Lokuta 4 da Donald Trump Ya Caccaki Netanyahu kan Yake Yake

Lokuta 4 da Donald Trump Ya Caccaki Netanyahu kan Yake Yake

Shugaban Amurka, Donald Trump da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu sun samu sabani a lokuta mabanbanta saboda yake-yake a duniya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya shafe shekaru yana jagorantar kai hare-hare a kasashe da wasu 'yankunan Gabas ta Tsakiya.

Hare-haren da ya ke kai wa sun jawo ya samu sabani da babban mai goya masa baya a duniya, wato shugaban Amurka, Donald Trump.

Donald Trump da Netanyahu
Donald Trump tare da Benjamin Netanyahu a White House. Hoto: Getty Images
Source: UGC

A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku lokutan da Donald Trump da Benjamin Netanyahu suka kai ruwa rana saboda yake-yake.

1. Trump ya matsawa Netantayu lamba

A ranar 10 ga Janairu, 2025, Trump ya fara shiga tsakani na farko a rikicin Gaza ta hannun wakilinsa na musamman a Gabas ta Tsakiya, Steve Witkoff.

Kara karanta wannan

Trump ya dakatar da sojojin Amurka daga kai hari a Iran bayan samun gargadi

Trump ya matsa wa Netanyahu ya amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, wacce tawagar Joe Biden ta shafe watanni tana tsarawa.

Netanyahu ya nuna adawa da farko, amma daga ƙarshe ya amince ba don ya gamsu ba, sai saboda dole kamar yadda New York Times ta rahoto Trump ya ce:

“Babu wani zaɓi dabam, dole ne ka amince.”
Hare-haren da aka kai Gaza
Yadda Isra'ila ta ruguza wani gini a Gaza. Hoto: Getty Images
Source: AFP

Yarjejeniyar ta fara aiki, kuma an fara sakin mutanen da aka yi garkuwa da su amma cikin makonni shida kacal, a watan Maris na 2025, Netanyahu ya karya yarjejeniyar ta hanyar ba da umarnin komawa Gaza tare da sake fara kai hare-hare.

2. Netanyahu ya sha zagi kan Gaza

Bayan watanni ana kai hare-hare kan fararen hula a Gaza, Trump ya shiga tsakani ya samar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta biyu a Oktoban 2025 amma cimma hakan ya buƙaci wata sabuwar takaddama.

Lokacin da Hamas ta bayar da abin da Trump ya ɗauka a matsayin wata dama ta cimma yarjejeniya, ya kira Netanyahu a ranar 4 ga Oktoban 2025, sai aka gaya masa cewa martanin Hamas ba shi da wata ma’ana.

Kara karanta wannan

Yakin Iran: Amurka ta jefa makamai, an hallaka jami'an kasar Indiya

Mujallar Time ta wallafa cewa Trump ya mayar masa da martani da cewa:

“Ban fahimci dalilin da ya sa kullum kake ganin mummunan sakamako ba. Wannan nasara ce. Ka karɓe ta.”
“Bibi, ba za ka iya yaƙar duniya baki ɗaya ba,”
Benjamin Netanyahu a Isra'ila
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Bayan matsin lamba, Netanyahu ya amince, aka sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta biyu. Amma zuwa ƙarshen shekarar 2025, Isra’ila ba ta matsa zuwa mataki na biyu ba, wato janye sojojinta gaba ɗaya daga Gaza kamar yadda yarjejeniyar ta tanada.

3. Trump ya tilasta Netanyahu

Yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a Gaza kullum, Netanyahu ya buɗe wani sabon fagen yaƙi ko kuma ya ƙara tsananta wanda ya riga ya fara a Lebanon, inda hare-haren Isra’ila suka kashe sama da mutum 300 a rana guda.

Trump ya kira shi a ranar 9 ga Afrilun 2026 a wata tattaunawar da Anadolu Agency ta bayyana a matsayin mai cike da tashin hankali.

Trump ya matsa wa Netanyahu da ya rage kai hare-hare kan Hezbollah saboda Amurka na iya ayyana tsagaita wuta a yankin ba tare da shi ba.

Kara karanta wannan

"Za su dandana kudarsu"; Trump ya yi sabuwar barazana ga Iran bayan musayar hare hare

Wajen da Isra'ila ta kai hari Lebanon
Hayaki na tashi a wani waje da Benjamin Netanyahu ya kai hari Lebanon. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Da yake fuskantar wannan barazana, Netanyahu ya amince da fara tattaunawa. Amma kwanaki kaɗan bayan haka, Isra’ila ta ƙara faɗaɗa hare-haren sojojinta na ƙasa a kudancin Lebanon.

4. Trump ya zargi Netanyahu da hauka

A ranar 1 ga Yuni, 2026, shugaba Donald Trump ya jiye duk wani ladabi na diflomasiyya tsakanin shi da Benjamin Netanyahu ya yi zage-zage.

Yayin da Isra’ila ke barazanar kai hari Beirut, matakin da ya sa Iran ta yi barazanar ficewa gaba ɗaya daga tattaunawar nukiliya, Trump ya kira Netanyahu a waya.

Legit ta rahoto Trump ya ce masa:

“Ka yi hauka ne. Da tuni kana kurkuku da ba don ni ba. Ni ne nake ceton ka. Kowa ya tsane ka yanzu. Kowa ya tsani Isra’ila saboda wannan.”
Yadda Isra'ila ta kai hari Lebanon
Harin Isra'ila ya rusa wani gini a Lebanon. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya tunatar da Netanyahu irin goyon bayan da ya ba shi yayin shari’ar cin hanci da rashawa, sannan ya gargade shi cewa kai hari Beirut zai ƙara ware Isra’ila a duniya.

Kara karanta wannan

Bayan yi masa ihu a Amurka, Trump ya fadi lokacin yin nasara kan Iran

Rasha, China sun gargadi Trump

A wani rahoton, kun ji cewa kasashen China da Rasha sun yi magana yayin da sabon rikici ya sake barkewa tsakanin Iran da Amurka.

China ta bukaci Donald Trump na Amurka da shugabannin Iran su kai zuciya nesa, su dakatar da kai hare-hare domin samun damar komawa sulhu.

Rasha ta bukaci Trump da Iran su dakatar da yakin tare da tayin ba ta damar samar da hanyar da za su bi wajen cimma yarjejeniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng