AbdulAziz Yari Ya Fadi Abin da Ya Karawa APC Tasiri a Arewacin Najeriya

AbdulAziz Yari Ya Fadi Abin da Ya Karawa APC Tasiri a Arewacin Najeriya

  • Sanata AbdulAziz Abubakar Yari ya nuna jin daɗinsa kan sauya sheƙar da sanatocin PDP guda uku suka yi zuwa jam'iyyar APC
  • Tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya bayyana cewa sauya sheƙar ta su alama ce da ke nuna ƙarfin da APC take da shi a Arewacin Najeriya
  • 'Dan majalisar ya kuma musanta zargin da ake yi na cewa ana ƙoƙarin maida Najeriya ƙarƙashin jam'iyya ɗaya a mulkin Bola Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Sanata AbdulAziz Yari, mai wakiltar Zamfara ta Yamma, ya yi magana kan sauya sheƙar sanatoci uku na PDP zuwa APC a jihar Kebbi.

Sanata AbdulAziz Yari ya ce sauya sheƙar su zuwa APC, alama ce ƙarara da ke nuna yadda jam’iyyar ke ƙara ƙarfi a Arewacin Najeriya.

Abdul'aziz Yari
Abdulaziz Yari ya yi farin ciki da komawar sanatocin PDP zuwa APC Hoto: Abdul'aziz Yari
Asali: Facebook

AbdulAziz Yari, wanda tsohon gwamnan jihar Zamfara ne, ya bayyana hakan ne ga manema labarai a ranar Talata, bayan zaman majalisar dattawa, cewar rahoton jaridar The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Talata, Sanata Adamu Aliero (Kebbi ta Tsakiya), Sanata Yahaya Abdullahi (Kebbi ta Arewa), da Sanata Garba Maidoki (Kebbi ta Kudu) sun sauya sheƙa daga PDP zuwa jam’iyyar APC.

Yari kan komawar sanatocin PDP zuwa APC

"Waɗannan mutane muhimmai ne, waɗanda tun da farko suna cikin APC tsawon shekara biyar zuwa shida."
“Amma kamar yadda kuka sani, siyasa cike take da faɗi tashi da ƙalubale. Ba su samu tikitin tsayawa takara a jam’iyyarmu ba a shekarar 2023, amma a zuciyarsu, sun kasance ƴaƴan jam’iyyar APC tun farko."
“Saboda haka sai suka tsaya takara a ƙarƙashin PDP, amma yanzu sun yanke shawarar komawa gida.”
“Wannan babban nasara ce ga jam’iyyarmu a jihar Kebbi, jam’iyyarmu a yankin Arewa maso Yamma, da jam’iyyarmu a Arewacin Najeriya."

Sanata AbdulAziz Yari

Sanata AbdulAziz Yari ya ce halartar gwamnan jihar Kebbi majalisar domin sauya sheƙar, wani mataki ne na nuna goyon baya da haɗin kai.

Yari ya musanta batun yin jam'iyya ɗaya

Da aka tambaye shi ko yawan sauya sheka daga jam’iyyun adawa zuwa APC na nufin Najeriya na shirin zama ƙasa da ke karkashin jam’iyya ɗaya, Abdul'aziz Yari ya ƙaryata hakan.

Abdul'aziz Yari
Abdul'aziz Yari ya ce ba a yunkurin maida Najeriya karkashin jam'iyya 1 Hoto: Abdul'aziz Yari
Asali: UGC
“To, hakan dai mutane ne ke faɗa, amma ni ban yadda da hakan ba domin Najeriya babbar dimokuradiyya ce, kuma muna da jam’iyyu kusan 56."
“Saboda haka ba yadda za a ce kowa zai shigo APC. Muna da jam’iyyu 56 da aka yi wa rajista, to tabbas mutane za su tsaya takara. Za a samu gasa tsakanin jam’iyyun.”
“Wataƙila wasu jam’iyyun za su kasance masu rauni, kuma APC za ta ci gaba da kasancewa yadda take. Amma ba burinmu bane mu zama jam’iyya ɗaya tilo. Muna maraba da kowa."
“Abin da muke hanƙoro shi ne a tabbatar da ingantacciyar gwamnati da samun nasara a zaɓukanmu na shekarar 2027. Muna addu’a kuma muna aiki tuƙuru don ganin mun samu nasara.”

- Sanata AbdulAziz Yari

An kare Tinubu kan komawar ƴan adawa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele, ya kare Shugaba Bola Tinubu kan komawar ƴan adawa zuwa APC.

Sanata Bamidele ya bayyana cewa ko kaɗan shugaban ƙasan bai tilastawa ƴan adawa shigowa cikin APC mai mulki a Najeriya.

Hakazalika shugaban masu rinjayen na majalisar dattawa ya bayyana cewa ƙofa a buɗe take ga ɗuk masu son sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng