Shugaba Tinubu Ya Shawo kan Sanatocin PDP 3, Za Su Sauya Sheƙa zuwa APC

Shugaba Tinubu Ya Shawo kan Sanatocin PDP 3, Za Su Sauya Sheƙa zuwa APC

  • Sanatocin jam'iyyar PDP daga jihar Kebbi sun gana da Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja yau Juma'a
  • Bayan wannan ganawa, sanatocin sun bayyana shirinsu na ficewa daga jam'iyyar adawa ta PDP da ta ba su nasara zuwa APC mulkin ƙasar nan
  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne ya jagoranci sanatocin zuwa wurin mao girma shugaban ƙasa a Aso Rock

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Sanatoci uku masu ci daga Jihar Kebbi, waɗanda aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar adawa ta PDP, sun amince za su sauya sheƙa zuwa APC mai mulki.

Sanatocin sun bayyana matsayarsu ne bayan wata gana wa da suka yi da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnati da ke Abuja yau Juma'a.

Sanatocin Kebbi da Tinubu.
Sanatocin PDP 3 daga Kebbi sun amince za su sauya sheƙa zuwa APC Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta tattaro cewa manyan kusoshin gwamnati da shugabannin jam'iyyar APC sun halarci taron wanda ya gudana yau 8 ga watan Mayu, 2025 a Aso Rock.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jerin sanatocin PDP da Tinubu ya gana da su

Sanatocin da suka amince za su koma APC sun haɗa da, Sanata Adamu Aliero mai wakiltar Kebbi ta Tsakiya, Sanata Yahaya Abubakar Abdullahi mai wakiltar Kebbi ta Arewa da Sanata Garba Maidoki mai wakiltar Kebbi ta Kudu.

Rahotanni sun nuna cewa sanatocin sun ziyarci fadar shugaban ƙasa ne karƙashin jagorancin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Ana ganin dai wannan mataki da sanatocin suka ɗauka na barin PDP zuwa APC wani babban sauyi ne da ka iya canza akalar siyasar jihar Kebbi, The Cable ta tattaro.

Har ila yau ana ganin idan sanaton Kebbi suka koma jam'iyyar APC, za a samu canji a harkokin Majalisar Dattawa da shirye-shirye da za su taso nan gaba.

Wadanda suka halarci ganawar Tinubu da Sanatocin

Waɗanda suka halarci ganawar Shugaba Tinubu da sanatocin sun haɗa da gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris (Ƙauran Gwandu da takwaransa na Sakkwato, Ahmad Aliyu.

Sauran jiga-jigan da aka hanga a ɗakin ganawar su ne ministan kasafin kudi da tsare-tsaren kasa kuma tsohon gwamnan jihar Kebbi, Sanata Atiku Bagudu.

Shugaba Tinubu.
Shugaba Tinubu ya shawo kan sanatocin Kebbi za su dawo APC Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Ana sa ran sauya shekar sanatocin zai ƙara ƙarfin APC a jihar Kebbi da kuma yawan mambobin jam'iyya mai mulki majalisar dokoki ta ƙasa.

A ƴan kwanakin nan, jam'iyyar APC ta karɓi manyan ƴan siyasa daga jam'iyyun adawa daban-daban duk a shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.

Ƴan majalisa 3 sun bar PDP zuwa APC

A wani rahoton, kun ji cewa ƴan Majalisar Wakilan Tarayya uku daga jihar Katsina, sun jefar da jam'iyyar PDP, sun sanar da komawa APC mai mulki.

Ƴan majalisar sun tabbatar da hakan ne a zaman Majalisar Wakilai na ranar Laraba, 8 ga watan Mayu, 2025, wanda gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya halarta.

Matakin da ƴan majalisar suka ɗauka ya sanya adadin mambobin majalisar wakilai da suka sauya sheƙa ya kai 27 tun bayan da aka ƙaddamar da ita a watan Yunin 2023.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262