Jim Kadan bayan Ziyarar Tinubu, Tsohon Kwamishina Ya Tattara Kayansa Ya Koma APC
- Jam'iyyar APC ta ci gaba da samun karuwa da ƴan siyasa a Najeriya ke turuwar sauya sheƙa daga jam'iyyu daban-daban
- Tsohon kwamishinan harkokin filaye da matasa na Anambra, Hon. Bonaventure Enemali ya fice daga APGA zuwa APC
- Ya bayyana cikakken goyon bayansa ga shugaban kasa da ɗan takarar gwamnan APC a Anambra, Prince Nicholas Ukachukwu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Anambra - Tsohon kwamishinan filaye da matasa a Jihar Anambra, Hon. Bonaventure Enemali, ya sauya sheka daga jam'iyyar APGA zuwa APC.
Enemali ya bayyana wannan sauyin sheƙa ne a wurin wani taron siyasa da aka gudanar a mazaɓarsa Nzam a jihar da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.

Asali: Facebook
Tsohon kwamishinan ya sha alwashin goyon bayan ɗan takarar gwamna na APC, Prince Nicholas Ukachukwu a zaben Anambra mai zuwa, Leadership ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matashin ɗan siyasar ya bayyana Ukachukwu a matsayin “jagora mai hangen nesa wanda zai iya sauya Anambra zuwa mafi alheri.”
Bola Tinubu ya kai ziyara a Anambra
Wannan sauya sheka dai na zuwa ne bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar kwana ɗaya jihar Anambra.
Yayin ziyarar, Bola Tinubu ya kaddamar da ayyukan da Gwamna Charles Soludo ya kammala ciki har da sabon gidan gwamnati.
Bonaventure Enemali ya ce ya yanke shawarar ficewa daga jam'iyyar APGA ne domin cika burinsa na samar da shugabanci na gari da haɗa kan al'umma.
Tsohon kwamishinan ya nuna kwarin gwiwa da tabbacin cewa Ukachukwu zai kawo ci gaba mai ɗorewa idan ya samu nasara a zaɓen gwamnan Anambra mai zuwa.
Me yasa tsohon kwamishina ya shiga APC
"Ba haka kurum na dawo APC ba, burin gina Anambra a kan turbar ci gaba ne ya sa na yanke shawarar komawa jam'iyyar APC.
"Saboda haka ina bayyana cikakken goyon bayana ga tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027,” in ji Enemali.
Ana ganin dai komawar tsohon kwamishinan zai ƙarawa APC ƙarfi saboda ƙarfin da yake da shi a siyasa yayin da ake shirye-shiryen zaɓen gwamnan Anambra a watan Nuwamba, 2025.

Asali: Getty Images
Jam'iyyar APC ta yi maraba da matashin ɗan siyasa
Shugabannin jam'iyyar APC a jihar sun tarbe shi hannu bibbiyu, tare da ba shi tabbacin cewa ba za a nuna masa banbanci ba, rahoton Guardian.
Bugu da ƙari, jagororin APC sun bayyana fatan cewa sauran manyan ’yan siyasa za su biyo baya domin sauya akalar siyasar jihar Anambra a zaɓe mai zuwa.
APC na son maida Najeriya ƙarƙashin jam'iyya 1?
A wani labarin, kun ji cewa shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje ya ce idan har ƴan Najeriya na son ƙasarsu ta koma jam'iyya ɗaya ke mulki, to ba wani abu ba ne dan ta zama hakan.
Ganduje ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan ya jagoranci sanatocin jihar Kebbi uku zuwa wurin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Tsohon gwamnan na Kano ya ce tara jam'iyyun siyasa a ƙasa ba shi da wani amfani kuma naƙasu ne ga kokarin kafa shugabanci nagari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng