Shugaban INEC Ya Raba Gardama kan Batun Korarsa daga Mukaminsa
- Shugaban hukumar INEC na kasa ya yi magana kan jita-jitar da ke cewa an sauke shi daga kan muƙamin da yake kai
- Farfesa Mahmud Yakubu ya nuna cewa ko kaɗan bai da wata masaniya kan batun cewa an raba shi da shugabancin hukumar
- Shugaban na INEC ya bayyana cewa za a yi wa dokar zaɓe kwaskwarima kafin babban zaɓen shekarar 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa za a yi sauye-sauye ga dokar zaɓe kafin babban zaɓen 2027.
Mahmud Yakubu ya kuma ƙaryata jita-jitar da ke cewa an cire shi daga muƙaminsa, yana mai jaddada cewa har yanzu shi ne ke jagorantar hukumar.

Asali: Facebook
Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yi magana ne bayan Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da sababbin kwamishinoni na ƙasa guda biyu a hukumar INEC.
Hukumar INEC na aiki tare da majalisa
Mahmud Yakubu ya ce INEC tare da wasu masu ruwa da tsaki sun tantance yadda zaɓen 2023 ya kasance, kuma sun fitar da shawarwari guda 142, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.
“Mun zo nan a yau ne musamman domin rantsar da sababbin kwamishinonin ƙasa guda biyu. Kamar yadda ku ka sani, hukumar tana da shugaba ɗaya da kuma kwamishinoni 12 daga yankuna shida na ƙasa, wato biyu daga kowane yanki."
"Don haka, akwai gurabe daga Arewa maso Yamma da kuma Kudu maso Gabas, inda majalisar dattawa ta tantance ta kuma amince da su, sannan shugaban ƙasa ya rantsar da su a yau."
- Mahmud Yakubu
Game da sauye-sauyen doka, Mahmud Yakubu ya ce INEC kwanan nan ta gana da kwamitocin majalisar tarayya kan sauye-sauyen dokar zaɓe a birnin Legas.
“Bayan haka, majalisar tarayya za ta shirya jin ra’ayin jama’a, kuma daga nan ne za a gabatar da sabon ƙudirin doka ga shugaban ƙasa domin ya rattaba hannu.”
"Don haka muna aiki tare da majalisar tarayya kan batun sauye-sauyen dokar zaɓe, amma a wannan mataki ba zan iya bayyana cikakken bayani ba. Majalisar Tarayya ce ke da haƙƙin hakan, kuma daga gare su ne za ku ji komai."
- Mahmud Yakubu

Asali: Getty Images
Menene gaskiya kan sauke Mahmud Yakubu?
Dangane da jita-jitar cewa an sauke shi daga muƙaminsa, Mahmud Yakubu ya ce:
“Ban ga dalilin ɓata lokaci kan wannan jita-jita maras tushe ba. Abin da na sani ta fuskar doka har yanzu ni ne shugaban hukumar INEC."
"A bisa kundin tsarin mulki ni ne kuma babban kwamishinan zaɓe na tarayya, a ƙarƙashin dokar zaɓe kuma ni ne jami’in da ke da hurumin bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasa."
Sababbin kwamishinonin INEC da aka rantsar su ne Mallam Tukur Abdulrazaq Yusuf daga Arewa maso Yamma da Farfesa Sunday Nwambam Aja daga jihar Ebonyi a Kudu maso Gabas.
Gyaran da INEC ke so a yi wa dokar zaɓe
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) na son a yi wa dokar zaɓe garambawul.
Ɗaya daga cikin gyaran da hukumar ke son a yi har da cire ikon naɗa kwamishinonin zaɓe na jihohi da shugaban ƙasa yake da shi.
Hukumar zaɓen na kuma neman sauya katin zaɓe daga PVC zuwa katin da za a iya amfani da shi a manhajar intanet domin sauƙaƙa wa masu kaɗa ƙuri'a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng