"Talauci da Jahilci Sun Yi Kamari a Arewa": Sarki Sanusi Ya ba da Mafita
- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bukaci shugabanni su mayar da hankali kan aiwatar da ayyuka maimakon yawan sanarwar za su yi aiki
- Ya nuna damuwa kan yadda talauci, rashin ingantaccen ilimi da matsalolin kiwon lafiya ke ci gaba da addabar miliyoyin mutane a Arewa maso Yamma
- Sarkin ya bayyana haka ne a wani muhimmin zama da jagororin yankin suka yi a jihar Kano domin nemo mafita a kan matsalolin da suka dame su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bukaci shugabanni a Arewa maso Yamma da ma Najeriya baki daya su daina maye gurbin aiki da yawan sanarwar za a yi aikin.
Ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a fuskanci matsalolin talauci, jahilci da rashin ingantaccen tsarin kiwon lafiya da suka addabi yankin a kuma yi maganinsu.

Kara karanta wannan
"Suna tare cikin daki"; Tsohon jami'in DSS ya fadi abin da ya kashe Janar Sani Abacha

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Sarki Sanusi ya bayyana haka ne a wani babban taron tattaunawa kan manufofi da aka gudanar a Kano ranar Laraba, 10 ga watan Yuni, 2026 a jihar Kano.
Kiran Sarkin Kano ga Arewa
Jaridar Daily Post ta kawo labarin cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya jaddada bukatar daukar matakan da za su haifar da sauyi mai ma’ana a rayuwar al’umma.
Sarkin ya ce duk da shekaru da aka kwashe ana aiwatar da shirye-shirye da tsare-tsare daban-daban, har yanzu al’ummomi da dama a yankin suna fama da matsanancin talauci.
Ya kara da cewa har yanzu, mutanen Arewa maso Yamma na fama da karancin damar samun ingantaccen ilimi da kuma rashin wadatattun ayyukan kiwon lafiya.

Source: Facebook
Ya kara da cewa ci gaba ba zai samu yadda ya kamata ba muddin shugabanni suna kauce wa tunkarar hakikanin matsalolin da ke gaban su ko kuma suna kasa aiwatar da matakan da suka dace.
Khalifa Sanusi ya zaburar da shugabanni
Khalifa Muhammadu Sanusi ya yi gargadin cewa al’adar yawan alkawura ba tare da sakamako a kasa ba na ci gaba da kawo cikas ga cigaban yankin.
Ya bayyana cewa wajibi ne shugabanni su tabbatar da cewa manufofi da shirye-shiryen gwamnati suna inganta rayuwar jama’a kai tsaye maimakon kasancewa a takarda kawai.
Sarkin ya kuma jaddada cewa magance talauci da gibin da ke tsakanin masu hali da talakawa na bukatar shugabanci na gaskiya tare da ci gaba da zuba jari a muhimman fannoni kamar ilimi da lafiya.
Gwamnonin Arewa sun taru a Kano
A baya, mun ruwaito cewa gwamnonin yankin Arewa maso Yamma sun yi wata muhimmiyar ganawa a jihar Kano saboda matsalolin da suka addabi yankin.
Shugabannin yankin sun fara aiwatar da tsare-tsaren hadin gwiwa domin rage talauci wanda ya yi katutu a tsakanin al'ummarta tare da nemi mafita ga sauran matsaloli.
Taron ya bayyana cewa talauci, rashin tsaro, matsalolin lafiya, sauyin yanayi da yara da ba su zuwa makaranta na bukatar mafita ta bai daya da shiyyar za ta dauka.
Asali: Legit.ng
