"Tinubu ba Zai Iya ba," Jigon APC Ya Cire Tsoro, Ya Faɗi Wanda Ya Dace da Mulkin Najeriya
- Jigon APC a jihar Ribas, Eze Chukwuemeka Eze ya ce ƴan Najeriya sun fara rokon tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya fito takarar
- Mista Eze ya bayyana Amaechi a matsayin mutum mai nagarta wanda ya dace da shugabancin Najeriya a 2027 a halin da ƙasar ke ciki
- Ya kuma soki gwamnatin Bola Tinubu saboda yadda ta maida hankali wajen shirin zaɓe maimakon magance damuwar talakawa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - Wani jigo a APC, Eze Chukwuemeka Eze, ya bayyana tsohon Ministan Sufuri, Chibuike Amaechi, a matsayin wanda ya dace ya karɓi shugabancin Najeriya a 2027.
Mista Eze ya ce Amaechi, tsohon gwamnan jihar Ribas yana da nagarta da duk wani abu da ake buƙata domin tsamo Najeriya daga ƙangin da ta tsinci kanta a ciki.

Asali: Facebook
Eze, wanda ke da kusanci da Amaechi, ya faɗi hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a birnin Fatakwal, babban birnin jihar Ribas, kamar yadda Leadership ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shin Amaechi zai nemi shugabanci a 2027?
Ya ce duk da Amaechi bai tabbatar masa da cewa yana sha'awar tsayawa takara ba, amma mutane da dama sun fara kiraye-kirayen ya nemi kujerar shugaban ƙasa a 2027.
Ya bukaci 'yan Najeriya da ke neman sanin matsayar Amaechi su yi haƙuri, domin lokaci zai yi da tsohon ministan zai fito fili ya faɗi shirinsa a siyasa.
Eze ya ce a halin yanzu siyasa, dimokuraɗiyya da shugabanci a Najeriya na bukatar gyara, yana mai cewa abubuwan nan guda uku kamar gine-gine ne masu tsayi amma babu tushe.
Jigon APC ya soki gwamnatin Bola Tinubu
“Gwamnati mai ci ta gaza, domin a yanzu ta fi maida hankali wajen tsara dabarun yadda za ta yi tazarce a 2027, maimakon magance matsalolin jama'a.
"Tattalin arziki na tangal-tangal, yunwa da rashin tsaro da kashe-kashen da ake yi kullum sun isa su sa gwamnati a damuwa amma ba shi ne a gabansu ba, sun fi maida hankali kan yadda za su ci gaba da mulki.”
- In ji Eze Chukwuemeka Eze.
Wane irin shugaba Najeriya ke buƙata?
Eze ya kara da cewa:
“Najeriya na bukatar shugaba mai hangen nesa, kuma ba abin mamaki ba ne dan mutane sun yi kira ga Amaechi ya fito takara.
"Kowa ya san irin jajircewarsa da sadaukarwarsa wajen ganin Najeriya ta gyaru. Idan ya bayyana aniyarsa, zan fito na sanar da duniya.”

Asali: Facebook
Ya bayyana Amaechi a matsayin mutumin da ya sadaukar da kansa wajen hidimar jama’a kuma ya cancanci shugabanci, kamar yadda Daily Post ta kawo.
“A lokacin da ake fama da matsaloli, ana bukatar irin Amaechi domin ceto Najeriya daga wannan hali da take ciki,” in ji shi."
Kallon da wasu ke yiwa gwamnatin Tinubu
A Najeriya, rashin nasara a bangaren tattalin arziki, tsaro da jin daɗin jama'a ya sa wasu 'yan siyasa da masu ruwa da tsaki a ƙasar ke kallon gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin wadda ba ta cika tsammanin da jama'a ke da shi ba.
Tun bayan hawansa kan mulki a Mayu 2023, abubuwa da dama sun fara rikicewa, musamman bayan cire tallafin man fetur da kuma yawan hauhawar farashin kayayyaki, wanda hakan ya ƙara tsananta rayuwar talakawa.
Ƙarin matsin lamba da ke tasowa daga tsadar rayuwa, rashin tsaro da karancin kudin shiga ya sa gwamnati ke fuskantar suka daga bangarori da dama, ciki har da 'yan jam’iyyarsa ta APC.
Wasu daga cikinsu na ganin gwamnatin ta karkata ne wajen shirye-shiryen siyasa da batun sake tsayawa takara a 2027, maimakon magance manyan matsalolin da suka addabi al’umma.
Jigogi irin su Eze Chukwuemeka Eze na ganin cewa irin wannan salon mulki na nuna rashin iya tafiyar da gwamnati.
Don haka, suna kallon irin su Rotimi Amaechi a matsayin madogara don ceto Najeriya daga halin da take ciki, suna mai zargin cewa tsarin mulki da shugabanci a yanzu na bukatar sabbin jagorori masu hangen nesa.
Amaechi ya sa baki a rikicin jihar Ribas
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi ya tsoma baki kan rikicin siyasar da ya addabi jiharsa.
Amaechi ya yi ikirarin cewa rikicin da ya haɗa Gwamna Siminalayi Fubara da ministan Abuja, Nyesom Wike yana da alaƙa da kasafta dukiyar Ribas.
Tsohon ministan sufurin ya kuma ce dokar ta ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya kafa a jihar ta saɓawa kundin tsarin mulki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng