Kwanakin Matsalar Wuta Zai Zo Karshe, Tinubu Ya Cusa N4bn domin Kawo Sauyi

Kwanakin Matsalar Wuta Zai Zo Karshe, Tinubu Ya Cusa N4bn domin Kawo Sauyi

  • Shugaba Bola Tinubu ya shirya kawo daukar mataki mai muhimmacin a bangaren wutar lantarki domin inganta bangaren
  • Tinubu ya ce bangaren wutar lantarki ya gaji matsaloli masu yawa, ciki har da ƙarancin samar da wuta da tarin basussuka
  • Ya bayyana cewa gyare-gyaren da ake yi za su jawo zuba jari, samar da ayyukan yi da inganta tattalin arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce an bai wa Kwamitin Musamman na Fadar Shugaban Ƙasa kan harkokin wutar lantarki izinin ware makudan kudi a bangaren.

Tinubu ya umarci kwamitin ya ware Naira tiriliyan huɗu ta hanyar domin biyan ingantattun tsofaffin basussukan bangaren wutar lantarki a Najeriya.

Tinubu ya dauko hanyar inganta bangaren wuta
Shugaba Bola Tinubu yayin bikin ranar tunawa da mazan jiya a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin jawabinsa na Ranar Dimokuraɗiyya, inda ya ce an ɗora wa kwamitin alhakin magance matsalolin ƙarancin kuɗaɗe a harkar harkokin wutar lantarki, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Sace dalibai: Gwamna ya umarci rufe makarantu bayan samun rahoton DSS

Wasu daga cikin matakan da Tinubu ya dauka

Shugaban ya tabbatar da cewa cikin matakin da ya dauka har da basussukan da ake bin kamfanonin samar da wuta da na rarraba ta.

Ya ce lokacin da gwamnatinsa ta karɓi mulki a shekarar 2023, bangaren wutar lantarki ya kasance cikin matsalolin ƙarancin samar da wuta, rashin tabbataccen iskar gas da kuma raunin hanyoyin isar da wutar lantarki.

A cewarsa, kamfanonin rarraba wutar lantarki sun kasance cikin matsanancin hali, tare da gibin mitoci da ya haura miliyan huɗu, yayin da harkokin wutar lantarki ta nutse cikin tarin tsofaffin basussuka.

Tinubu ya ce sakamakon haka, bangaren ya kasa samar da wutar da ta kai ƙarfin megawatt 13,500 da aka girka, sannan ya kasa isarwa da rarraba yadda ya kamata tare da tattara kuɗaɗen shiga da za su tabbatar da dorewarsa.

Ya ƙara da cewa ya rattaba hannu kan Dokar Wutar Lantarki domin bai wa jihohi damar shiga harkokin samarwa, isarwa da rarraba wutar lantarki.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta kashe Naira biliyan 10, Tinubu ya kafa kwamitin gaggawa a yaki Ebola

Tinubu ya tuna yadda ya samu wutar lanatarki
Shugaba Bola Tinubu da sabon ministan makamashi, Joseph Tegbe. Hoto: @StateHouse/x.
Source: UGC

Umarnin Tinubu a bangaren wutar lantarki

Shugaban ya ce Kwamitin Musamman kan Wutar Lantarki na ci gaba da aiki domin rage gibin mitoci, kuma an ba shi izinin ware Naira tiriliyan huɗu domin biyan ingantattun basussukan da ake bi.

Ya bayyana cewa Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara, tare da tallafin Bankin Duniya da Bankin Raya Afirka, na faɗaɗa ayyukan samar da wutar lantarki ga yankunan da ba su da isasshen wuta.

Tinubu ya jaddada cewa wutar lantarki wata ribar dimokuraɗiyya ce dakowane dan Najeriya ke bin gwamnati bashi, yana mai cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar samar da ita, cewar Punch.

Tinubu ya ba yan ta'adda zabi a Najeriya

A wani labarin, an ji cewa shugaba Bola Tinubu ya yi jawabi ga ƴan Najeriya yayin bikin ranar dimokuraɗiyya ta shekarar 2026 da ake yi.

Tinubu ya gargadi 'yan bindiga da masu daukar nauyin ta'addanci su mika wuya ko su fuskanci hukunci mai tsanani.

Ya ce an kashe sama da 'yan ta'adda 13,000 cikin shekara guda, yayin da sama da mutum 124,000 suka ajiye makamansu daga 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.