Kawu Sumaila: Sanatan Kano Ya Fadi Dalilinsa na Barin NNPP zuwa APC
- Sanata AbdulRahman Kawu Sumaila ya bayyana cewa ficewarsa daga jam’iyyar NNPP na da alaka ta kai tsaye da mutanen Kano ta Kudu
- A cewarsa, ya yanke shawarar barin jam’iyyar ne saboda yana son ci gaba da kawo wa mazabarsa mafita da ci gaba da ba zai samu a NNPP ba
- Ya ce ko da yake ya fice daga jam’iyyar da ke mulki a Kano, hakan ba zai kawo wata matsala a dangantakarsa da gwamnatin jihar ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Sanata AbdulRahman Kawu Sumaila ya yi magana awanni kaɗan bayan ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP a yammacin Laraba.
Ya bayyana cewa ya fice daga NNPP ne saboda maslahar al’ummarsa, da kuma don samar musu da mafita ta gari.

Asali: Facebook
A hira da ya yi da BBC Hausa, Kawu Sumaila ya bayyana cewa ya bar NNPP ne saboda yana da wata dama yanzu da zai iya kawo ci gaba ga al’ummarsa — wanda bai samu damar yi a baya ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin Kawu Sumaila na ficewa daga NNPP
Kawu Sumaila ya ce akwai dalilai da dama da suka sa suka bar NNPP, amma mafi muhimmanci shi ne kula da yankinsu don samo musu abin arziki. Sanata Kawu ya ce:
"Wasu daga cikin dalilanmu shi ne maganar yankin da muka fito — yaya za mu yi mu iya samowa yankinmu wani abu da zai amfanar da su. Ka ga kuma ita siyasa yarjejeniya ce, tattaunawa ce da neman maslaha ga al’umma.”
Kawu Sumaila ya musanta yi wa NNPP butulci
Sanatan Kano ta Kudu a majalisar dattawa ya ce NNPP ta taka muhimmiyar rawa a zabukan da suka gabata.

Asali: Facebook
Ya ce:
"NNPP ta taka rawar gani a zabe na, Ni ma ba taka rawar gani a zabenta."
"Babu wanda zai iya cewa shi kawai ne ya dinka wa wani riga, sanda ka dinka wa wani riga, shi kuma shi ya dinka maka wando."
Kawu Sumaila ya bayyana cewa ficewarsa daga NNPP ba za ta kawo baraka tsakaninsa da gwamnatin Kano ba, musamman wajen gudanar da ayyukan ci gaba a jihar.
Kawu: 'Ban yi nadamar barin NNPP ba'
Sanata Kawu Sumaila ya ce yana kallon cewa sauya shekarsa za ta habaka abin arziki ga jama'ar da ya ke wakilta.
Ya ce:
"Da wanda ya ke yin magana da Allah? Duk ba a wajen Allah ake nema ba?"
Ya tabbatar da cewa ba shi da wata nadama ko da na sani a kan barin NNPP, domin kowa na duba mafitarsa da ta al'ummarsa ne.
'NNPP ta yi rashi,' Hadimin Kawu Sumaila
Abbas Adam Abbas, Mai taimakawa na musamman kan yada labarai da hulda da jama'a ga Kawu Sumaila, ya yi magana kan fargabar ware Sanatan a APC.
Abbas ya shaida wa Legit cewa jam’iyyar NNPP ta rasa babban dan siyasa, wanda APC ta ke marmari, saboda haka zai yi wahala a nuna masa wariya. Ya ce:
"Ki duba duk irin ayyukan da ya kawo a yankin, ki kalli dimbin ayyukan da ya kawo, ki ga yadda al'umma suke mararinsa, a ce kuma sai jam'iyya ta ajiye shi, gaskiya ina ga wannan abu ne mai matukar wahala."
Abbas ya kara da cewa jam’iyyar NNPP ta rasa wani jigo a cikinta, wanda saboda shi aka ci zaben Kano ta Kudu a 2023.
Sanata Kawu Sumaila ya bar NNPP
A wani labarin, kun ji cewa Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa, AbdulRahman Kawu Sumaila, ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP.
Sanatan ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne domin cika alkawari da kuma ci gaba da kare muradun al’ummar da ya ke wakilta bayan tsawon lokaci ana tattaunawa.
Kawu Sumaila ya ce manufarsa tun farko ita ce kare ci gaban jama’arsa, tare da tabbatar da cewa wakilcinsa ya zamo alheri ga rayuwar yau da kullum ta masu kada masa ƙuri’a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng