Sanatoci 3 Sun Sake Rikita Majalisar Dattawa, Sun Sauya Sheƙa daga PDP zuwa APC

Sanatoci 3 Sun Sake Rikita Majalisar Dattawa, Sun Sauya Sheƙa daga PDP zuwa APC

  • Jam'iyyar APC ta samu ƙaru a Majalisar Dattawan Najeriya da sanatoci uku daga jihar Kebbi suka sanar da ficewarsu daga PDP a hukumance
  • Adamu Aliero (Kebbi ta Tsakiya), Yahaya Abdullahi (Kebbi ta Arewa), da Garba Maidoki (Kebbi ta Kudu) sun koma APC yau Talata a Abuja
  • Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan Kebbi, Dr. Nasir Idiris da wasu jiga-jigan gwamnatin tarayya sun halarci zaman majalisar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kebbi - Sanatoci uku daga jihar Kebbi da ke Arewa maso Yammacin Najeriya sun sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Sanatacin sun tabbatar da komawa APC a hukumance ne a wasikun da suka miƙa wa Majalisar Dattawa ranar Talata, 12 ga watan Mayu, 2025.

Sanatocin Kebbi.
APC ta samu karuwa a Majalisar Dattawan Najeriya Hoto: Nigerian Senate
Asali: Twitter

Sanatocin PDP 3 sun koma APC a Majalisa

Majalisar Dattawa ta tabbatar da sauya shekar sanatocin a zamanta na yau Talata, kamar yadda gidan talabijin na kasa watau NTA ya wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatocin da suka koma APC sun haɗa da Adamu Aliero (Kebbi ta Tsakiya), Yahaya Abubakar Abdullahi (Kebbi ta Arewa), da Garba Maidoki (Kebbi ta Kudu).

Wannan dai na zuwa ne bayan sanatocin sun sanar da ficewa daga jam'iyyar PDP a hukumance, lamarin da ya ƙara rage ƙarfin adawa a Majalisar Dattawa.

Taƙaitaccen bayani kan sanatocin Kebbi 3

Sanata Adamu Alieru, ya rike kujerar gwamnan jhar Kebbi na tsawon zango biyu watau shekara takwas daga 1999 zuwa 2007. Daga nan ya wuce Majalisar Dattawa daga 2007 zuwa 2008.

Tsohon shugaban ƙasa, Marigayi Alhaji Umaru Musa Ƴar'adua ya naɗa Adamu Aliero a matsayin ministan harkokin Abuja, muƙamin da ya rike daga 2008 zuwa 2010.

Haka nan kuma Sanatan Kebbi ta Arewa, Yahaya Abubakar Abdullahi ya riƙe kujerar shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa ta tara daga 2019 zuwa 2023.

Sai kuma Garba Maidoki wanda wannan ne karo na farko da ya shiga Majalisar Dattawa bayan ya doke sanata mai ci, Bala Ibn Na’Allah a zaɓen 2023.

Manyan jiga-jigan APC da suka hada da shugaban jam’iyyar na Ƙasa, Abdullahi Ganduje, Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, da Ƙaramin Ministan Harkokin Jin ƙai, Yusuf Sununu sun halarci zaman Majalisar.

Majalisar Dattawa.
Sanatocin APC sun zama 68 a Majalisar Dattawa ta 10 Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Sanatocin APC sun zama 68 a Majalisa

Da wannan ci gaba, adadin sanatocin APC a majalisar dattawa ta 10 ya karu zuwa 68, wanda ya ƙara ba jam'iyya mai mulki ƙarfi, kamar yadda Channels tv ta kawo.

Ga sabon tsarin kujerun kowace jam'iyya a majalisar dattawa:

APC – 68

PDP – 30

LP – 5

NNPP – 1

SDP – 2

APGA – 1.

Shirin zaben 2027

Yayin da ake ci gaba da samun sauyin yanayin siyasa a Najeriya, masana da 'yan kasa na hasashen zaben 2027 zai kasance tsakanin jam’iyyun APC da PDP kamar yadda aka saba.

A halin yanzu, APC na da karfi sosai a Majalisar Dattawa, musamman bayan samun sanatoci da dama da suka shiga jam'iyyar kwanan nan. Wannan na kara musu rinjaye a majalisar da kuma inganta hasashen nasu a 2027.

Sai dai PDP har yanzu tana da tushenta a wasu jihohi, musamman a kudancin kasar da kuma sassan Arewa ta Tsakiya.

Wasu na ganin cewa jam’iyyar na iya dawowa da karfi idan ta daidaita rikice-rikicenta na cikin gida da kuma fitar da dan takara da zai hada kan jama’a.

A daya bangaren, ana ta tattaunawa a fadin kasa cewa PDP tana fuskantar kalubale na sauya sheka daga jiga-jiganta, wanda ke iya rage mata karfi.

Duk da haka, akwai masu ganin cewa matsin lamba daga gwamnati na iya jefa APC cikin matsaloli nan gaba, wanda PDP za ta iya amfana da su idan ta gyara kurakuranta.

Zaben 2027 zai zama gwaji mai tsanani ga jam’iyyun biyu, kuma yana iya bayyana sabon salo a siyasar Najeriya.

Rikici ya kunno kai a APC ta jihar Kebbi

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC reshen jihar Kebbi ta dakatar da tsohon dan Majalisar Wakilai, Hon. Muhammad Shehu Koko da shugabanni 9.

Ana ganin wannan lamari alamu ne na ɓarakar da ke neman kunno kai a APC reshen jihar Kebbi a lokacin da jam'iyyar ke shirin karɓar sanatoci uku daga PDP.

A takardar dakatarwar, APC ta ce ta ɗauki wannan matakin ne saboda zarginsu da cin amana, rashin ladabi da ƙoƙarin cin mutuncin shugabannin jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262