Tsofaffin Shugabannin Majalisa da Suka Yi Murabus daga APC kan Zaben Fitar da Gwani
FCT, Abuja - Jam'iyyar APC ta gudanar da zaben fitar da gwani domin zabar 'yan takara a kujeru daban-daban a sassan Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Zaben fitar da gwanin da APC ta gudanar ya bata ran wasu mambobi, inda suke ganin cewa ba a yi masu adalci ba.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro wasu tsofaffin shugabannin Majalisar dokokin jihohi da suka yi murabus daga APC bayan gudanar da zaben fitar da gwani.
Zaben fitar da gwanin APC ya jawo tarnaki
Zaben fitar da gwanin na APC dai ya bar baya da kura a wasu jihohi, inda wasu ba su yi nasara ba suka nuna rashin gamsuwarsu da tsarin.
Wasu mambobi masu faɗa a ji, ciki har da 'yan majalisun tarayya da na jihohi, sun fara yin murabus daga jam'iyyar tare da sauya sheka zuwa wata jam'iyyar domin tabbatar da burinsu a zaɓubbuka masu zuwa.
Tsofaffin shugabannin majalisa da suka bar APC
Haka zalika, aƙalla tsoffin shugabannin Majalisun dokoki na jihohi daban-daban guda uku ne suka yi murabus daga APC sakamakon zaɓubbukan fitar da gwani na jam'iyyar mai mulki.
Sun koma jam'iyyun hamayya ne domin tabbatar da burinsu na shekarar 2027 duba da cewa ba su samu damar yin hakan ba a cikin APC.
Ga jerinsu nan kasa:
1. Idris Garba Kareka (jihar Jigawa)
Tsohon shugaban majalisar dokoki ta jihar Jigawa kuma mamban da ke wakiltar mazaɓar Jahun, Rt. Hon. Idris Garba Kareka, ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP.
Kareka ya sanar da sauya shekarsa ne a wurin wani gagarumin taron siyasa da aka gudanar a garin Jahun, jaridar Tribune ta kawo labarin.

Source: Facebook
Bayan barin APC ya shiga jam'iyyar hamayya ta PDP a hukumance kuma ya bayyana aniyarsa ta neman sake zaɓe domin ci gaba da wakiltar mazaɓar a majalisar dokokin jihar.
Yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a wurin taron, tsohon shugaban majalisar wanda ya yi wa'adi biyu ya ce matakin da ya ɗauka na barin APC ya biyo bayan buƙatar kare muradin al'ummar mazaɓarsa da kuma haɓaka ci gaban karamar hukumar Jahun.
2. Victor Ochei (jihar Delta)
Tsohon shugaban majalisar dokoki ta jihar Delta, Victor Ochei, ya yi murabus daga jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Rt. Hon. Ochei ya sanar da murabus ɗinsa ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Alhamis, 28 ga watan Mayun 2026.

Source: Facebook
A cikin sanarwar tasa, Mista Ochei ya ce ya ɗauki wannan matakin ne bayan zurfafa tunani da yin shawarwari sosai.
Tsohon shugaban majalisar ya ce ya shiga APC ne a shekarar 2016 tare da “tsantsar kyakkyawar niyya” kuma ya shafe shekaru yana aiki domin ƙarfafa jam'iyyar a faɗin jihar Delta.
Bayan barin APC, tsohon shugaban majalisar dokokin ta jihar Delta ya sauya sheka zuwa sabuwar jam'iyyar NDC
3. Hyacinth Dajoh (Jihar Benue)
Tsohon shugaban majalisar dokoki ta jihar Benue, Hyacinth Dajoh, ya bar jam'iyyarsa ta APC domin komawa PDP mai adawa.
Hyacinth Dajoh Ya fice daga jam'iyyar ne bayan ya janye daga zaɓen fitar da gwani na APC na mazabar Gboko ta Yamma, inda ya bayyana zargin tafka kura-kurai da rashin gaskiya a cikin tsarin, rahoton jaridar The Sun ya nuna hakan.

Kara karanta wannan
Atiku ya zayyano kurakuran gwamnatin Tinubu kan rashin tsaro "ta ki daukar darasi"

Source: Facebook
Dajoh ya yi zargin cewa a wasu wuraren, an riga an cike takardun sakamako tun kafin a kaɗa ƙuri'a, yayin da aka nuna cewa kayayyakin zaɓe ba su isa wasu rumfunan zaɓe da dama ba duk da cewa an sanar da waɗanda suka yi nasara.
A cikin wata sanarwa da hadiminsa kan harkokin yaɗa labarai, Agber Kulugh, ya sanya wa hannu, an bayyana cewa Dajoh ya sauya sheka zuwa PDP ne a hukumance a Makurdi ranar Laraba, 20 ga Mayu, 2026.
Gwamnoni za su yi takarar sanata a APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu gwamnonin da ke kan kujera sun samu tikiitin takarar sanata na APC a zaben 2027.
Gwamnoni bakwai da ke kan kujera ne suka samu tikitin takarar sanata na jam'iyyar APC a babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara.
Daga cikinsu akwai gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, wanda ya samu tikitin APC don takarar kujerar sanata ta Nasarawa ta Arewa.
Asali: Legit.ng

