Sarki Sanusi Ya Yi wa Kashim Shettima Raddi kan Dangote da Abdul Samad Rabiu
- Sarki Muhammadu Sanusi II ya ce jihar Kano ce ta assasa tushen nasarar kasuwancin Alhaji Aliko Dangote da Abdul Samad Rabiu
- Sanusi II ya ce Dangote da Abdul Samad sun fara harkoki ne a Kano kafin su faɗaɗa kasuwancinsu zuwa Legas da sauran yankuna
- Kalaman sarkin sun zo ne bayan Kashim Shettima ya ce Legas ce ta samar da attajirin Afirka, Aliko Dangote da Abdul Samad a wani taro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Sarki Muhammadu Sanusi II, ya ƙalubalanci kalaman da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya yi kwanan nan kan Aliko Dangote da mai kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu.
Sarkin ya jaddada cewa Kano ce, ba Legas ba, ta assasa tushen kasuwancin attajirin Afirka, Aliko Dangote, da hamshaƙin ɗan kasuwa Abdul Samad Rabiu.

Source: Facebook
Business Day ta rahoto cewa Sanusi II ya yi wannan bayani ne yayin da yake jawabi ga mambobin ICSAN, inda ya bayyana tarihin Kano a matsayin cibiyar kasuwanci da kuma matattarar fitattun ‘yan kasuwa.
Raddin Sanusi II ga Shettima
A cewar sarkin, Dangote da Abdul Samad sun taso ne daga al’adar kasuwanci mai zurfi da Kano ta daɗe tana da ita kafin daga bisani su faɗaɗa daulolin kasuwancinsu a faɗin Najeriya da sauran ƙasashe.
“Waɗannan ‘yan kasuwa sun tafi Legas ne domin faɗaɗa harkokinsu da kuma koyon abubuwa daga yanayin kasuwancin da ke can, ba domin koyon yadda ake fara kasuwanci tun daga tushe ba,”
In ji Sanusi.
Ya ƙara da cewa Kano ta daɗe tana samar da fitattun ‘yan kasuwa da masu zuba jari, yana mai cewa tarihin kasuwancin jihar ya taka muhimmiyar rawa wajen gina wasu daga cikin manyan attajiran Afirka.
Daily Post ta wallafa cewa ana kallon kalaman sarkin a matsayin martani ga abin da Shettima ya faɗa yayin taron tattalin arziki da jawo masu zuba jari a jihar Legas
Abin da Shettima ya fada
A taron, mataimakin shugaban kasar ya yaba da yanayin tattalin arziki da shugabanci a jihar Legas, yana mai cewa Legas ce ta samar da attajirin mutum mafi arziki a Afirka.
“Legas ce ta samar da attajirin Afirka, ba Kano ba. Aliko Dangote ɗan Legas ne. Haka kuma ba Kano ce ta samar da mutum na biyu mafi arziki a Afirka ba, Abdul Samad Rabiu,”
In ji Shettima.
Mataimakin shugaban kasar ya yi wannan furuci ne yayin da yake jaddada gudunmawar da jihar Legas ke bayarwa ga tattalin arzikin Najeriya da kuma rawar da take takawa wajen bunƙasa kamfanoni masu zaman kansu da samar da arziki.

Source: Facebook
Sanusi II ya gana da Turawa
A wani labarin, kun ji cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya gana da wata tawaga mai karfi daga tarayyar Turai a jihar Kano a makon nan.
Jakadan tarayyar Turai ya hada kan jakadun kasashen Turai da suka hada da Italy, Spain, Faransa da sauransu zuwa jihar Kano wajen sarkin.
Sarkin ya bayyana cewa ya sanar da su muhimman abubuwa game da tarihin jihar Kano, inda daga baya ya masu hawa na musamman.
Asali: Legit.ng

