Bayan Taron Gwamnoni, An Hango Abin da Zai Iya Ƙarasa Murƙushe PDP Kafin 2027

Bayan Taron Gwamnoni, An Hango Abin da Zai Iya Ƙarasa Murƙushe PDP Kafin 2027

  • Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa son zuciya kaɗai na iya ƙarisa kashe jam'iyyar PDP gabannin zaɓen 2027
  • Wike, tsohon gwamnan Ribas ya ce alamu sun nuna PDP za ta samu nasara ba a zaɓen 2027 matuƙar abubuwa suka ci gaba da tafiya a haka
  • Ya kuma bayyana sauya shekar tsohon gwamnan Delta kuma abokin takarar Atiku a zaɓen 2023, Ifeanyi Okowa a matsayin dabarar siyasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya ce jam’iyyar adawa ta PDP ba za ta iya samun nasara ba a zaɓen 2027.

Nyesom Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas ya yi gargaɗin cewa son zuciya na iya ƙarisa PDP ta mutu murus kafin babban zaɓen 2027 da ake tunkara.

Nyesom Wike.
Wike ya gargaɗi PDP, ya ce son zuciya zai ƙarisa kashe jam'iyyar kafin 2027 Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Twitter

Wike ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai da aka shirya a Abuja ranar Litinin, kamar yadda Leadership ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya gargaɗi PDP ta kaucewa son zuciya

Ministan na Abuja ya yi gargadin cewa abubuwan da ke faruwa a cikin PDP yanzu na iya ruguza jam’iyyar kafin zaben 2027.

"Mutane na ta magana kan gwamnan Delta da magabacinsa saboda sun koma APC, laifi suka yi? Ko kawai saboda sun ce za su goyi bayan Shugaba Tinubu ne?
"Amma Shugaban Kwamitin Amintattu (BoT) na PDP, wanda ya kamata ya kasance abin koyi a jam’iyyar, ya fito karara ya marawa Gwamna Alex Otti na jam’iyyar LP baya, babu wanda ya ce komai a kai.”

- Nyesom Wike.

Me zai iya ƙarasa murƙushe PDP kafin 2027

Ya zargi PDP da yin watsi da aikin gina jam’iyya da jawo sababbin mambobi, maimakon haka ta maida hankali kan cin mutuncinsa saboda yana cikin gwamnatin APC.

A ruwayar Vanguard, Ministan ya ce:

"Ni kadai ne tsohon gwamna da bai goyi bayan dan takarar shugaban kasa na PDP ba, amma na tabbatar PDP ta yi nasara 100% a zaɓukan gwamna, ‘yan majalisu na jiha da na tarayya a jihata. Waye kuma ya yi hakan?”

Wike ya ce idan PDP ba ta kaucewa rashin adalci da son zuciya ba, tarihi zai sake maimaita kansa a zaben 2027.

“Ba ku ci zabe ba amma kuna korar wasu daga jam’iyya. Kuna son maimaita abin da kuka yi ne a 2023? Ba za ku kai labari ba, ku canza salo tun lokaci bai ƙure ba.
Wike.
Wike ya ce dabarar siyasa ce ta sa Okowa da gwamnan Delta suka koma APC Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Facebook

Wike ya yi magana kan sauya shekar gwamna

Ya kuma bayyana ficewar tsohon gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, daga PDP zuwa APC a matsayin hikima da wayo na siyasa, yana mai cewa PDP ta kasa hangen hakan, duk da ya sha gargadi.

“Na sha gaya musu, ku kula. Amma suka ce wai su gwamnoni ne, babu matsala. Bari mu ga abin da zai faru nan gaba," in ji shi.

Nyesom Wike ya soki Atiku Abubakar

A wani labarin, kun ji cewa Wike ya bayyana tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar a matsayin mutumin da ba ya cika alƙawari.

Ministan na harkokin Abuja ya ce babu dalilin da zai sa ya marawa Atiku baya domin bai manta abin da aka yi masa ba a zaɓen 2019.

Wike ya zargi Atiku da wasu manyan kusoshin PDP ciki har da tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da saɓawa yarjejeniyar da suka yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262