Borno: Boko Haram Ta Bude Wuta, Ta Kai Hare Hare 4 a kasa da Kwanaki 2
An shiga tashin hankali a Borno bayan ‘yan ta’adda na Boko Haram da na ISWAP sun kai hare-hare a sansanonin soji guda hudu a cikin jihar tsakanin ranar Litinin da Talata.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno – Wasu da ake zargin ‘yan ISWAP ne sun kai hari sansanin soji a Marte da tsakar dare, suka kashe sojoji bakwai tare da kwace motoci guda uku masu dauke da makamai.

Asali: Getty Images
Premium Times ta wallafa cewa a kasa da sa’o’i 24 bayan harin Marte, ‘yan ta’addan sun sake kai hari kan sansanonin soji uku a Dikwa, Rann da Gajiram.
Yadda ISWAP ta kai hari a Marte
Leadership ta ruwaito cewa wasu 'yan ISWAP sun fara kai hari sansanin sojoji da ke Karamar Hukumar Marte, da misalin 3.00 na safiyar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun ce ‘yan ta’addan sun kutsa garin Marte a kafa ta bangarori daban-daban, suka kewaye yankin gaba daya, suka tilasta sojojin komawa Dikwa dake makwabtaka da su.
Wani dan rundunar hadin gwiwa ya bayyana cewa, baya ga sojoji bakwai da aka tabbatar sun mutu, har yanzu ba a san inda wasu daga cikin sojojin suke ba.

Asali: Facebook
Sai dai majiyar ta musanta rahoton cewa ‘yan ta’addan sun kwace motocin yaki uku daga sansanin, tana mai cewa an kone motocin a sansanin sojojin.
A ranar Litinin din nan ce aka ga ‘yan ta’addan suna tafiya da babura da suka sace, makamai da kayan abinci zuwa garuruwan Chukungudu, Krenuwa da Klabariya da ke wajen Borno.
Sojoji sun gwabza da ISWAP a Dikwa
A Dikwa, hedikwatar Karamar Hukumar Dikwa, rahotanni sun nuna cewa an yi artabu sosai a tsakanin sojojin Najeriya da ‘yan ta’addan ISWAP.
Harin da suka kai a Dikwa ya auku ne kimanin sa’o’i 13 bayan wanda aka kai a Marte, kuma wata majiya daga Dikwa ta shaida cewa sojoji sun yi nasara a kan ‘yan ta’addan.
Ta bayyana cewa harin, wanda ya fara kimanin 1:00 na safiyar Talata, ya gamu da cikas bayan sojoji sun bude masu wuta.
Yadda ISWAP ta kai hari a Rann
Rahoton ya ci gaba da cewa an kai hari sansani na 3 na sojin Najeriya da ke Rann, hedikwatar Karamar Hukumar Kala Balge, kusan a lokaci guda da na Dikwa.
Majiyoyi sun ce harin ya fara ne kimanin 12:00 na dare ranar Talata, inda ‘yan ta’addan suka mamaye sansanin da manyan makamai, lamarin da ya jefa al’umma cikin tsoro.
Majiyar ta kara da cewa:
“Sojoji biyar aka tabbatar sun mutu, yayin da wasu shida suka jikkata. Bayan haka, ‘yan ta’addan sun kwace motocin yaki uku kafin suka fice daga sansanin.”
ISWAP ta kai hari sansanin Gajiram
A Gajiram, hedikwatar Karamar Hukumar Nganzai, majiyoyi sun bayyana cewa ‘yan ta’addan sun kai hari da daddare, amma sojoji sun fatattake su.
Rahoton ya ce:
“Boko Haram sun zo bayan tsakar dare. Sojoji sun fatattake su. Abinda suka iya yi kawai shi ne kona kujera guda a Gajiram, ba su yi wata barna ba."
An shawarci gwamnati kan harin ISWAP, Boko Haram
A ganawarsa da Legit, Kyaftin Abdullahi Bakoji rai ritaya ya shawarci gwamnati a kan korar mayakan yan ta'adda da ke fakewa a dajin Sambisa don rage mugun iri.
A cewarsa:
"Yadda ake kai farmaki a dajin Sambisa, a kashe ɗaruruwan mayakan Boko Haram, sauran su gudu, sannan sojoji su koma sansani – hakan zai ba su damar dawowa cikin dajin."
Ya nuna cewa mayakan Boko Haram sun ƙware wajen amfani da dabarun tsira daga hare-haren sojoji, ciki har da ɓoyewa a ƙasa ko cikin rami domin kauce wa hare-haren jiragen sama.
Bakoji ya ce:
"Mayakan Boko Haram na amfani da dabarun tsira na kansu domin kauce wa farmakin sojoji, ciki har da buɗe rami ko ɓoyewa a ƙasa don guje wa bama-bamai da ake jefa musu daga sama."
Ana zargin ISWAP da dasa bam a Borno
A baya, kun ji cewa ma’aikata biyu na hukumar ilimi ta karamar hukumar Damboa sun rasa rayukansu a ranar Litinin bayan da abin fashewa ya tashi da motar da suke ciki.
An gano mutanen da lamarin ya rutsa da su sune Blessings Luka da Gideon Bitterleaf, kuma an tabbatar da rasuwarsu nan take a wajen da bam din ya tashi a hanyar Damboa zuwa Maiduguri.
Rahotanni sun bayyana cewa mutanen biyun na zaune ne a gaba cikin wata motar Toyota Hiace dauke da mangwaro lokacin da motar ta taka bam da ake zargin 'yan ta’adda ne suka dasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng