'Dan Takarar Gwamnan Bauchi zai Gamu da Cikas da PDP Ta Taso Shi a gaba
- 'Dan takarar gwamnan PDP a Bauchi, Adamu Usman Ahmed, ya ce ba zai bari Gwamna Bala Mohammed ya dora magajinsa a mulki ba
- Ya bayyana cewa tarihin siyasar Bauchi ya nuna babu gwamnan da ya taba samun nasarar dora wanda zai gaje shi, kuma ba za a fara yanzu ba
- Adamu Usman Ahmed ya yi alkawarin mayar da hankali a kan share hawayen mutanen garin, musamman ta fuskar samar da ayyukan yi ga matasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Bauchi – Dan takarar kujerar gwamnan jihar Bauchi na jam'iyyar PDP, Adamu Usman Ahmed, ya bayyana cewa ba zai bari gwamna Bala Mohammed ya dora wanda zai gaje shi a zaben da ke tafe ba.
Adamu Usman Ahmed ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai a Abuja, inda ya nuna kwarin gwiwar cewa jam'iyyarsa za ta samu nasara a jihar Bauchi.

Source: Twitter
Daily Trust ta wallafa cewa Bala Mohammed, wanda a baya ya kasance shugaban kungiyar gwamnonin PDP, ya koma jam'iyyar APM bayan rikicin cikin gida ya haifar da bangarori biyu a PDP.
Bauchi: 'Dan takarar PDP ya ja layi
Daily Post ta kawo labarin Adamu Usman Ahmed ya ce yana da yakinin samun nasara a zaben gwamna, kuma al'ummar Bauchi sun shirya tsaf domin zabar jam'iyyar adawa.
Ya bayyana cewa mutanen jihar suna da hikima wajen yanke hukunci a lokacin zabe, yana mai cewa tarihin siyasar Bauchi ya nuna babu wani gwamna da ya taba samun damar dora wanda zai gaje shi bayan kammala wa'adinsa.
A cewar dan takarar gwamnan, wannan al'amari na kara nuna cewa jam'iyyun adawa na da damar samun nasara a zaben da ke tafe.
Adamu Usman Ahmed ya kuma ce yanayin siyasar yanzu ya sha bamban da yadda aka saba gani a baya, musamman yayin da ake tunkarar zaben 2027.

Kara karanta wannan
Rikicin NDC na kara kamari, Dickson ya ce ya fi Obi da Kwankwaso cancanta da takara a 2027
Siyasar Bauchi ta canja, cewar Adamu
Adamu Usman Ahmed ya bayyana cewa a baya ana ganin fafatawar siyasa tsakanin manyan jam'iyyu biyu ne kawai, amma yanzu akwai jam'iyyu da dama da za su fafata a zaben gwamna.
'Dan takarar ya ce yawaitar 'yan takara daga jam'iyyu daban-daban na daga cikin abubuwan da ke ba shi karin damar samun goyon bayan masu kada kuri'a.

Source: Twitter
A cewarsa, zabe mai zuwa zai kasance na musamman saboda akwai kusan jam'iyyu bakwai zuwa takwas da ke neman kujerar gwamna, sabanin yadda aka saba gani a baya.
Da yake bayyana shirinsa idan aka zabe shi gwamna, Adamu Usman Ahmed ya ce samar da ayyukan yi ga matasa da sauran al'umma ne zai kasance babban abin da gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali a kai.
Gwamnan Bauchi ya tsayar da 'dan takara
A baya, kun samu labarin cewa Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya sha alwashin tunkarar duk wani nau’i na magudin zabe a babban zaben 2027 mai zuwa.

Kara karanta wannan
"Sau 3 kacal na ga ƴaƴana," Zulum ya tuno abin da ya faru da shi bayan zaben 2019
Bala Mohammed ya yi magana ne yayin da jam’iyyar APM ta tabbatar da shi a matsayin dan takararta na Sanata a mazabar Bauchi ta Kudu yayin da ake ci gaba da shirya wa zabe mai zuwa.
APM ta kuma ta tabbatar da kwamishinan kudi, Yakubu Adamu, a matsayin dan takararta na gwamna da Nuhu Zaki a matsayin dan takarar Sanata a fafatawar da za a yi da jam'iyyun siyasa.
Asali: Legit.ng
