2027: Takarar Kwankwaso da Obi Ta Sake Samun Karfi, Dattawa Sun Mara Masu Baya
- Wata kungiyar Dattawan Igbo ta bayyana wanda za ta goyi baya a zaben shugaban kasa na shekarar 2027 da ake tunkara
- Dattawan sun yaba da tsarin tikitin takarar Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NDC gabanin zaben 2027
- Rabi'u Kwankwaso ya yaba da kyakkyawar alakarsa da Obi, yana mai jaddada kudirin NDC na samun nasara a zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa ya karbi bakuncin wata tawaga ta Dattawan Igbo a gidansa da ke Abuja.
Tsohon gwamnan Kano ya nuna jin dadi game da ziyarar da kuma bayyana alakar da ke tsakaninsa da Peter Obi a tafiyar NDC.

Source: Facebook
Kwankwaso ya sanar da hakan ne ta wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana ziyarar a matsayin wata muhimmiyar alama ta hadin kai da goyon baya.

Kara karanta wannan
Rikicin NDC na kara kamari, Dickson ya ce ya fi Obi da Kwankwaso cancanta da takara a 2027
Abin da ya daɗaɗa wa dattawan Igbo rai
A cewarsa, Dakta S.N. Okeke, shugaban Majalisar Dattawan Ohanaeze na jihohi 19 da Babban Birnin Tarayya, ne ya jagoranci tawagar tare da tsohon gwamnan Enugu, Okwesilieze Nwodo.
Ya ce dattawan sun nuna jin dadinsu kan yadda alakarsa da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ke kara karfi da fahimtar juna.
Sun bayyana cewa wannan hadin gwiwa tsakanin Obi da Kwankwaso wata alama ce mai kyau ta dunkulewar kasa da bai wa kowa damar shiga siyasa.
A cewar Kwankwaso, sun yi alkawarin ba da cikakken goyon baya ga tikitin Obi da Kwankwaso tare da tara kuri'u masu yawa.
Ya ce dattawan sun tabbatar da cewa za su yi aiki tukuru domin samun gagarumar nasara ga tikitin a Kudu maso Gabas da sauran yankunan Kudancin Najeriya.
Ya ce:
"'Dattawan sun nuna matukar farin ciki kan kyakkyawar alakar da ke tsakaninmu da Mai Girma Mista Peter Obi a karkashin NDC."

Kara karanta wannan
Atiku ya yi murna da ceto mutane 360, ya ce sojoji za su iya murkushe ta'addanci a Najeriya

Source: UGC
Godiyar da Kwankwaso ya yi ga dattawan
Da yake mayar da martani, Kwankwaso ya gode wa tawagar bisa ziyarar da kuma damar tattauna muhimman batutuwan da suka shafi Najeriya.
Ya ce tattaunawar ta ba su damar waiwayen tarihin siyasar kasar nan, musamman dangantakar siyasa tsakanin Arewa da Kudu maso Gabas.
Tsohon gwamnan Kano ya bayyana gamsuwarsa da yadda yake aiki tare da Obi, yana mai cewa hadin gwiwar tana amfani ga manufofin jam'iyyar.
Kwankwaso ya sake jaddada biyayyarsa ga tafiyar OK Movement da kuma jam'iyyar NDC, yana mai cewa mambobi da magoya baya sun kuduri aniyar samun nasara.
Ya kara da cewa jam'iyyar za ta ci gaba da karfafa tsarinta da fadada goyon bayan jama'a a fadin kasa domin gina kawancen kasa mai fuskantar kalubalen Najeriya.
Dattawan Arewa sun caccaki Kwankwaso, Atiku, Tinubu
A baya, an ji cewa kungiyar Arewa Consultative Forum, ACF, ta bayyana damuwa game da salon mulkin Bola Tinubu bayan zaɓen 2023.
Ya ce Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ba su gabatar da sahihin tsarin da zai gamsar da yankin Arewa ba.
Kungiyar ta bayyana cewa matsin tattalin arziki, rashin tsaro da talauci za su yi tasiri a zaɓen 2027 da ake tunkara.
Asali: Legit.ng
