‘Tinubu Ya Dawo da Zaman Lafiya a Wasu Yankuna’: Matawalle Ya Hango Nasara a 2027
- Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya bayyana kwarin gwiwa cewa Shugaba Bola Tinubu zai samu karin kuri’un Arewa a 2027
- Ya ce ’yan adawa na yada furofaganda da labaran karya kan tsaro, suna yin watsi da ci gaban gwamnati wajen yaki da matsaloli masu
- Matawalle ya yaba wa sojoji da sauran jami’an tsaro kan kokarinsu,yana cewa dabarun Tinubu sun rage ayyukan ‘yan bindiga suna kawo zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya bayyana kwarin guiwa game da zaben shekarar 2027 wanda ake tunkara.
Matawale ya nuna tabbacin cewa Shugaba Bola Tinubu zai samu ƙarin goyon bayan Arewa a zaɓen 2027 saboda ingantattun tsare-tsare tsaro.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harokin yada labarai, Ahmad Dan-Wudil, ya bayyana wanda The Nation ta samu.
Matawalle ya zargi yan adawa kan rashin tsaro
Ministan ya jaddada cewa babu wata furofaganda, yaɗa ƙarya ko suka daga ‘yan adawa da za su iya karkatar da hankalin Shugaban ƙasa daga aiwatar da aikinsa yadda ya kamata.
Ya zargi wasu ‘yan adawa, musamman daga Arewa maso Yamma, da yaɗa labaran ƙarya tare da ƙara girman matsalolin tsaro domin rage darajar nasarorin gwamnatin Tinubu.
A cewarsa, masu sukar gwamnati sun yi watsi da ci gaban da aka samu a yaki da rashin tsaro, suna mai da hankali kan wasu ƙananan abubuwa domin haifar da tsoro da tashin hankali a siyasa.
Matawalle ya ce ‘yan adawa ba su jin daɗin abin da ya kira gagarumar nasara a yaki da ‘yan bindiga da kuma ci gaban ayyukan raya ƙasa a sassa daban-daban na Najeriya.

Source: Facebook
'Tsare-tsaren da Tinubu ya kawo a tsaro'
Matawale ya ce gwamnatin Tinubu ta ɗauki sabuwar hanya ta amfani da bayanan sirri da hadin kai wajen yaki da rashin tsaro, musamman a jihohin Sokoto, Zamfara, Katsina, Kaduna da Kebbi.
A cewarsa, wannan dabarar ta taimaka wajen kawar da manyan shugabannin ‘yan bindiga tare da rusa maboyarsu a sassa daban-daban na yankin.
Ya ƙara da cewa ayyukan soji sun dawo da zaman lafiya a wasu yankuna, wanda ya ba mutane damar komawa gonaki da sauran harkokin rayuwa.
Ministan ya bayyana ayyukan gwamnati a Arewa ciki har da gyaran hanyoyi, tallafin noma, tsaro da samar da damammaki ga matasa da mata, cewar Daily Post.
Ya nuna kwarin gwiwa kan zaɓen 2027, yana mai cewa nasarorin gwamnati za su sa ‘yan Najeriya su sake goyon bayan Shugaba Tinubu a rumfunan zaɓe.
Sarki, Matawalle sun jagoranci addu'o'i ga Tinubu
Kun ji cewa karamin ministan Tsaro, Bello Matawalle ya yaba wa salon mulkin shugaban kasa, Bola Tinubu a cikin shekaru uku.
Matawalle ya bayyana cewa nasarorin Shugaba Tinubu cikin karin wa’adi na shekaru hudu za su kai Najeriya matsayi mafi girma.
A wajen taron addu’a da aka gudanar a fadar Sarkin Maradun, dubban mutane sun yi addu’o’i domin nasarar Tinubu.
Asali: Legit.ng

