Jihar Kebbi
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Kebbi. 'Yan bindigan sun yi garkuwa da mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar.
Gwamnatin jihar Kebbi ta fito ta yi magana kan rahotannin da ke cewa akwai wani boyayyen filin jirgin sama a Argungu. Ta bayyana cewa karya ce tsagwaronta.
Dakarun sojoji sun tarba yan bindiga ta sama da kasa, sun sheke sama da 80 lokacin da suka yi yunkurin kutsawa cikin jihar Kebbi ta iyakarta da Zamfara.
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya sauya ma'aikatu ga wasu daga cikin kwamishinoninsa. Ya ce matakin na daga cikin manufarsa ta inganta ayyuka.
Peter Obi ya yi Allah wadai da cewa an kashe kudin da FIFA ta bayar wajen gina filin wasan jihar Kebbi a kan Naira biliyan 1.75. Ya ce rashawa ta yi yawa a Najeriya.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan miyagun 'yan bindiga a jihar Kebbi. Sojojin sun hallaka 'yan bindiga masu yawa bayan an gwabza fada.
Babban hafsan tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa, ya bayyana cewa nan da wani lokaci kadan za a kawo karshen ayyukan 'yan bindiga da 'yan Lakurawa.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya karyata zargin kisan Kiristoci a Najeriya. Ya bayyana cewa ko kadan babu kamshin gaskiya.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III zai jagoranci taron Majalisar Sarakunan Arewacin Najeriya yau Talata a birnin Kebbi, jihar Kebbi.
Jihar Kebbi
Samu kari