'Dan Majalisa Ya Fallasa Yadda Boko Haram Ta Kwace Makaman Tiriliyoyin Naira daga Sojoji
- 'Dan majalisa daga Filato, Yusuf Gagdi ya bayyana cewa Boko Haram sun kwace makaman sojoji da kudinsu ya kai tiriliyoyin Naira
- Ya ce Majalisa ta ware kuɗi masu yawa don sayen makamai da motocin yaƙi, amma ’yan ta’adda na ci gaba da kwace su a cikin ruwan sanyi
- Hon Gagdi ya yi gargaɗi cewa idan gwamnati ba ta ɗauki mataki ba, ’yan Najeriya za su iya ɗaukar matakin kare kansu da kansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Ɗan Majalisar Wakilai, Honorabul Yusuf Adamu Gagdi, ya bayyana cewa ’yan ta’addan Boko Haram sun kwace makaman da aka saya wa sojojin kasar nan.
Ya kara da bayyana takaicin yadda yan ta'addan suka kwace dukiyoyin sojoji da kuɗinsu ya kai tiriliyoyin naira a hare-haren da suka kai kan sansanonin soja da ke Arewa maso Gabas.

Asali: Facebook
Jaridar Aminiya ta wallafa cewa Hon. yusuf Gagdi ya fadi haka ne a lokacin da yake tofa albarkacin bakinsa a majalisa kan kudirin da Honorabul Ahmed Satomi daga jihar Borno ya gabatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hon Santomi ya yi magana ne a kan gobarar da ta tashi a ɗakin ajiyar makamai da ke Barikin Sojoji na Giwa a Maiduguri, da kuma yawaitar hare-haren Boko Haram a Borno da Yobe.
An koka kan ta'adin 'Yan Boko Haram
A cewarsa, barnar da ’yan ta’adda ke yi wa kayan aikin sojoji a wannan lokaci, ya kai wani matsayi da ba a taɓa ganin irinsa ba a baya.
Ya yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, za a fuskanci mummunan tasirin yan ta'addan, musamman ga shugabannin da aka zaɓa.
Gagdi ya ce:
"Na firgita da abin da Boko Haram ta aikata a Barikin Giwa da wasu wuraren soji. Wannan abu babban ƙalubale ne ga tsaron jama’a da zaman lafiyar ƙasar nan."
Boko Haram sun kwace makaman sojoji
A cewar Gagdi, Majalisar Tarayya ta amince da kuɗi masu yawa ga rundunar soji domin siyan motoci da makaman yaƙi fiye da guda 40, waɗanda kuɗinsu ya kai tiriliyoyin Naira.
Dan majalisar ya ce:
"To me zai hana a tambayi yadda za a iya tabbatar da tsaron jama’a, idan ’yan ta’adda za su kwace waɗannan makamai da motocin yaƙi?"
"Majalisa tana bakin ƙoƙarinta wajen ɗaukar matsaya a kan harkar tsaro, amma dole ne hukumomin gwamnati su tashi tsaye. Ya zama wajibi shugaban ƙasa ya binciki manyan hafsoshin tsaro da sauran hukumomi game da wannan gazawa, sannan ya ɗauki matakin da ya dace."

Asali: Facebook
Ya ƙara jan hankalin gwamnati da hukumomin tsaro cewa idan suka cigaba da nuna halin ko-in-kula, zai sa al’umma su daina amincewa da su, kuma hakan barazana ce.
Boko Haram ta kashe babban soja
A baya, mun ruwaito cewa yan ta’addan Boko Haram sun kai wani hari ƙauyen Izge da ke ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno, inda suka kashe wani Kyaftin ɗin sojoji.
Sarkin Gwoza, Mai Martaba Alhaji Mohammed Shehu Timta, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce maharan sun kai harin da daddare, kuma an kashe karin soja daya.
Sarkin ya bayyana cewa maharan sun tsere daga yankin bayan fafatawar, suka bar makamai da babura fiye da guda 10, lamarin da ya kara jefa jama'a a cikin dar dar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng