'adi na biyu a 2027 Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Punch ta rahoto cewa wannan amincewa ta fito ne daga taron tattaunawa na Jiga-jigan APC na yankin, wanda aka gudanar a ranar Asabar a jihar Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane goyon baya Tinubu ya samu a Arewa?

Kakakin Majalisar Wakilan Tarayya, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ne ya gabatar da kudurin goyon baya ga Tinubu a karo na biyu, yayin da Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya mara masa baya nan take.

Daga nan ne shugabannin APC a Arewa maso Yamma suka kaɗa kuri'ar amincewa da tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Bayan haka ne Gwamnan jihar Kaduna kuma jagoran APC na Arewa maso Yamma, Sanata Uba Sani, ya karanta wata takaitacciyar sanarwa daga taron.

A madadin masu ruwa da tsakin APC a Arewa maso Yamma, Gwamna Uba Sani ya bayyana cikakken goyon bayan yankin ga Tinubu da gwamnatinsa.

APC ta ba gwamnoni 5 tikitin tazarce a 2027

Sakamakon goyon bayan da suka ba Tinubu, jam'iyyar APC ta yanke shawarar bai wa duka gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma tikitin neman tazarrce a zaɓen 2027.

Ma'ana dai APC ta ba gwamnonin jihohin da take mulki guda biyar a yankin, Katsina, Kaduna, Kebbi Sakkwato da Jigawa tikitin neman wa'adi na biyu babu hamayya.

APC ta Arewa maso Yamma.
Gwamnonin jihohi 5 a Arewa maso Yamma sun samu tikitin tazarce a 2027 Hoto: @Abdool85
Asali: Twitter

Jerin waɗanda suka halarci taron APC a Kaduna

Manyan mutanen da suka halarci wannan taro a Kaduna sun haɗa da, shugabannAPC na ƙasa Dr. Abdullahi Ganduje da gwamnoni; Uba Sani (Kaduna), Nasir Idris (Kebbi), Umar Namadi (Jigawa)

Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin sun halarci taron a Kaduna.

Sauran ƙusoshin da aka gani a wurin sune ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu, da takwaransa na ma'aikatar muhalli, Balarabe Abbas Lawal.

Tsofaffin gwamnoni; Aminu Bello Masari (Katsina), Ahmed Sani Yerima (Zamfara), Mahmud Shinkafi (Zamfara), Adamu Aliero (Kebbi) da tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani (Kaduna) sun halarci taron.

APC za ta maida Najeriya hannun jam'iyya 1?

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta ƙasa ta bayyana cewa ko kaɗan ba ta da niyyar juya akalar Najeriya ta koma jam'iyya ɗaya ke mulki.

Sakataran yaɗa labaran APC, Felix Morka ya ce sauya sheƙar da wasu ƴan adawa ke yi zuwa APC ba yana nufin jam’iyyar na neman kafa tsarin jam’iyya ɗaya ba ne.

Ya ce lokacin da jam’iyyar PDP ke kan mulki, tana da iko a jihohi fiye da 28, amma babu wanda ya zarge ta da wani abu mai kama da haka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262