2027: Kwankwaso Ya Fadi Alakar Shi da Obi, Gawuna da Jam'iyyar NDC

2027: Kwankwaso Ya Fadi Alakar Shi da Obi, Gawuna da Jam'iyyar NDC

  • Tsohon gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a NDC, Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce shi da Peter Obi na da abubuwa da dama iri ɗaya
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da rade-radin cewa an fara samun baraka a jam'iyyar NDC da Kwankwaso ke ciki, ana cewa zai iya komawa wata tafiya
  • Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa babban burin su shi ne a samu a ci zabe domin kawo cigaba mai dorewa a Najeriya a bangarori da suka shafi 'yan kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Yayin da ake cigaba da tattauna batun zaben 2027, Rabiu Musa Kwankwaso ya fito ya yi magana kan makomar shi a jam'iyyar NDC.

Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa suna tare da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi sabanin abubuwan da ake fada marasa tushe.

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya ta yi magana game da ƙorafin Kwankwaso da barazanar zai bar NDC

Rabiu Kwanwaso da Peter Obi
Peter Obi na bayani a gefen Rabiu Kwankwaso a wajen taron NDC. Hoto: Mr Peter Obi
Source: Facebook

A wata hira da BBC Hausa ta yi da Rabiu Kwankwaso kuma ta wallafa a shafinta na X, ya tabbatar da cewa shi ne zai yi wa Obi mataimaki a takarar 2027.

Alakar Obi da Kwanwaso

Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa akwai abubuwan da shi da Peter Obi suke da shi iri daya a tsarin siyasar da suke kai.

Kwankwaso ya ce shi da Peter suna da matasa 'yan gani kashe ni da suke goyon bayan su domin sun tabbatar da nasarar su ita ce ta su.

Tsohon gwanan Kanon ya ce idan aka duba yadda 'yan Kwankwasiyya da 'yan Obidient za a tabbatar da irin yadda mabiyansu suke.

Ya ce

"Muna da abubuwa da ya wa iri daya... musamma idan ka duba Obidient da 'yan Kwankwasiyya. Hadin nan zai zama mana alheri."

Maganar takarar Obi/Kwankwaso

Kwankwaso ya bayyana cewa ya amince zai yi wa Peter Obi mataimaki, inda ya ce dan takarar shugaban kasar ya tabbatar da cewa ba zai mayar da shi dan kallo ba.

Kara karanta wannan

"Ku daina yi wa Fulani kudin goro," Peter Obi ya yi jan hankali kan ayyukan 'yan bindiga

A kan maganar cewa Obi zai yi wa'adi daya ne a kan mulki, Kwankwaso ya bayyana cewa a gaban jama'a dan takarar ya yi alkawari ba a cikin daki ba.

Ya kara da cewa yana kallon Peter Obi a matsayin dattijo kuma yana ganin zai cika wannan alkawarin da ya yi na mayar da mulki Arewa bayan ya yi wa'adi daya.

Jagororin NDC a Najeriya a wajen taro.
Rabiu Kwankwaso da wasu 'yan NDC a Abuja. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Maganar takarar Gawuna

Kwankwaso ya yi karin haske kan takarar Nasiru Gawuna da aka ba Sanata alhali wasu na tunanin za a ba shi takarar gwamna.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa samun takara rabo ne, kuma sanata ba karamin mukami ba ne a tsarin siyasar Najeriya.

Ya kara da cewa suna tare da Gawuna da Aminu Abdulsalam Gwarzo da aka ba takara cikin zaman lafiya da fahimtar juna har yanzu.

Ba bidiyon da Kwankwaso ya yi magana a cikinsa:

Ana neman rusa NDC

A wani labarin, kun ji cewa an kai jam'iyyar adawa ta NDC da Rabiu Musa Kwankwaso ke cikinta gaban kotu domin neman a rusa ta.

Mai shigar da kara, Ahidjo Karlahi ya yi zargin cewa jam'iyyar bata cika sharudan da kundin tsarin mulkin kasa ya gindaya ba.

A kan haka ya bukaci kotun ta hana jam'iyyar NDC shiga takarar dukkan zabukan da za a yi a zaben shekarar 2027 da ke tafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng