Shugaban APC, Ganduje Ya Taso Sule Lamido a Gaba kan Batun Komawa PDP

Shugaban APC, Ganduje Ya Taso Sule Lamido a Gaba kan Batun Komawa PDP

  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, ya yi wa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido martani kan batun komawa PDP
  • Ganduje ya bayyana cewa zai ci gaba da zama daram a APC domin ko kaɗan bai da niyyar ficewa daga cikin jam'iyya mai mulki
  • Shugaban na APC ya buƙaci Sule Lamido da ya maida hankali wajen warware rikicin cikin gida da ya addabi jam'iyyar PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi martani ga kalaman tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido.

Ganduje ya bayyana cewa Alhaji Sule Lamido wanda yake babban jigo a jam'iyyar PDP, yana dab da sauya sheƙa zuwa APC mai mulki.

Ganduje da Sule Lamido
Ganduje ya ce Sule Lamido zai shigo APC Hoto: Sule Lamido, All Progressives Congress
Asali: Facebook

Ganduje ya bayyana hakan ne ranar Litinin ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Edwin Olofu, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdullahi Ganduje ya yi wa Sule Lamido raddi

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya musanta rahotannin da ke cewa yana shirin komawa PDP, inda ya sake jaddada cikakkiyar biyayyarsa ga jam’iyyar APC.

Shugaban na APC ya mayar da martani ne ga kalaman da Sule Lamido ya yi, inda ya ce jam’iyyar APC za ta rushe nan ba da jimawa ba, kuma cewa waɗanda suka bar PDP da suka haɗa da Ganduje za su dawo gida.

Ganduje ya ce a maimakon haka, Sule Lamido ne zai sauya sheƙa zuwa APC nan ba da daɗewa ba, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

Shugaban na APC ya bayyana iƙirarin na Sule Lamido a matsayin maras tushe wanda ya saɓawa hankali, ya jaddada cewa babu wani dalilin da zai sa ya bar jam’iyya mai mulki zuwa abin da ya ƙira da jam’iyyar adawa mai rauni.

Ya yi hasashen cewa PDP za ta zama tarihi kafin ƙarshen shekarar 2025, duba da rikice-rikicen cikin gida da jam’iyyar ke fama da su.

Me Ganduje ya ce kan Sule Lamido?

"Kowane mai hangen nesa ya san cewa ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, APC na ƙara samun karɓuwa a faɗin ƙasa, inda fitattun ƴan siyasa daga sassa daban-daban ke sauya sheƙa zuwa jam’iyyar."
“Tare da irin wannan goyon baya daga kowane lungu da saƙo na ƙasar nan, APC na ci gaba da tabbatar da nasarorinta da kuma shirin samun gagarumar nasara a zaɓen 2027."
“A taƙaice, nan ba da jimawa ba Sule Lamido zai shigo cikin APC, domin PDP ta mutu, ba shi da inda zai koma."

- Abdullahi Umar Ganduje

Abdullahi Umar Ganduje
Ganduje ya bukaci Sule Lamido ya maida hankali kan PDP Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Facebook

Ya shawarci Sule Lamido da ya mayar da hankalinsa wajen warware rikice-rikicen cikin gida da PDP ke ciki, maimakon ya rika yayata zancen da bai da tushe ballantana makama.

Babban jigo a PDP ya koma APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani babban jigon jam'iyyar PDP a jihar Edo, ya sauya sheƙa zuwa APC mai mulki a Najeriya.

Chief Tom Irehovbude ya koma jam'iyyar APC ne mai mulki a Edo tare da dubunnan magoya bayansa.

Tsohon jigon na PDP ya bayyana cewa gamsuwa da kamun ludayin mulkin Gwamna Monday Okpebholo ne ya sanya shi komawa APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng