Kasar Iran Ta Harbo Jirgin Yakin Amurka, Trump Ya Sha Alwashin Ɗaukar Fansa

Kasar Iran Ta Harbo Jirgin Yakin Amurka, Trump Ya Sha Alwashin Ɗaukar Fansa

  • Shugaba Donald Trump ya zargi Iran da harbo jirgin yaki mai saukar ungulu na Amurka a mashigar Hormuz da ke Gabas ta Tsakiya
  • Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce an ceto matukan jirgin cikin koshin lafiya ta amfani da jirgin ruwa mara matuki
  • Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Iran da Isra'ila, sabon rikicin na iya sake tayar da tarzoma a yankin Gabas ta Tsakiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi magana game da yaki da ake ci gaba da yi a yankin Gabas ta Tsakiya.

Shugaba Trump ya zargi Iran da harbo jirgin yakin Amurka mai saukar ungulu a mashigar Hormuz.

Trump ya ce Iran ta kado jirgin Amurka
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian da Donald Trump na Amurka. Hoto: Anadolu Ajansi, Donald J Trump.
Source: Getty Images

'Iran ta harbo jirgin yakin Amurka' - Trump

A cewar wata sanarwa daga Ma'aikatar Tsaron Amurka, an samu nasarar ceto matukan jirgin Apache guda biyu bayan jirgin ya fadi sakamakon harin, cewar rahoton BBC.

Kara karanta wannan

Yadda miji da mata suka tafka damfarar kusan N2bn da matakin da EFCC ta dauka

Shugaban kasar na Amurka ya bayyana cewa dole ne kasarsa ta mayar da martani kan harin wanda ake tunanin zai yi zafi sosai saboda barnar da Iran ta yi mata.

Trump ya ce:

"Akwai matuka biyu a cikin jirgin kuma dukansu suna cikin koshin lafiya ba tare da rauni ba, duk da haka, Amurka dole ne, saboda larura, ta mayar da martani ga wannan hari."

Har yanzu ba a bayyana irin matakin da Amurka za ta dauka ba, amma duk wani matakin soja na iya kara dagula yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran.

Iran ba ta fitar da wata sanarwa kai tsaye kan kalaman Trump ba a lokacin da aka wallafa rahoton.

Wani jami'in Amurka ya bayyana cewa har yanzu ba a tabbatar ko jirgin marar matuki ya kai harin da gangan ba.

Kafofin yada labarai na Iran sun yi nuni da faruwar lamarin, inda kamfanin dillancin labarai na Mehr ya ce Iran ba ta dauki alhakin harin ba.

Iran ta yi nasarar kado wani jirgin Amurka
Sabon jagoran Musulunci a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Yadda aka ceto matukan jirgin Amurka

Rundunar CENTCOM ta ce an ceto matukan jirgin da karfe 7:33 agogon gabashin Amurka a daren Litinin 9 ga watan Yunin 2026, cewar Al Jazeera.

Kara karanta wannan

Bayan yi masa ihu a Amurka, Trump ya fadi lokacin yin nasara kan Iran

Ta bayyana cewa rundunar sojin ruwa ta Amurka tare da rundunar 82nd Airborne Division ne suka jagoranci aikin ceto.

An kuma samu goyon bayan rundunar sojin sama da ta ruwa, ciki har da Task Force 59 na rundunar Fifth Fleet.

Mai magana da yawun rundunar CENTCOM ya ce jirgin ruwa mara matuki na Task Force 59 da ke Bahrain ne ya dauko matukan.

Trump ya sake magana kan yakin Iran

Mun ba ku labarin cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya nuna alamun samun nasara a yakin da kasarsa ta kaddamar kan Iran a kwanakin baya.

Donald Trump ya nuna cewa Amurka na yin nasara a yakin, inda ya bayyana lokacin da za a samu cikakkiyar nasara kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Shugaban na Amurka ya bayyana cewa killace tashoshin jiragen ruwan Iran ya matsa mata lamba domin a kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakaninsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.