Fadar Shugaban Kasa Ta Tsorata, Ta Ce Peter Obi Zai Iya ba Atiku Mamaki a Zaben 2027

Fadar Shugaban Kasa Ta Tsorata, Ta Ce Peter Obi Zai Iya ba Atiku Mamaki a Zaben 2027

  • Fadar shugaban kasa ta ce 'dan takarar NDC, Peter Obi na iya samun kuri'u fiye da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a 2027
  • Hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala ya ce Obi na kara samun karfi a siyasa, wanda zai iya ba mutane mamaki a babban zabe na gaba
  • Bwala ya kuma yi ikirarin cewa Atiku Abubakar bai taba samun gagarumin rinjaye na kuri'u daga yankin Arewa maso Yamma ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Daniel Bwala, ya yi hasashen wanda zai fi taka rawa a zaben 2027 tsakanin Atiku Abubakar da Peter Obi.

Bwala ya bayyana cewa 'dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, na iya samun kuri'u fiye da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a zaben 2027.

Kara karanta wannan

'Zaben Peter Obi da Kwankwaso kamar ba Tinubu damar nasara ne a 2027'

Bwala da Peter Obi.
Hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala da dan takarar NDC a zaben 2027, Peter Obi Hoto: @bwaladaniel, Mr. Peter Obi
Source: Twitter

Bwala ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da tashar Symfoni TV a ranar Juma'a, inda ya yi nazari kan yanayin siyasar Najeriya gabanin babban zaben kasar na gaba.

Bwala ya damu da karuwar tasirin Obi

Mai taimaka wa shugaban kasar ya ce yana ganin tasirin siyasar Peter Obi na kara karfi, lamarin da ka iya sa ya zarce Atiku wajen samun kuri'u idan aka ci gaba da tafiya a haka.

Bwala, wanda ya kasance 'daya daga cikin masu magana da yawun kwamitin kamfen Atiku a 2023, ya kuma yi magana kan sauye-sauyen da ake samu a tsagin adawa da kalubalen da manyan 'yan takara ke fuskanta kafin zaben 2027.

A cewarsa:

"Ina fargabar Peter Obi zai iya samun kuri'u fiye da Atiku Abubakar a zaben 2027. Sai dai kuma ina ganin zai iya karewa a matsayi na hudu."

Bwala ya fadi abin da ya taimaki Obi

Kara karanta wannan

Atiku ya zayyano kurakuran gwamnatin Tinubu kan rashin tsaro "ta ki daukar darasi"

Bwala ya ce a zaben 2023, Peter Obi ya samu goyon bayan wasu gwamnoni, sanatoci da 'yan majalisar wakilai daga jam'iyyar PDP amma a halin yanzu babu wani gwamna da ke mara masa baya.

A cewarsa:

"A zaben 2023, PDP tana da gwamnoni da sanatoci da 'yan majalisar tarayya da suka mara masa baya, amma a yanzu babu ko gwamna guda daya da ke goyon bayansa."
Atiku Abubakar.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar a taron ADC a Abuja Hoto: @Atiku
Source: Facebook

Bwala ya kuma yi ikirarin cewa Atiku Abubakar bai taba samun gagarumin rinjaye na kuri'u daga yankin Arewa maso Yamma ba a tarihinsa na siyasa, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.

Kalaman Bwala na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan yiwuwar kulla kawance tsakanin jam'iyyun adawa da kuma shirye-shiryen da manyan 'yan siyasa ke yi domin zaben shugaban kasa na 2027.

Okonkwo ya soki takarar Peter Obi

A wani rahoton, kun ji cewa jigon ADC mai adawa a Najeriya ya bayyana damuwa game da zaben dan takarar NDC, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a 2027.

Keneth Okonkwo ya bayyana cewa goyon bayan Peter Obi a zaben shugaban kasa na 2027 na iya karawa Shugaba Bola Tinubu damar samun wa’adi na biyu.

Tsohon kakakin LP ya bukaci jam’iyyun adawa su hade kan dan takara guda domin kauce wa rarrabuwar kuri’u a zaben 2027

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262