"So Suke a Yafe Masu Zunubai," Jigon PDP Ya Tona Asirin Wasu Gwamnoni da Jiga Jigai

"So Suke a Yafe Masu Zunubai," Jigon PDP Ya Tona Asirin Wasu Gwamnoni da Jiga Jigai

  • Tsohon kakakin PDP na kasa ya ce ƴan siyasa na tururuwar shiga APC saboda suna son gwamnati mai ci ta yafe masu zunubban da suka yi
  • Kola Ologbondiyan ya tunatar da ƴan Najeriya yadda tsohon shugaban APC na ƙasa ya yi alƙawarin yafe wa duk wanda ya shiga jam'iyyar
  • Mai magana da yawun APC, Felix Morka ya maida masa martani, yana cewa PDP ta gaza warware matsalolinta bare ta karɓi mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Tsohon kakakin jam’iyyar PDP na ƙasa, Kola Ologbondiyan, ya danganta yawaitar sauya sheƙar jagororin adawa zuwa APC da tsoron farautar siyasa daga gwamnati mai ci.

Ologbondiyan, ya yi ikirarin cewa gwamnoni da sauran jiga-jigan adawa da ke komawa APC, suna haka ne domin a yafe masu "zunubbansu."

Kola Ologbondiyan.
Tsohon kakakin PDP na kasa, Kola Ologbondiyan ya caccaki masu sauya sheka zuwa APC Hoto: Kola Ologbondiyan
Asali: Twitter

Ologbondiyan ya bayyana hakan ne a cikin shirin siyasa a yau na gidan talabijin na Channels a ranar Litinin, 12 ga watan Mayu, 2027.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin gwamnoni da jiga-jigai na komawa APC

Ya ce waɗanda ke sauya sheƙa suna neman wurin da ake “yafe zunubi” ne kawai, yana mai nuni da maganar da tsohon shugaban APC da ya yi cewa duk wanda ya koma jam'iyyar za a yafe masa laifuffukansa.

"Kada ku manta cewa tsohon shugaban APC ya shaida wa ‘yan Najeriya cewa, ku zo APC, za a yafe muku dukkan zunubanku. Don haka mutane suna neman inda ake yafe zunubi ne kawai,” in ji Ologbondiyan.

A cikin watan da ya gabata, gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, tare da tsohon gwamna Ifeanyi Okowa, kwamishinoni da shugabannin jam’iyya suka fice daga PDP zuwa APC.

Hakan dai ya kara ƙarfafa jita-jitar da ake yaɗa wa cewa wasu gwamnonin za su bi sahunsu nan ba da jimawa ba.

Jam'iyyar APC za ta gwabza ne da ƴan Najeriya

Sai dai Ologbondiyan ya jaddada cewa, duk da yawan shugabannin da APC ke janyo wa zuwa cikinta, dole sai jam'iyyar ta kayar da miliyoyin ƴan Najeriya kafin ta samu tazarce a 2027.

"Za ka iya tara dukkan gwamnonin 36 a daki guda ka ce su sauya sheƙa zuwa APC. Amma za ka iya tara ‘yan Najeriya miliyan 200 a wancan ɗakin guda? Amsa ita ce, a’a".
Felix Morka.
Tsohon kakakin APC ya ce ba don Allah ƴan siyasa ke komWa APC ba Hoto: Felix Morka
Asali: UGC

APC ta tsame kanta daga rikicin PDP

A martanin da ya mayar a wannan shirin, Felix Morka, kakakin APC na ƙasa, ya soki PDP bisa dora alhakin rikicinta na cikin gida kan jam’iyya mai mulki.

“Na tabbata abokina Kola Ologbondiyan ba da gaske yake ba, domin ba zai yiwu a zargi APC da rashin daidaito da gazawar jam’iyyar PDP ba.
“Idan PDP ba za ta iya warware rikicin da ke tattare da shugabancinta ba, me ya sa za a yarda da ita wajen tafiyar da mulkin ƙasa?”

- In ji Felix Morka.

Jigon APC ya ce Amaechi ne ya dace da Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa jigon APC a jihar Ribas, Eze Chukwuemeka Eze ya ce ƴan Najeriya sun fara kiran tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya fito takara.

Mista Eze ya ce Amaechi, tsohon gwamnan jihar Ribas yana da nagarta da duk wani abu da ake buƙata domin tsamo Najeriya daga ƙangi.

Ya bukaci ƴan Najeriya su kara haƙuri, domin yana fatan daga nan zuwa zaɓen 2027, tsohon ministan zai fito ya faɗi shawarar da ya yanke.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262