Kawu Sumaila Ya Hada Kai da Barau wajen Yi wa NNPP da Abba Barna a Kano

Kawu Sumaila Ya Hada Kai da Barau wajen Yi wa NNPP da Abba Barna a Kano

  • Sanata Barau Jibrin ya karɓi wasu kungiyoyi biyu na jam’iyyar NNPP da suka fice daga Kwankwasiyya kuma suka shiga APC a Majalisar Dattawa
  • Ɗaya daga cikin rukunin ya haɗa tsofaffin kansiloli daga Sumaila, yayin da ɗaya kuma ke wakiltar mazauna Kano a birnin tarayya Abuja
  • ‘Yan kungiyar sun ce an zalunce su a tafiyar Kwankwasiyya, kuma yanzu sun sauya taken su zuwa "Tinubu-Barau Kawai Alherin Kanawa"

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya karɓi wasu gungun ‘yan jam’iyyar NNPP suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a ranar Talata.

Sanata Barau ya karɓi rukunin ne a ofishinsa da ke Majalisar Dattawa a Abuja, tare da rakiyar wasu sanatoci da manyan ‘yan siyasa daga yankin Arewa maso Yamma.

Barau
Barau ya karbi 'yan NNPP zuwa APC a Abuja. Hoto: Barau I. Jibrin
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan sauya shekar ne a cikin wani sako da Sanata Barau Jibrin ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsofaffin ‘yan Kwankwasiyya sun ce sun fice daga tafiyar ne saboda rashin adalci da suka fuskanta, tare da bayyana goyon bayansu ga Tinubu da Sanata Barau.

Tsofaffin kansilolin Kano sun koma APC

Rukunin farko da Barau ya karɓa ya haɗa da tsofaffin kansiloli 11 daga mazabu 11 na karamar hukumar Sumaila ta jihar Kano.

Sun iso tare da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, wanda ke wakiltar Kano ta Kudu kuma shugaban kwamitin man fetur na Majalisar Dattawa.

Sanata Barau da shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Michael Opeyemi Bamidele, ne suka tarbe su cikin farin ciki da fatan alheri.

'Yan Kano mazauna Abuja sun koma APC

Rukunin na biyu kuma ya ƙunshi wasu ‘yan asalin Kano da ke zaune a Abuja, karkashin sunan “44 LGAs Kano Mazauna Abuja”.

Jagoran kungiyar, Hon. Sunusi Mustapha Dan Alhaji, da shugabar mata, Hajiya Amina Abdullahi, ne suka jagoranci taron da ya samu halartar Sanata Muntari Dandutse daga jihar Katsina.

Sun bayyana cewa sun shafe shekaru suna goyon bayan Kwankwasiyya tun daga 1999, amma yanzu sun fahimci an rinƙa cutar da su a cikin tafiyar.

An maye gurbin taken Kwankwasiyya

A yayin taron, ‘yan kungiyar sun bayyana cewa sun sauya taken da suka dade suna amfani da shi na “Abba Kawai Alherin Kanawa” zuwa “Tinubu-Barau Kawai Alherin Kanawa”.

Barau
Barau yayin karbar 'yan NNPP a Abuja. Hoto: BArau I. Jibrin
Asali: Facebook

Sanata Barau ya bayyana jin daɗinsa da wannan sauyin da suka yi, ya ce za su ci gaba da haɗa gwiwa da su domin nasarar jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.

Ya kuma tabbatar musu da cewa za su samu cikakken goyon baya a jam’iyyar APC, yana mai jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin shugabanni da al’umma.

Matasan Arewa sun gana da Sanata Barau

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Barau Ibrahim Jibrin ya gana da wata kungiyar matasan Arewacin Najeriya.

Kungiyar matasan ta fitar da tsari na musamman domin samawa Bola Tinubu nasara a zaben 2027 mai zuwa.

A karkashin tsarin da suka fitar, matasan sun bayyana cewa za su samawa Bola Tinubu sama da kuri'a miliyan biyar a jihohin Arewa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng