Turawa Sun Zo Kano, Sun Gana da Sanusi II maimakon Aminu Ado
- Tawagar kungiyar tarayyar Turai (EU) ta kai wa Khalifa Dr. Muhammadu Sanusi II ziyara ta musamman a fadar shi da ke jihar Kano
- Rahotanni sun nuna cewa tawagar ta hada da jakadan EU a Najeriya, Gautier Mignot da sauran jakadu daga Italy, Spain da sauransu
- Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi wa tawagar bayani game da tarihin masarautar Kano tare da yi masu hawa na musamman
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II ya karɓi baƙuncin wata babbar tawagar jakadu da jami’an diflomasiyya daga tarayyar Turai (EU) da wasu ƙasashen Turai.
Rahotannin da Legit Hausa ta tattaro sun nuna cewa sun gana ne a fadar masarautar Kano a jiya Litinin, 8 watan Yunin shekarar 2026.

Source: Facebook
Shafin da ke kula da fadar mai martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II a X ya wallafa bidiyon hawan daba da sarkin ya yi wa jakadun.
Turawa sun ziyarci Muhammadu Sanusi II
Tawagar da suka ziyarci Sanusi II ta haɗa da jakadan tarayyar Turai a Najeriya, Gautier Mignot, jakadan Denmark, Jens Ole Bach Hansen da jakadan Spain, Félix Costales.
Haka zalika ta hada da jakadan Italy, Roberto Mengoni, mataimakin shugaban ofishin jakadancin Faransa, Jean-François Hasperué, mataimakin shugaban ofishin jakadancin jamhuriyar Czech, Martin Čech.
Wakilin jakadan Finland, Maria Ruuskanen, wakiliyar ofishin jakadancin Belgium, Dorien Laermans, da mai ba da shawara kan harkokin siyasa na ofishin jakadancin Austria, Lukas Duenser na cikin tawagar.
Dalilin ziyarar turawa Kano
An bayyana cewa ziyarar ta kasance wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa fahimtar juna, haɗin gwiwa da musayar ra’ayoyi tsakanin cibiyoyin gargajiya da ƙasashen duniya.
Ziyarar na da nufin mayar da hankali kan kan batutuwan da suka shafi zaman lafiya, ci gaba mai ɗorewa, shugabanci da bunƙasa al’umma.

Kara karanta wannan
Mutuwa ta sake girgiza Najeriya, Sarkin Gazargamu ya riga mu gidan gaskiya a Masar

Source: Facebook
Bayanin Sarki Sanusi II ga Turawa
A yayin ganawar, mai martaba sarkin ya yi wa tawagar bayani kan tarihin masarautar Kano, rawar da cibiyoyin gargajiya ke takawa wajen samar da zaman lafiya, warware rikice-rikice, inganta ilimi da kiwon lafiya.
Bayan kammala zaman tattaunawar, Sanusi II ya shirya musu wata ƙaramar daba ta musamman, inda baƙin suka samu damar shaida kyawawan al’adun masarautar Kano.
A sakon da EU ta wallafa a Facebook, ta nuna jin daɗinta da irin tarba, karamci da kuma abubuwan tarihin da suka gani a masarautar.
Ta ce:
"Shugabannin EU sun ji daɗin ziyartar mai martaba, Sarkin Kano, wanda masarautarsa ta kasance mahaɗar kasuwanci, al’adu da shugabanci a yankin Sahel da Afirka ta Yamma."
Ga bidiyon hawan da Sarki Sanusi II ya yi wa Turawa:
Sulhun da aka yi wa Buhari da Sanusi II
A wani labarin, mun kawo muku cewa Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa ya sha yi wa manyan mutane sulhu a Najeriya a baya.

Kara karanta wannan
Matsalar tsaro: NLC da TUC sun yi barazanar hana ma'aikata zuwa wurin aiki a Najeriya
Malamin ya bayyana cewa a lokacin mulkin marigayi Muhammadu Buhari ya jagoranci sulhu tsakanin shugaban da Sarki Muhammadu Sanusi II.
Ya bayyana haka ne yayin da ya ke bayyana irin kokarin da ya ke wajen magance matsalolin da suka shafi al'umma ta bayan fage.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
