Gwamnonin Arewa 7 Sun Haɗa Kai, Sun Nemo Hanyar Rage Talauci a Yankin
- Gwamnonin yankin Arewa maso Yamma sun yi wata muhimmiyar ganawa a jihar Kano saboda matsalolin yankin
- Shugabannin yankin sun fara aiwatar da tsare-tsaren hadin gwiwa domin rage talauci wanda ya yi katutu a tsakanin al'ummar yankin
- Taron ya bayyana cewa talauci, rashin tsaro, matsalolin lafiya, sauyin yanayi da yara da ba su zuwa makaranta na bukatar mafita ta bai daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma sun nuna damuwa game da karuwar talauci a yankin.
Gwamnonin sun fara daukar matakan aiwatar da tsare-tsaren hadin gwiwa domin rage talauci da ya yi katutu.

Source: Facebook
Gwamnonin Arewa sun shirya yaki da talauci
Premium Times ta ce gwamnonin sun dauki hanyar fadada shirye-shiryen kariyar zamantakewa da samar da sababbin hanyoyin samar da kudade a jihohi bakwai na yankin.
An gudanar da wannan shiri ne a Kano yayin wani babban taron tattaunawa na kwanaki biyu kan rage talauci ta hanyar inganta tsarin kariyar zamantakewa.
Dandalin Gwamnonin Arewa maso Yamma ne ya shirya taron tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya da tallafin Tarayyar Turai da UNICEF.
Da take jawabi, babban daraktar sakatariyar Dandalin Gwamnonin Arewa maso Yamma, Maryam Yahaya, ta ce tattaunawar wani muhimmin mataki ne na mayar da alkawuran yanki zuwa aikace-aikacen da za su inganta rayuwar miliyoyin mutane.
A cewarta, wadannan matsaloli sun wuce iyakokin jihohi, don haka suna bukatar hadin gwiwa da tsare-tsaren bai daya domin magance su yadda ya kamata.
Maryam Yahaya ta ce:
"Arewa maso Yamma na da dimbin damar ci gaba, amma muna ci gaba da fuskantar manyan kalubalen ci gaba."
Wannan tattaunawa na daga cikin aiwatar da tsarin zaman lafiya, tsaro da ci gaban yankin ta hanyar karfafa kariyar zamantakewa da saka hannun jari wajen bunkasa jarin dan Adam.
Mataimakiyar wakiliyar UNICEF a Najeriya, Dakta Rownak Khan, ta bayyana taron a matsayin wani babban ci gaba wajen yaki da talauci da rashin walwala a yankin.

Kara karanta wannan
Lokaci ya yi: An shiga rudani kan yanayin da wani babban jami'in Kwastam ya rasu a Bauchi
Ta ce jihohin Arewa maso Yamma bakwai na da kusan mutane miliyan 60, kuma suna cikin yankunan da ke da mafi munin alkaluman walwalar yara a kasar nan, cewar Daily Post.

Source: Twitter
Martanin Gwamnan Kano game da yaki da talauci
Yayin bude taron a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf, mataimakin gwamnan Kano, Murtala Sule Garo, ya ce ya kamata a dauki kariyar zamantakewa a matsayin wata muhimmiyar hanyar saka jari wajen bunkasa jarin dan Adam.
Ya ce Kano ta riga ta kafa dokar manufofin kariyar zamantakewa tare da samar da darakta mai kula da daidaita shirye-shiryen tallafawa masu rauni da mabukata.
Garo ya bukaci mahalarta taron su tabbatar da cewa tattaunawar ta haifar da manufofi da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar al'ummar Arewa maso Yamma baki daya.
Gwamnonin Arewa sun damu kan matsalar tsaro
Mun ba ku labarin cewa gwamnonin da ke mulki a Arewa sun gudanar da muhimmin taro tare da sarakuna kan matsalolin da suka addabi yankin.
Bayan kammala taron, sun cimma matsaya kan hanyar da za a magance matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.
Hakazalika, sun yaba wa Mai girma Bola Tinubu kan kokarin da ya yi wajen ganin an kubutar da daliban da 'yan bindiga suka sace.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
