PDP Ta Samu Koma Baya, Sanata Ya Sauya Sheka zuwa jam'iyyar APC

PDP Ta Samu Koma Baya, Sanata Ya Sauya Sheka zuwa jam'iyyar APC

  • Sanata Ned Nwoko mai wakiltar mazaɓar Delta ta Arewa a majalisar dattawa, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya
  • Ned Nwoko ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC bayan ya fice daga PDP, inda ya nuna goyon bayansa ga manufofin gwamnatin Bola Tinubu
  • Sauya sheƙar da sanatan ya yi zuwa APC, ya sanya yanzu dukkanin sanatoci uku da ke wakiltar jihar Delta a majalisa, ƴa ƴan jam'iyyar ne

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Delta - Sanatan da ke wakiltar mazaɓar Delta ta Arewa a majalisar dattawa, Sanata Ned Nwoko, ya fice daga jam'iyyar PDP.

Sanata Ned Nwoko bayan ficewarsa daga PDP ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai adawa a jihar Delta.

Sanata Ned Nwoko ya koma APC
Sanata Ned Nwoko ya fice daga PDP zuwa APC Hoto: Senator Prince Ned Nwoko
Asali: UGC

Sanata Ned Nwoko ya koma jam'iyyar APC

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Sanatan ya sanar da ficewarsa daga PDP ne a garinsu na Idumuje Ugboko, da ke ƙaramar hukumar Aniocha ta Arewa, a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Ned Nwoko ya bayyana goyon bayansa ga manufofin gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

"Na yi amanna da manufofin hangen nesa na gwamnatin tarayya ƙarƙashin shugabancin Shugaba Tinubu. Hakan ya yi daidai da burin ƴan Najeriya."

- Sanata Ned Nwoko

Meyasa sanatan ya fice daga PDP?

Daraktar watsa labarai ta sanatan, Honorabul Gloria Okolugbo, ta tabbatar da sauya sheƙar Ned Nwoko a cikin wata gajeriyar sanarwa.

Gloria Okolugbo ta ce Nwoko ya yanke shawarar sauya sheƙa zuwa APC, bayan ya gaji da gazawar PDP wajen tallafa masa kan burinsa na kawo ci gaba ga al’ummar Anioma.

Ta bayyana cewa Nwoko ya gudanar da jerin tarurruka da masu ruwa da tsaki, magoya baya, da mazauna yankin Delta ta Arewa kafin ya yanke wannan hukunci.

Jam'iyyar APC ta samu ƙaruwa a Delta

Matakin Sanata Ned Nwoko na sauya sheƙa zuwa APC ana sa ran zai sauya tsarin siyasar jihar Delta gabanin zaɓen 2027.

Sauya sheƙarsa na nufin cewa dukkanin sanatoci uku da ke wakiltar jihar Delta a majalisar dattawa, Ned Nwoko, Ede Dafinone, da Joel Onowakpo Thomas, ƴan jam'iyyar APC ne.

Wannan cigaban ya haifar da jita-jitar cewa gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, na duba yiwuwar sauya sheƙa, duk da cewa ba a fitar da wata sanarwa a hukumance ba.

Masu nazarin siyasa sun yi amanna cewa sauya sheƙar Ned Nwoko babban tagomashi ne ga jam’iyyar APC a jihar Delta, wanda hakan zai zai iya haifar da giɓi a PDP.

Sanata ya musanta ficewa daga APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanatan da ke wakiltar mazaɓar Kwara ta Tsakiya a majalisar dattawa, Saliu Mustapha, ya taɓo batun jita-jitar da ake yi kan shirinsa na barin APC.

Sanata Saliu Mustapha ya musanta jita-jitar wacce ya bayyana a matsayin mara tushe ballantana makama, ya nuna cewa yana nan daram a jam'iyyar APC.

Ya buƙaci jama'a da su yi watsi da ƙarairayin da ake yaɗawa a kansa cewa ya raba gari da APC mai mulki a jihar Kwara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng