2027: El Rufa'i Ya Fadi Madogarar Kifar da Tinubu duk da Komawar Gwamnoni APC
- Tsohon gwamnan Kaduna ya ce kawancen jam’iyyu na da tsari da ya dogara kan jama’a kai tsaye, ba gwamnonin jihohi ba
- Nasir El-Rufa'i ya ce ko gwamnoni 36 duk sun goyi bayan shugaban kasa, idan jama’a ba su tare da shi, ba zai ci zaɓe ba
- El-Rufai ya bayyana cewa nasarar kowane zaɓe da za a yi tana hannun talakawan kasa ne, ba wasu manyan ‘yan siyasa ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa kawancen jam’iyyun adawa ba ta bukatar goyon bayan gwamnoni domin kayar da Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Tsohon gwamnan jihar Kadunan ya ce nasarar kowane zaɓe na hannun jama’a ne, ba shugabannin siyasa ba.

Asali: Twitter
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa El-Rufa'i ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da manema labarai a Kano ranar Juma’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya jaddada cewa tsarin su na neman kuri’un talakawa ne kai tsaye, ba tare da jingina da gwamnoni ba.
A cewar shi:
"Gwamna na da kuri’a ɗaya ne. Talakawan Najeriya na da kuri’u fiye da kowane gwamna ko ma dukkan su gaba ɗaya."
“Ba gwamnoni ke yanke sakamakon zaɓe ba”
El-Rufai ya ce goyon bayan gwamnoni bai da tasiri sosai idan jama’a ba su mara wa dan takara baya ba.
Ya ce kawancen su na kokarin gabatar da wata sabuwar hanya ta shugabanci da za ta zama madogara ga ‘yan Najeriya.
Nasir El-Rufa'i ya kara da cewa:
“Ko ka tara gwamnoni 36 gaba ɗaya, idan jama’a ba su tare da kai, to zaɓe ya ƙare. Wannan shi ne gaskiyar siyasa."
El-Rufai ya tuno da yadda Shugaba Tinubu ya fadi jihar Legas a 2023 duk da cewa yana da gwamna mai ci a jihar.
Tsohon gwamnan ya yi tambaya da cewa:
“Menene amfanin gwamna idan har za ka fadi jiha kamar Legas?”

Asali: Twitter
Darasin da El-Rufa'i ya koya daga zaɓen 2023
Yayin da yake bayyana irin darasin da ya samu a siyasarsa, El-Rufai ya ce ya yi iya ƙoƙarinsa domin tabbatar da nasarar Tinubu a jihar Kaduna a 2023, amma hakan bai yiwu ba.
Daily Post ta wallafa cewa El-Rufa'i ya ce:
“Na yi gwamna a Kaduna. Na yi iya bakin ƙoƙarina don nasarar Tinubu, amma ba mu kai ga cin nasara ba.
"Wannan darasi ne da na koya cewa talakawa ne ke yanke hukunci, ba manyan ‘yan siyasa ba.”
El-Rufai ya jaddada cewa za su mayar da hankali ne kan samun goyon bayan talakawa ba tare da dogaro da gwamnoni ko wasu manyan 'yan siyasa ba.
'Dole Tinubu ya zarce,' Festus Keyamo
A wani rahoton, kun ji cewa ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya ce dole ne Bola Tinubu ya zarce a 2027.
Festus Keyamo ya ce hakan zai taimaka wajen cigaba da ayyukan da Bola Tinubu ya fara tun hawa mulkin Najeriya a 2023.
Ministan ya bukaci 'yan APC su fifita tazarcen Bola Tinubu a kan dukkan wata bukatar siyasa da suke da ita a lokacin zabe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng