Wata Sabuwa: An Nemi Tinubu Ya Ajiye Shettima, Ya Dauki Kiristan Arewa a 2027

Wata Sabuwa: An Nemi Tinubu Ya Ajiye Shettima, Ya Dauki Kiristan Arewa a 2027

  • Kungiyar matasan Arewa ta bukaci Bola Tinubu ya zaɓi mataimaki Kirista daga Arewa domin samun nasara a zaɓen 2027
  • Shugaban kungiyar ya ce wannan mataki zai magance matsalar addini da yanki da aka samu a siyasar Najeriya a zaɓen 2023
  • Matasan sun bayyana cewa matakin zai ƙarfafa haɗin kai da kuma jawo hankalin masu kada ƙuri'a a sassan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja -Yayin da ake cigaba da magana kan zaɓen 2027, kungiyar Arewa Youth Movement ta ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawari.

Kungiyar ta bayyana wa Tinubu hanyar da zai bi domin sake samun nasara, inda ta ce ya zaɓi ɗan Arewa Kirista a matsayin mataimakinsa.

Shettima
Kungiyar Arewa ta bukaci Tnubu ya dauki Kirista mataimaki a 2027. Hoto: Bayo Onauga
Asali: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa an ce shawarar za ta taimaka wajen magance raɗaɗin da ya biyo bayan zaɓen 2023 dangane da rashin daidaiton addini tare da kara haɗa kan al'umma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kungiyar na kasa, Muhammed Sa’ad Aboki, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da suka gudanar a birnin Abuja a ranar Litinin.

Rahotanni sun nuna cewa matasan sun jaddada muhimmancin adalci da haɗin kai a harkokin siyasa.

Bukatar Kiristan Arewa a mataimakin Tinubu

Kungiyar ta bayyana cewa zaɓar Kirista daga Arewa a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa zai taimaka matuƙa wajen faɗaɗa karɓuwar Tinubu.

Ta bayyana cewa hakan zai yi tasiri musamman a yankunan Arewa ta Tsakiya da kuma yankunan da Kiristoci suka fi yawa.

Sa’ad Aboki ya bayyana cewa:

"Daga cikin manyan batutuwan da ake tattaunawa akwai yiwuwar sake tsayawa takarar shugaban ƙasa da Bola Tinubu zai yi, wanda ka iya sake sauya yanayin siyasar Najeriya."

Ya ƙara da cewa,:

"Zaɓar Kirista daga Arewa za ta taimaka wajen gyara matsalar rashin daidaito da aka fuskanta a 2023.
"Kuma zai isar da saƙon haɗin kai da mutunta bambancin addini da ke tsakanin 'yan Najeriya."

Tinubu
Wasu 'yan Arewa sun bukaci a ajiye Shettima a dauki wani a 2027. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Maganar gyara kura-kuran da suka gabata

Kungiyar ta ce sakamakon zaɓen 2023 ya nuna cewa akwai bukatar adalci da daidaito wajen neman goyon bayan jama'a a sassan Najeriya daban-daban.

Sun nuna cewa Tinubu ya fadi a wurare masu muhimmanci irin su Babban Birnin Tarayya (FCT), jihar Nasarawa da Filato — inda Kiristoci ke da rinjaye.

Sa’ad Aboki ya ce:

"Zaɓen ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa Kirista daga Arewa zai zama wani mataki na gyara kura-kuran baya.
"Da kuma nuna kyakkyawar niyya ga al’ummomin da suka ji an ware su a baya."

An nemi Kwankwaso ya goyi bayan Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa wata kungiyar Yarabawa ta yi kira ga Sanata Rabiu Kwankwaso game da mara baya ga Bola Tinubu.

Kungiyar ta yi kira da cewa ya kamata Kwankwaso ya goyi bayan Bola Tinubu maimakon hada kai da 'yan adawa.

Ta kara da cewa a matsayin Kwankwaso na dan siyasa mai tasiri a Najeriya, bai kamata ya tsaya a jam'iyyar adawa ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng